18

7K 591 254
                                    

"Grad dinmu ne fa. Amman kalli yanda gaba daya makarantar hankalin kowa ya koma kan yaya"

Asaad ya karasa maganar yana dariya. Da murmushi a fuskar Aseem yace.

"Nasan abinda zai faru kenan ai"

Agogon hannun shi Mamdud ya duba, lokaci na kurewa, shi kanshi so yake ya wuce tasu makarantar. Inda labeeb yake yana gaisawa da mutane ya karasa.

"Ina son wucewa school dinmu"

Dakuna mishi fuska labeeb yayi.

"Kabari muyi hotuna kawai, sai mu wuce tare mana. Banason su Asaad suji kaman bana nan"

Sosai Mamdud ke kallon shi. Har ranshi baisan me yasa ranshi ya sosu da maganar labeeb din ba.

"Nah, kabarshi kawai. Ka zauna nan din har a gama, muma ba wani abu zamuyi ba. Hotunan ne kawai"

Sauke numfashi labeeb yayi.

"Ka tabbata?"

Kai Mamdud ya daga mishi.

"Kuma mota daya muka dauko. Ko in dropping dinka in dawo"

Yar dariya kawai Mamdud yayi ya juya yana fadin.

"Karka damu fa"

Su Asaad ne suka hango zai tafi.

"Come on. Ina zakaje kuma?"

"Makarantar mu"

Aseem ne ya karbe zancen da fadin.

"Makarantar ku is lame, ka tambayi yaya. Ka zauna nan mana"

Murmushi kawai yayi, baice musu komai ba ya wuce abinshi. Machine ya tare yayi makarantar su. Harya isa yana jin yanda ranar ke da muhimmanci a wajen shi.

Saboda ya taka wani mataki a rayuwar shi da bai taba zaton zaizo cikin sauki ba. Amman baida kowa dazai celebrating ranar dashi.

"Mamdud Ibrahim Maska"

Ya furta a hankali yana yin dan murmushi. Labeeb dayai alkawarin zama dan uwanshi, abokin shi, koshi baya tare dashi a wannan ranar.

Ya nuna mishi banbacin jini da bare. Baya son jininshi suji kaman baya rayuwar su. Ranshi kara baci yake. Koda ya shiga cikin makaranta kowa kagani da walwala da fara'a a fuskarshi.

Wasu mata guda biyu yan ajinsu da sukan gaisa sosai suka karaso wajen shi.

"Mamdud, ya Rabb, ina El-Maska? Kaga yanda nagama yima yayyena kuri muna class daya dakai.

Yau har hoto zamuyi dashi. Please karka cemun bazai zo ba"

Cewar fadila. Amina ta jinjina kai tana dorawa da fadin.

"Wallahi nima nasa rai. Kaga yanda nake crushing akan shi kuwa. Time din yana school din nan tsoro ke hana ni zuwa in gaishe dashi"

Kallon su kawai Mamdud yake. Maganganun su kaman tunzura shi suke. Su kadai ne yake dauka suna mishi magana dan shi.

Sai yau yagane duk kulashin da suke saboda labeeb ne. Kaman duk wani wanda zaizo kusa dashi a ajij ba suda zance sai na El-Maska. Wata tambayarsu, wani komai El-Maska.

Ko wanda ba yan ajin su ba. Zasu zo suna mishi tambayoyi. Babu abinda yafi mishi ciwo irin yanda suke tambaya sun san kaf yan gidan su labeeb. Sun rasa inda yai fitting.

"Bazai zo ba"

Ya amsa su can kasan makoshin shi. Yana kallon yanda ko kadan basuji dadin amsar shi ba. Juya sukai sukai tafiyar su ba tare da sunce mishi komai ba.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now