33

9.1K 542 95
                                    

Fuskarta harta kumbura saboda kukan da tayi. Idanuwanta zafi suke mata, ga kanta da take ji kaman ana buga ganga a ciki saboda ciwon da yake yi, ta kuma san kukan da tayi ne. Zazzabi ruf a jikinta, bata damu da ta nemi ko panadol ta sha ba dan tasan zazzabin ta bana asibiti bane.

Zazzabin ta kishi ne kawai da yake cinta. Duk yinin ranar wankanta daya, yanzun ma dakyar taja kafafuwanta zuwa toilet tayi wanka ta fito, rasa kayan da zata saka. Idanuwanta suka tsaya kan wata doguwar riga baqa, plain ce, Labeeb ya siyo mata da suka je aiki Ghana.

Fito da ita tayi ta saka ma jikinta, mai ta shafa sai powder, ta nade kanta da siririn mayafi fari, tasa hannunta kan cikinta tana kallon yanda fuskarta ta kumbura ta cikin mudubin. Kamun ta maida dubanta zuwa siririyar chain din dake wuyanta.

Hannunta tasa ta taba tana lumshe idanuwanta, tana jin komai na ranar da Labeeb ya saka mata sarkar na dawo mata, a irin lokacin nan ne, da bayan isha'i haka.

*

Wanka ta fito jikinta daure da towel ta zauna gaban mirror tana shafa mai Labeeb ya turo kofar da sallama, a hankali ta amsa mishi. Kamun ya tako ya karaso inda take, ta cikin mirror din ta sauke idanuwan ta cikin nashi.

"Sannu da zuwa..."

"Kece da sannu da zaman gida"

Ya amsa yana murmushi hadi da zura hannunshi a aljihu ya dauko wani dan akwati karami, tana kallonshi ya bude, saidai bata ga me ya ciro a ciki ba ya mayar da akwatin a aljihunshi yana saqalo hannauwanshi duka biyun a wuyanta.

Ware idanuwa tayi da taga siririyar sarqar daya daura mata yana dafa hannuwanshi kan kafadar ta, kamo hannunshi tayi ta sumbata.

"Tayi kyau....nagode sosai"

Hararta yayi ta cikin mudubin

"Ba wani... Ban taba ganin ki da sarqa ko daya ba. Kawai wannan yamun kyaune na siyo.... Nasan bakya so"

Mikewa tayi tsaye ta fuskance shi, hannuwan ta ta saka cikin nashi ta dumtse sosai.

"Ban dauka kana lura ba..."

Goshin su ya hada waje daya. Muryarshi can kasa yace

"Ina lura da komai naki Tee... Karami da babba... Komai ina lura. Nasan duk idan kika sa red janbaki fushi kikemun saboda kinsan bana son ganin komai a labban ki.

Bakya hada ido dani in kinmun laifin da kikasan zanyi fada... Ranar nafi ganin kaunarki dan a rikitani ko?"

Sakin hannunshi tayi tana ja mishi hanci hadi dayin dariya. Wannan kana nan abubuwa ne da bata zaci yana kula ba.

"Banda sharri... Ko yaushe ma ai ina nuna maka kauna"

Turo leben shi yayi gaba yana daga mata gira.

"Bana gani nikam..."

Hannuwanta ta zagaya kan kafadarshi hadi sa sumbatar shi a ko ina na fuskarshi.

"Um ba laifi..."

Ya fadi yana daquna fuska, kyau yai mata ba kadan ba, dariyar da tayi ta sashi dariya shima, kamun ya rungumeta a jikinshi yana shakar kamshin sabulun datai wanka dashi.

*

Bude idanuwanta Ateefa tayi saboda zafin da take ji a kirjinta, kamun ta soma jero Inalillahi wa ina ilaihi raji'un. Duk soyayyar nan ta Labeeb, duk wannan kulawar daga yau raba su zatayi da zulfa.

Sam hawayen ta sunki fitowa wannan karin, dan ma tana ta jero Inalillahi wa ina ilaihi raji'un dan Allah ya kawo mata daukin duhun kishin da take ji. Turare kawai ta iya dauka ta fesa ma jikinta. Ta samu waje ta zauna gaban mirrow din tana dafe kanta dake dokawa da hannuwan ta duka biyun.

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now