09

5.2K 556 130
                                    

Please if you like this story, vote, share, and tell me what you think by commenting, thank you all. 😍

Bedroom din Aisha ya wuce ya shiga dauko jakunkunan kayansu yana watsowa waje. Daya daga cikin jakar hajiya beeba takai hannu zata taba tayyab yace.

"Kuskuren da zakiyi dana sani yana tare da taba jakar nan"

Idanuwanshi data kalla tagansu a bushe. Jira kawai yake duk wani bacin rai dayake ji ya sauke shi a kanta. Tabe baki tayi ta matsa gefe ta rike kugu tana wasu girgije girgije.

Dakyar Aisha ta iya dago da kanta. Taga yanda yau Auwal ke watso musu kaya. Zuwa yai ya wuce. Dakin dawud ya fara shiga yana dibo kayanshi yana watsowa tsakar gida.

Kamun ya shiga dakin tayyab. Hannun dawud Aisha ta kama ta mike hawaye masu zafin gaske na zubo mata. Yawo tunaninta yake. Inda Auwal yake so taje da yara hudu.

Da tsohon cikin da babu kunya yake kokwanto akai. Yasan bata da kowa sai shi. Yasan cikin yan uwanta babu mai riketa ita kadai balle da yara.

Tsakar gidan ta fita. Duk cikin dake jikinta bai hanata durkusawa ba ta rike kafafuwan shi.

"Ka rufamun asiri abban sajda. Ina zani da yara? Ka duba sajda ba tada lafiya. Banda kowa kai kasani.."

Taba shin da take kara ruru wutar tsanarta take a zuciyar shi. Muryarshi a dake yace.

"Bana son ganinki Aisha. Bana kaunar ganinku gabaki daya. Inda zakuje ba matsalata bane. Ku barmun gidana shine abinda ya dame ni"

Kuka Aisha take mai tsuma zuciya. Amman ko a rigar Auwal balle ya taba shi. Sallama suka ji. Da gudu zulfa ta fito daga daki.

Su dukansu babu mai karfin amsa ma labeeb sallamar da yayi. Mamakin da yake yasa shi kasa karasowa.

Zulfa ma daya ji ta rukunkume shi. Hannu yasa ya dafa kanta. Idanuwanshi a kafe kan ummi dake durkushe rike da kafafuwan Auwal tana kuka.

Da jakunkuna da kayyakin dake watse tsakar gidan. Dakyar ya iya dauke idanuwanshi daga kansu ya juya gefe inda dawud ya fito rike sa sajda a kafadarshi.

Dago zulfa yai daga jikinshi ya kama hannunta ya karasa wajen dawud. Muryarshi cike da rashin fahimta yace.

"Dawud meke faruwa ne haka? Lafiya?"

Baki zai bude ya amsa labeeb. Auwal ya karbe zance da fadin.

"Gidana nake so subarmun. Shine abinda yake faruwa. Ko ban isa bane?"

Da wani sabon mamakin labeeb ya taka ya karasa wajen da Auwal yake tsaye.

"Abba? Subar maka gidanka fa kake fadi. Abin har yakai haka? Suje ina?"

Da hanzari hajiya beeba ta karaso inda suke. Cikin tsiwa tace.

"Kai kuma asuwa? Tsare shi kake da tambaya a matsayinka na....."

Bata karasa ba ya dauketa da wani irin mari daya sa ta ganin haske ga gilma mata ya cikin idanuwanta. Kunnenta ya daina jin iska.

"Ba'a dagamun murya. Ba'amun ihu, ba'a sakamun baki idan ina magana mai muhimmanci...."

Ya karasa maganar yana juyawa kan Auwal. A fusace ya sa kafa ya ture Aisha dake jikinshi.

"Labeeb har cikin gidana zaka shigo ka marar mun mata? Lallai rashin mutunci ka ya kai. Wallahi badan yaya ba yau sai nayi shara'a dakai"

Wani kallo labeeb ya watsa mishi. Ya tsugunna ya kamo Aisha dake share kwalla da hannunta.

"Ummi......"

RAYUWAR MUWhere stories live. Discover now