page 1

4.9K 205 11
                                    

👉🏽💍  *KYAKKYAWAR ALAK'A* 💍👈🏽

                 ©
   *_ZULAYHEART RANO_*

*STORY* *AYSHA WAZIRI*
        
    *Wannan labari mai suna a sama kirkirerren labari ne sunayen ciki da sunayen garuruwa duk marubuciyar ta yi amfani da su ne domin ta k'awata labarin ta, don   haka idan ya ci karo da yanayin rayuwar ki ki yi hakuri ba mu yi don cin zarafin kowa ba*       

'''BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM'''

                 *01*

Daddaɗar iska ce mai cike da ni'ima take kadawa, wacce duk mahalukin da yake cikin garin matuk'ar yana da cikekken lafiya za tai masa daɗi, musamman da yake garin Ningi gari ne mai manyan bishiyoyi idan har iska ta kaɗa ko ina ni'ma ce gaskiya Allah ya wadata garin Ningi da sanyi mai ratsa jikin mutum.

Yammata ne guda hudu, suke tafe a hanyarsu ta komawa gida daga rafi. Kowacce dauke da bokitin ruwa idan ka cire daya a cikinsu wacce daga ita sai 'yar kara a hannu tana wasa da shi.
   Kugunta daure  da dan kwalinta ta ci dammara da shi, gashinta na asalin bafulatana wanda ya sha tufka gaba daya ya sauko a gadon bayanta, fuskarnan cike da digo-digo na kwalliya. Duk  cikinsu shigarta ta fi tasu kyau da kuma daraja. Tafe suke suba hira  cikin nishadi suna dariya tamkar basu ta6a sanin wani abu wai shi matsala ba. A haka har suka shigo cikin garin sosai. Sun yi nisa kadan, ta kusa da ita ta ta6ota. Cikin rada-rada ta ce.
  "Ga mutuminki can, dama yana garinnan?"
   Jin haka gabanta ya fadi, tayi saurin kai duba ga inda Yahanasu ke mata nuni. Jingine yake jikin bishiya, ya sha kananun kaya na yan gayu, jeans blue da tshirt brown. Idanun 6oye cikin bak'in gilashi, sai hira suke da ɗan waziri ana tafawa. Ta saukar da kanta kasa kirjinta na kara k'aimi wajen bugu.
   "Uhm, abin ya zo kenan. Ai fa yanzu ba mu da ikon ganinki, dan takurarnan ya zo."
  Cewar ta kusa da Yahanasu, Asiya. Tana turo baki.
  Ita dai bata ce komai ba, sai  can ta dago tare da dubansu ta ce a sanyaye
  "Ku zo mu bi ta kofar baya." Tana gama faɗin  haka bata jira cewarsu ba ta juya, sai dai kafin ta  ankara ba ta ji muryar Dan Waziri ya rattabamata kira.
  "Salmah!"
Wani tarin takaici ya cikata, dole tasa ta juyo badan tana so ba  ta amsa tana dubansa. Inkiya ya yi mata da hannu alamar ta zo. Sum-sum ta soma tafiya kanta na kasa, su kuwa abokan tafiyar tuni suka yi gaba bayan sun kwashi gaisuwa cike da ban girma.
Durkusawa tayi a gaban Dan waziri, ta gaishesu a ladabce, ciki-ciki ta ji mutuminnata ya amsa fuska babu wata walwala, idan da sabo ya kamata ma ace ta saba.
  "Ban hanaki bin wadancan rafi ba? Ko so kike a zagemu? Wannan damarar da kika yi ta mece? Gashinki a bude, ke yanzu hakan bai ba ki kunya ba?" Yayanta ɗan waziri ya dire maganar yana aika mata wata uwar harara.
Kasa cewa komai ta yi, sai kawai ta shiga murza ido da yatsa. Sai sannan ta ji kunyar yawo ba kallabin.
  "Kin yi shiru." Ya kuma jefa mata tambaya.
A Dole Salmah ta tattaro nutsuwarta ta soma magana.
  "Ka yi hakuri Yaya."

"Ai fa, idan har wannan ne kin iya. Wannan matartaka nan gaba sai ka yi dagaske don na lura kauyancinta yawa gareshi." Dan waziri ya yi maganar cike da zolaya.

Wanda ake yi domin shi, bai ce komai ba, hasalima ya karkata gaba daya hankalinsa ne ga danna wayarsa.
Itama jin bai ce komai ba yasa ta mike gwuiwa a sake, ta dubi Yaya dan Waziri idanunta rau-rau.
  Ta ce "na tafi?"
Kallo daya ya yiwa kanwartasa ya fahimci damuwarta, take ya ji tausayinta ya kama shi,
A sannu ya gyada mata kai.
Ya ce "Shike nan, idan na shigo za mu yi magana, karki kara fita a haka ba kallabi, kada kuma na kara ganinki da damara."
"To Yaya." Ta amsa a hankali tare da  gyada kai sannan ta juya tana warware damarar ta yafa dankwalin a kanta, cikin  sauri-sauri ta bar wajen zuwa cikin gida.
   Bata zame ko ina ba sai bangaren Hajja Chub'ad'o, wacce takasance uwargidan Sarki Abdulkarim, da zazzakar muryarta ta doka sallama, Hajja dake zaune a rantsatsen falonta kuyangu biyu suna matsa mata kafa ta amsa cike da sakin fuska. "Wa'alaikumus salam Ummuna Salmah daga ina haka da yammaci?" Ta karashe tambayar tana jawo Salmah jikinta. "Hajjata daga rafi na ke na je raka su Asiya." "Oh! Allah ita dai Salmah bata gajiya da zuwa rafi ko?" Shagwaɓe fuska ta yi ta ce "Allah Hajja idan na je wajen rafin ina jin nishaɗi ne." "Ai wallahi Hajja haka Salmah take kullum zuwa rafi ni mamaki take bani." Ameena dake shigowa falon ne take maganar.
   "Ai kuma gara ita domin tana son jama'a ke kam halinki ai sai ke." Hajja ta dire maganar tana dan hararan Ameena. "Kai Hajja ni na lura baki son laifin Salmah amma tsakani ga Allah a matsayin mu na 'ya'yan Sarki sai ta rika zuwa rafi?" Salmah bata ce komai ba domin ita ɗin ba mai yawan surutu ba ce, sai Hajja ce ta ba Ameena amsa da "Eh! Ta je ɗin zuwa rafi ai ba wani abu bane ku dai da kuka ɗauki kanku da nisa ku yi ta yi, ke Salmah tashi ki shiga ciki Allah ya yi albarka." "Amin Hajjata na ga Ya Yarima da Ya ɗan waziri a kofa." "Eh ɗazun ya iso ta shi maza kin san yau akwai babban taro." Ta bude baki da niyyar amsawa ta ji sallamar Ya Yarima da Ya ɗan waziri, wani kallo da Yarima ya aika mata da shi ya sanya jikinta mutuwa ta nema duk wani kuzari ta rasa, lumshe ido ta yi cikin wani irin yanayi a hankali ta mik'e tana niyyar barin falon.
"A'a ina zaki je Salmah?" Hajja a yi tambayar da dan mamaki "Ciki zan shiga fa Hajja." Salmah ta bata amsa. "Ga  Yayanki Yarima baku gaisa ba." "Hajja mun fa gaisa da su a kofa ki tambayesu." Ta dire maganar kamar zata yi kuka. "To kuma menene abin bata fuska?" "Haba Hajja mun shigo a maimakon ki kula mu kin biyewa wannan yarinyar." Yarima ne yake magana amma sai ka rantse da Allah ba shi yake yi ba, domin hankalinsa na kan wayar hannunsa. "Kai nifa bana son irin halin nan naka, idan ban kula Salmah bawa kake so na kula? tashi ka tafi idan ka gaji." A ɗan zafafe ta yi maganar.
   Murmushi ɗan Waziri ya yi ya ce  "Hajja mai Salmah Allah ya baku hak'uri."  " Al'ameen kenan  kai kana da  fahimta shi yasa nake jinka a raina amma shi wannan dan zafin kan idan ya iso gidan nan baya da buri sai na ya takura min yara musamman Salmah." "A yi hakuri Hajja ai itama Salmah wani lokacin sangarta na damunta fa..."
   "Ku tashi ku tafi na gode da gaisuwar." Cikin faɗa take maganar.

Yanzu aka fara ko hannu bamu sanya ba, wannan ɗin somin taɓi ne.😍😍😍

*MUNA SON JIN RA'AYIN KU GAME DA WANNAN LABARI, MATUKAR DAI KUNA SON A CI GABA DA TYPING.*

*ALKAMIN ZULAYHEART RANO*✍

'''TEAM SALMAH
TEAM YARIMA
Zulayheart Rano'''

KYAKKYAWAR ALAK'AWhere stories live. Discover now