3

5.2K 543 6
                                    

BISMILLAHI RAHMANI RAHIM DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA

Zaune take a daki tana waya da sagir chan naji tace "serious da gaske kana hanyar gidanmu yaushe ka dawo"

Sagir: "yau da safe na dawo i just can't afford not seeing that your beautiful face"

Murmushi mai sauti tayi, wanda yasa tsigar jikin Sagir ya mike sannan tace "like seriously"

Sagir: "yea so am i free to come right now"

"yap of course but kayi sauri fah dan I missed you so much "

Sagir: "miss you more zaujat"

daga nan suka katse call din, ita Kuma ta shiga toilet da saurinta dan yin wanka tana gamawa, tafito daure da towel pink, ta dauki lotion dinta mai suna love nature, ta shafa sannan ta shirya cikin material gown light blue and yellow Wanda akasa ma stones blue.

Ta yafa gyale da takalmi duk  baki sanan ta fesa jikin tada tulare, tayi kyau sosai, fitowa tayi daga dakin ta nufi kitchen domin tanadar abinda zata tarbesa da shi snacks da drinks ta hada mai.

Tana gamawa call yashigo already ta rigada ta San sagir ne dan haka bata damu yin picking ba ta nufi waje da tray din da tasa mai snacks and drinks akai.

Garden ta nufa, zaune ta tarar dashi sanye yake acikin blue shadda yayi kyau dan ba laifi yana da kyaun sa dadai gwargwado, karasowa tayi wurin sa ta gaida shi sannan ta zauna chan nisa da shi.

bata fuska yayi yace "haka kika yi missing dina koh" kanta na kasa tace 'ka dai san a gidanmu muke koh" haka dai suka cigaba da hira kaman awa daya yace toh ni zan wuce zo ki raka ni mota.

bude baki tayi da niyar yin magana yayi saurin daura yatsansarsa a bakinta yace "sshhhh ban san musu" haka dai tabi bayan shi ba dan ta so ba suna iso wa bakin motar ta tsaya sagir dake jiran ta shigo yace "zaujat shigo mana magana nake Son yi da ke"

"toh" tace ta zagaya ta shiga tana shigowa ta kule kofa da sauri yayi pinning din motar ya jawo ta yafara kissing dinta a gaggauce kasancewar motar tinted ce dan haka ba mai ganin su jin Yana lullubar zip dinta yasa tayi saurin ja da baya tace "sagir meye haka"

Hannu ya daura a bakinta yana girgiza mata Kai alama tayi shiru haka dai ya gama tsote tsote da lashe lashen sa sanda ya gamsu sannan ya saketa bata jira cewarsa bah ta gyara jikinta dasauri tafita daga motar ta shiga gida cikin sauri

Taci sa'a ba kowa a falo da sauri ta karasa daki ta kule kofa tafada kan gadon tana maida numfashi ta hau tunani abinda sagir yake mata dan randa ya fara taba ta sai da ta mare shi har call dinsa ta daina picking hama da yake namijin duniya ne ya samu yayi mata dadin baki sharrin shaitan ne ba halin shiba taba mata.

Haka suka dawo yanda suke a da tun lokacin bai Kuma kara taba ta bah sai ran da suke a motarsa suna hira ya yunkurin tabata ta hanashi yafara mata korafi bata Son shi yanda yake santa sai taji sanyi aranta tun daga ran bata kara hanashi bah tun bata jin dadin abin da yake mata har ta fara ji hama bata taba nuna mai hakan bah.

           WAYE SAGIR

Sagir saurayin Zarah ne sun hadu ne a auren Hauwa 'yaar Hajiya Rahma wato umma shi sagir abokin kanin ango ne toh tun lokacin ne ya ganta ya fara takura ta da nacin sa haryayi nasara ta amince da soyayyar shi, duk cikin familyn ba wanda bai San sagir bah a mastayinsa na saurayin zarah.

Dan abi da kansa yasa haka yi mai bincike a kanshi Kuma ya gamsu basu san sagir irin wayayun mazan nan bane  masu neman mata, hama tunda ya fara son zarah ya daina in ya debo zafi yazo wurin zarah suyi tabe tabe wannan kenan.

Amira ce ta bude kofa ta shigo dakin ganin yanayin yaruwarta, ta fara takowa gab daita sannan ta dafata tace zarah a zumbure zarah ta tashi tana "uhmn ehmn na'am" kallon ta Amira tayi tace "ke wai meke damun ki ne nagan ki duk a hargitse sai tunani kike"

Zarah ta yastine fuska tace "bah komai" ganin bata son ta fada mata ta yasa ta kwarda zancen tace "nazo dakin ki dazun baki nan Ina kika je"

"Eh sagir ne yazo" uhmmn kawai Amira tayi dan Allah ya gani wannan sagir be mata bah randa ta tunkuri zarah da maganar tayi hankali dashi sai da suka yi ba dadi daita, ita Kuma tayi shiru tun ran kar a zo ace tana kishi dan yar uwarta ta samu miji mai kyau dan ta lura zarah zata iya ciwa kowa mutunci hakan sagir.

"Anty tunanin me kike" kirkiro murmushi Amita tayi tana cewa "ba komai kifito mu daura abincin dare kinsa yau ya Ahmed zai dawo koh" tsaki zarah taja tace "mtsw wlhi nina gaji wannan masifafen koh mai zai dawo da shi oho wlhi gidan Ammi zan koma haba mutum kulum cikin aiki"

Sakin baki Amira tayi tace "ki koma mana waye tsayarda ke na maji ya kalifah zai dawo" zarah tace "uhmmn ba zani Kuma bah wannan jarababen d'anta yazo ya jibge ni a banza" dariya Amira ta fara mata dan ta san basu shiri da ya Khalifa shiyasa tace zai dawo haka dai suka mike suka shiga kitchen.

jollof din shinkafa sukayi da naman kaji suka jera komai a dinning table zarah tace "bara naje nayi wanka mtsw ji yanda mutum ya hada uwar zufa" Amira tace "eyye yarinya sai kace ba jikin ne da ni bah, i wonder yanda Zaki yi a gidan ki" yatsine fuska zarah tayi tace "oho dai ba zan auri jarabbaben da zai yita sani aiki kulum bah" Amira tace "wlhi da han hada ki aure da ya khalifa da naji dadi" dadauri Zarah tace "ba Amin bah barin shiga ciki nayi wanka kinga magrib ta kusa"

Daga nan ta wuce daki wanka tayi tana shirin fitowa taji hana Kira sallar magrib ta koma cikin toilet tayi alwala sannan tafito doguwar riga mara nauyi ta zura ta shimfida sallayar tasa hijjabi ta fara sallah ba ita ta tashi bah saida tagama sallar ishai.

Nade sallayar da hijjabi tayi ta ajiye su in da take ajiyewa ta je wajen mirror ta dauko lotion ta shafa sannan ta fita zuwa falo zaune ta tarar dasu a dinning suna cin abinci harda ya Ahmed din itama gaida su ta taja kujera ta zauna abinci ta zuba dan kadan tafara ci chan ta dago ta bude baki zatayi magana suka yi ido hudu da ya Ahmed kasancewa suna facing juna ne harara ya wasto mata

Sanin halin shi yaki jinin yana cin abinci ayita surutu, haka suka cigaba da cin abinci shiru ba wanda yayi magana sai motsin chokali suna gamawa ta tashi ta nufi hanyar daki Abba yace "yau bah hira"

" eh Abba bacci nike ji"

" toh sai da safe Koh" a haka tashiga daki wayar ta dake chaji ta dauko daniyar chatting Miss call din sagir guda goma ta tarar tsaki tayi ta mayar da wayar ji tayi chatting ya fita aranta koh mai yake nema oho aka dai ta kwanta

            Vote And Comment Pls

wannan littafin inshallah zai zo da darasi da mastalan da muke fuskanta a yau kar a manta da vote da Kuma comments a karfafamin guyiwa nagode

Vote
Comment
Follow Meenarlee ❤️ 😌
 

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now