26

2.2K 335 11
                                    

A wahalace ta mike tashiga bayi ta dauro alwala tazo tayi sallar ishai, wani irin zazabi take ji gayi jikin ta ya da zafi sosai, tana gama sallah ko adua'a bata tsaya yi ba ta koma kan gado ta kwanta hawaye suka Fara silowa kuncinta.

tana cikin haka taji an banko kofar da karfi  bata dago ba dan tasan sarai khalifa ne, "ke" ya daka Mata tsawa still bata dago ba illa gyara kwanciyar da tayi kaman bata san da mutum a gurin ba.

Ganin yanda ta basar dashi ne ya kara masa bacin rai wato ta maida shi mahaukaci ko girgiza kai yayi "ba dake nake magana ba" ya sake dakaata tsawa.

Tsaki zarah taja tadan dago da kanta tace "ehen Mr Man meye na wani zo kana min ihu akai"

Lallai wannan yarinyar, rashin kunyarta ya kai ta zage ni, ya fada cikin zuciyarsa danne mamakin sa yayi yace "wlhi in baki tashi yanzun ba sai na miki dukan mutuwa"

"Mtsw toh wa ke tsoron ka do your worst" tace tana masa kalon sama da kasa.

Aii Khalifa na ganin aka ya nufe ta cikin zafin nama, zarah na ganin haka ta mike dasauri tashiga bayi tana gab da kule kofa, ya daura hannu a handle din ya bude kofar da karfi, ya jawo ta tass kake ji yakifa mata mari "shegiya mara kunya, karuwa, mazinaciya" yace sannan ya tofa mata miyau ya hankade ta tafadi a kasa jikake tim, goshin ta ya buga da gadon wani irin ihu ta kwala sannan ta fashe da kuka.

Gogan naku kuma ko ajikin sa haka ya fita a dakin yana dariyar mugunta, kuka zarah take har muryar ta ya dashe, goshin ta kuwa ya kumbura saboda taji ciwo kadan dan ba karamin bugawa tayi da gado ba.

Ita bama wannan ke damun taba kalaman sa sun fi mata ciwo, wulakancin sa yakai har ya tofa Mata miyau, kukan da take yasa zazzabi mai karfi ya rufe ta nan da nan ta fara rawar sanyi duk da blanket dake jikinta sai hucin zafi jikinta yake sosai, da kyar ta samu wani wahalalan bacci yayi gaba da ita.

❤️❤️❤️

Tana cikin bacci taji abu mai zafi ya ratsa jikinta, a matukar tsorace ta miki tana shafa wurin, dagowa tayi jin dariyar sa, tamke fuska yayi kamar bashi ke ta dariya yanzun ba.

"Next time da zaran an kira Sallar fajr you're expected to be awake kin gane" yana gamawa ya fita a dakin

Zarah kuwa mutuwar tsaye tayi, tana sake kallon inda ruwa zafin ya taba duk wurin yayi ja sosai, uhmmn kawai tayi dan she's speechless, bata taba tunani Khalifa zai kai wannan limit ba amma sai ta nuna mishi in yasan wata bai san wata ba.

Triple Update Yeah Guys, I Just Decide To Update Because You Guys Deserve It, I Just Wanted To Say A Big Thank You To All Of You For The Vote's And Comment, And Also The Reads Thank You I Really Appreciate 😘😘😘

VOTE
COMMENT
SHARE

💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙💙

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now