23

2.3K 247 10
                                    

Yana bude drawer yagan wayam ba key wani irin wawan tsaki yaja Ya zauna a gefen gado ya fara neman mafita yanda zai ya fita a dakin.

Samir ne zaune a falo yasa kafa daya kan daya sai faman murmushi yake yana latsa waya, tuna halin da Khalifa zai shiga in bai gan key bah.

Har yanzun kuma mamakin canzawar halin Khalifa yake da abinda yaso aikata, wai zai je asibitin da haka kai zarah lokacin da tayi Bari (miscarriage) a mishi fake HIV report a ce Zarah na dashi da gannan sai yace shi bai son auren ta kuma ya fasa.

Ajiyar zuciya ya zauke dan yama kansa alkawari komin mene ne sai an daura Auren Khalifa da Zarah, dan yana hangowa masu Alheri a ciki, shi kuma bazai bi bayan Khalifa ya cutar da shi ba...



Zarah da Amira ne zaune a daki sanye suke cikin wata tsadadiyar lace blue da ratsi fari da gold sunyi kyau sosai an musu light make-up, sai kuma wasu kawayen Amira sai hayaniya suke suna tsokanar juna, Zarah kuwa shiru tayi ko tal bata ce ba kamar wacce aka sato.

Wani irin bugawa zuciyar Zarah yafara jin hayaniya ya karu afalo ga kuma wasu sai rangada guda suke, bata gama tunani ba Batool ta taho dakin a guje tace Anty Amira, Zarah an kawo lefen ku ta fada tana rawa, dariya kawayen Amira suka fara daganan suma suka mike suka nufi waje dan ganin lefen.

Suna gama fita a dakin hawaye suka fara sauka afuskar Zarah, "Wai Zarah ban ce miki ki daina wannan kuka ba" Amira tace dan ita fa tagaji da wannan koke koken da Zarah take kullum, zarah bata tanka mata bah illa karfin kuka data kara.

"Oh dan nayi magana shine kike min kuka wlhi ko kiyi shiru kona kira miki Ya Ahmed" da sauri Zarah ta goge hawayen ta, tayi shiru ta sada kai kasa kamar ba ita tayita kuka yanzun bah

Suna cikin haka sai ga wasu kyawawan yan mata farare sol dasu, shigowa daki sukayi da Salama duk wace sanye take cikin tsadadiyar atamfa, amsa musu su Amira sukayi, fuskar su dauke da fara suka zo suka zauna a wurin Amira "baki Gane mu ba" wata daga cikin su ta tambaya, girgiza Kai Amira tayi alamar a'a, Zarah data kura musu ido tun dazun tace "kaman kannen ya Yusuf koh"

"Lah ya kika gane" karama cikin su tace cikin mamaki, murmushi Zarah tayi tace "kuna yan kama aii" "gashi kuma Antyn mu bata gane mu bah" suka ce suna kallon Amira dan ita harga Allah bata gane su ba, da sauri ta boye mamakin ta tace "oh sorry wlhi na mantardw fuskokin kune" "ok aii ba damuwa" daganan hira ya barke tsakanin su, sai karfe hudu suka bar gidan.

"Wlhi Zarah kin gan lefen ki kuwa ya mafi na Aunty Amira yawa da kyau" batool tafada, uhmmn kawai zarah tayi dan ta gaji da wannan surutun batool akan lefenta har tafara Jin ciwon kai, "Dan Allah ki mana shiru" Aisha tace dan itama ta fara gajiya da surutun ta.

"eh aii nasan bakin ciki kike saboda nata yafi naki kyau" filo Aisha ta wurga mata tace "Batool ban fa son iskanci"

(Last week haka kai lefen Aisha tare za'a yi dana su Zarah, saboda Ya Nazir ne mijin da zata aura)

Sai bayan sallar ishai kowa ya kama gabansa, zaune suke a falo suna duba lefen, na Amira akwati set uku duk an cika su da kaya masu tsada da kyau har da kyan make-up, sai na Zarah akwati set biyar su Ammi suka kawo komin dake cikin akwatin kuwa daga Dubai aka hado komai illa atamfa da lace, lefen dai duk sunyi kyau sai dai makiyi........

Vote
Comment
Share

Thanks

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now