38

2.5K 242 5
                                    

Bayan an Kai zarah gidan ta kuka sosai ta sha, har Bata San sanda bacci ya dauke ta ba, can taji motsin bude kofa da sauri ta bude ido, gani khalifa yasa ta cewa "ka fitar min a daki"

Yi yayi kaman bai ji ta ba yazo kusa da ita ya zauna.

Matsa baya tayi tace "get out of my room ban son ganin ka na tsane ka"

Share ta khalifa yayi ya sa hannu ya jawo ta da karfi ta fada a jikin sa, sannan yafara shinshi na wuyar ta

"Ban fa so iskanci" tace bakin ta na rawa

"Shi Kuma na fi so" khalifa yace cikin shakeken muryar sa.

Kiciniyar sauka ta fara ganin haka yasa Khalifa ya mirgino ta yanzun shi yake a saman ta

Bude baki tayi da niyar masifa sai kawai khalifa ya cafke bakin ta kissing dinta yake sosai da kyar ta samu ya sake ta miyau ta zubar tace mugu kazami Allah ya isa, "Dan iska"

"Nine dan iska" Khalifa yace cikin mamaki Yana nuna kanshi.

"Eh din walahi ka Kara tabani ban yafe bah"

"Ni da Kaya na Kuma sai a min rowa" yafada Yana nufar ta, da sauri Zarah ta shiga toilet ta kule tana "Allah ya kiyaye na zama kayan ka"

Murmushi khalifa yayi kawai ya ajiye Mata kaza da drinks da ya kawo Mata yayi ya fita a dakin tun dama bai da niyar yi Mata komai kawai dai Yanayin yanda ta kwanta da Yar rigar baccin dake a jikin tane ya tada Mai hankali

Bayan minti talatin zarah ta fito daga toilet ganin ba kowa yasa ta saki ajiyar zuciya taje ta kule kofarta tazo ta kwanta tayi adduar bacci

💠💠💠💠💠

Idon ta ta bude da sauri Jin hanna shafa Mata Kai hana hura Mata iska a kune.

Ganin ta bude ido yasa yace "lokacin sallah yayi"

Wani harara ta Mai tayi uhmmn, ta tashi taje toilet sanda tayi brush sannan tayi alwala.

Lokacin da ta fito ya riga ya bar dakin, sallaya ta shimfida tasa hijabi ta fara Sallah tana gamawa  tayi wanka ta koma bacci

Sai karfe takwas ta farka, sanda ta Kara brush, sannan ta nufi falo ganin khalifa zaune yasa ta kauda Kai kaman Bata gan shi ba ta wuce kitchen, shima basar da ita yayi ya cigaba da kalon shi.

Can ta fito hannun ta dauke da plate din indomie, dafafar kawai, soyayyar plantain da kazar Jiya sai juice a glass cup. Kamin kace kamshi ya cika falo, kujerar da ke fukantar inda Khalifa ke zaune taje ta zauna ta fara ci hankalin ta kwance.

Khalifa kuwa sai kukan yunwa cikin sa yake, can yace "zarah yunwa nake Ji"

Zarah har taso tayi dariya yanda yayi maganar sai Kuma ta daure fuska tace "abincin ya Kare"

"Toh ki Samar min wani"

"Kasan Allah ba abincin da zan ma tunda kace nawa baya dadi"

"Uhmmn toh kiyi hakuri Koh kadan ne ki daure ki min"

Mtsw taja tsaki ta cigaba da cin abincin ta

Ganin tana son Bata Masa lokaci gashi Kuma cikin shi yafara ciwo Dan yunwa yasa shi Mikewa yaje wurin ta ya dauki plate din

Da sauri Zarah tace "ka bani abinci na" tana bin shi a baya.

Da gudu khalifa ya hau stairs ya shiga daki ya kule kofar, ya zauna a gado yafara ci kaman Wanda yayi shekara bai ci abinci ba Dan ba laifi zarah akwai iya girki sosai.

A falo Kuma dariya zarah ta yita yi ganin yanda ya gudu har da kule kofa, sanda tayi Mai isar ta sannan ta wuce daki.

One week ❤️

Cikin wannan sati daya ba abinda ya canza a zaman su, Sai abincin da Zarah take mishi Dan tun rannan da taki bashi abinci har ciwon shi ya tashi take tsoro Dan rannan ta mutakar tsorata da yanda ya yita yi kaman zai mutu Kuma ya ana ta Kiran kowa.

Bayan Zarah ta gama abincin rana daki ta nufa Dan Kara wanka.

Tana cikin toilet Khalifa ya shigo, ganin ba kowa a dakin Kuma Yana Jin motsin ruwa yasa ya zauna a bakin gadon, ganin har minti talatin bata fito ba Kuma har yanzun bai bar jin motsin ruwa ba yasa ya nufi wurin toilet din ya Kai minti biyar kamin ya daura hannu a handle din kofar ya bude.

Jin han bude kofa yasa zarah ta juyo a tsorace ta kurma ihu tasa hannu tana Kare kirjinta.

Khalifa Kuma bai ma San tana yi ba Ido ya kura mata Kamar wani soko.

Ganin yanda ya kura Mata ido yasa zarah taje wurin kofa da dabara ta ture shi ta kule kofa. Bayan ta gama wanka kasa fitowa tayi Dan wani irin kunyar shi take ji🙈

💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💕💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞💞

VOTE
COMMENT
SHARE.

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now