5

3.6K 370 2
                                    

     BISMILLAH.....
    
"YA MACE

**WRITTEN BY MEENARLEE**

Zarah ce zaune akan gado tana chatting da Sagir.

Sagir : zaujat wai dan Allah me na miki ne, why are you giving me that cold attitude kinsan yanda na shiga damuwa kwana biyun nan da baki yi picking call dina.

Yatsine fuska zarah tayi ta tura mishi kafini sanin laifin ka

Sagir : toh ni ban sani ba ki gaya min laifin me nayi.

turo baki gaba zarah tayi kaman tana gaban shi ta rubuta mai : ni dai bana son wannan taba nin da kake.

Sagir : meye laifin haka aii wannan shine wayewa da soyayya kuma auren ki zanyi so i don't see anything there.

Gala ma text dinsa harara zarah tayi sannan ta tura mishi, ni dai in ka kara wlhi that will be the end of this relationship dan ni ba muharramar ka bace.

Sagir : Dan wannan abin ne you want to end the relationship zaujat hanya kina so na kuwa.

Tsaki taja sai kuma ta tura masa, wannan abinda muke aikatawa a ganin ka ya dace kenan, kuma in bana son ka sai na yarda kayita taba ni yanda kake so halin ku kenan maza in kuna son abu aka hana ku sai ku fara hanya ana sonku toh nama fasa bana so.

Sagir : wayyo Allah na zaujat kiyi hakuri me yayi zafi aka toh baran kara bah shikenan

Zarah : da dai yafi maka.

Daganan ta sauka online tana cewa "mtsw kaji min d'an rainin wayo ajiya wayar tayi ta kwanta dan gobe za su family reunion dan duk shekara sai an yi reunion kuma dole kowa yazo sai dai in baka kasar .

Washe gari da safe suka shirya dukansu ummi da Abba mota daya sai Amira,zarah ,ya Ahmed da ya Nazir mota daya dan jiya da d'are ya dawo.

Gidan cike yake da yan uwan na nesa da kusa su ma ciki suka shiga suka gaida baba da inna haka fara abinda ya kawo su taro aka bude da addua daganan baba ya fara godiya ga Allah.

Sannan ya dawo masu nasiya dasu rike zumunci ko bayan ranshi duk Wanda ya tsarwatsa zumunci cikin su toh bai yafe bah yayi ta kawo musu muhinmanci da girman zumunci daga baya ya dawo sa musu Albarka da yayansu

Sannan yace akwai mai magana kallo kallo haka fara yi sannan mahaifin su zarah yace "eh baba dama maganar auren Amira ne wannan yaron da yake sonta ne yake son turo da magabatansa nace, toh ya dan dakata muji ta bakin ku"

Murmushi Baba yayi yace "toh Masha Allah aii mu bamu da matsala sai fatan Alheri" Abba yace "Baba wani rana kuke ganin za'a sa musu

Aka dai akayi shawara kowa yace ran sati tunda ba, mai zuwa aiki ana weekend, baba yace "Allah yasa Alheri" duk haka amsa da "Amin" aka cigaba da tataunawa daga baya haka ci abinci akayi hira basu suka bar gidan ba sai karfe goma....

Vote
Comment
Follow
        THANK YOU

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now