29

2.3K 317 18
                                    

Yau sati biyu kenan da Auren Khalifa da Zarah amma ba abinda ya canza a zaman su, illa bakar wahallan da Zarah take sha a'hannun sa dake karuwa, kullum da salon muguntar da yake bijiro mata dashi kullum sai tayi mishi Abinci kuma bazai ci bah, wani lokaci ma har zuba mata yake a jiki komin zafin sa.

Shara da mopping kuwa kullum yake sata in tayi laifi, zarah duk tayi baki ta rame, gashi Khalifa ya kwace Mata waya, sai dai in aka kira ta lambarsa, sai ya bata tayi magana shima a gabansa zatayi shi.

Rayuwarta ya koma kamar na cikin prison, kuka kuma ya zame mata kamar abincin saboda yin sa take kullum, gayi  ya uma ana kowa kawo musu ziyara.

Yanzun tsaye take a kitchen tana hada masa coffee tana gamawa ta zuba masa a jug, ta ajiye shi a wani karamin faranti sannan ta dauka ta nufi dakin shi dasalama ta shiga.

Ganin kamar yana bacci yasa ta ajiye masa a drawer dake gefen gadon tana juyawa taji yace "ke zonan" a'tsorace ta juyo ta tako wurin sa tace "gani"

Wani irin harara ya bankaro mata sannan yace "ki zuba min shi a cup"

"toh" tafurta ta zuba a cup din, ta mika mishi yana kaiwa baki ya kurba kadan sai kawai tagan ya bata fuska juyowa yayi gareta a'fusace ya juya mata sauran ajiki "washhhh" ta kwalla kara tana shafa gurin dan akwai zafi amma ba sosai bah.

"Mtsw in ba dan kauyanci ba common coffee baki iya hadawa ba, i give you one minute to pack this trash"

Zarah na Jin haka tayi saurin daukan farantin ta bar dakin, dakinta ta koma ta kwanta...............

Su Amira da Ya Yusuf kuwa, zaman su Alhamdulillah, sai cin amarcin suke, sai dai duk da aka Amira na cikin damuwa dan kullum cikin Kira lambar zarah take kuma switched off.

Aisha da nazir suma zaman nasu sai dai Masha Allah, zaman girmamawa da mutunta juna suke komin ya daidaita tsakanin su.

Washe gari da safe karfe biyar da minti talatin Khalifa ya tada zarah "ke tashi" bude idonta da suka yi nauyi dan bacci tayi tace "uhmmn"

"zanyi tafiya make sure you Clean my room and take care of the house understand" hmmmn kawai Zarah tayi ta koma bacci dan bata da sallah, ba ita ta tashi ba sai 6:30am wanka tayi sannan ta wuce kitchen, plantain da kwai ta soya sannan ta dawo falo taci tana gamawa ta maida kwanonin kitchen sannan ta dawo ta kwanta a falo tafara bacci saboda tunda aka kawo ta gidan bata taba samun damar hutawa irin wannan ba.

Karfe goma ta tashi taje ta wanke fuska sannan ta nufi dakin Khalifa ta fara gyara masa daki wani paper, ta gani a kasa dauka tayi tasaka a'dustbin sannan ta dauka dustbin in ta nufi waje ta zuba datin a babban basket da ake zuba sharan gidan ga baki daya sannan ta koma ciki sanda ta wanke dustbin in sannan ta je ta ajiye shi.










Khalifa.💋💋💋💋

Mtsw tsaki yaja ganin ya manta da wani abu, juya mota yayi zuwa hanyar gida da sauri ya faka motar ya nufi ciki, isowar sa daki yafara duba koina, tunan da yayi yace Zarah ta gyara masa daki kamin ya fita, yasa ya nufi dakinta dasauri bude kofar dakin yayi yace "ke dana ce ki gyara min daki kin gan wani paper" ya tambaye ta sai da kirjin zarah ya bada dam sannan tace "eh"

"toh Ina yake" khalifa ya tambaya "gani nayi the paper is useless shi yasa na wurgar da shi a basket"

"what" Khalifa yace yana zarowa idonshi kamar su fado, "do you know how important that paper is" Khalifa yadaka mata tsawa, "wlhi ban......... "Dan Allah ki min shiru mstw"

wurin basket yanufa dasauri wayam ya gan basket ba komai, malam Ismail ya kwada ma maigadi kira dasauri malam ismail ya taho yace na'am yalabai, "ina sharan dake a wannan basket"

"yallabai dazun naba Idris ya je ya zubar"

"ok kana iya wucewa" malam ismail na wucewa ya juyo ga zarah yace "in ba jahilci irin naki bah who even gave you the permission to touch my things kai waye ma aike ki daki na"

"Mtsw da alama tsufa tafara kama ka toh bari na tuna ma kai da kanka kace naje na gyara  ma daki"

"Uhmmn i can see tarbiya bai ishe ki bah koh, har ki kalle idona kice na fara tsufa  da alama ba'a miki tarbiya agida ba"

"Khalifa don't even dare drag my family into this, batun tarbiya kuwa kaine kafi cancanta ace baka dashi da alama ba'a baka isheshen tarbiya daga gida ba" zarah tace cikin fushi

"Zarah did you just insult my Ammi and Abi"

"Oh ashe da zafi kana zagin na wasu baka son a zagi naka mtsw"

Tasss ya dauke ta da Mari Yana "you're very stupid da farko kin wurgar min da takarda yazun Kuma iyayen nawa Zaki zaga Koh"

"Eh an zaga din, wlhi matukar ka zagi nawa sai na rama" kara Mata  wani mari yayi yana jin wani irin  baccin Rai har baisan sanda ya furta mata "Dan ubanki na sake ki saki daya pack your things and live before i come back" yafada sannan ya je wurin motar sa ya shiga ya bar gidan da gudu.

Wani ihu zarah ta kurma tafashe da kuka duk da ba zaman lfy suke ba amma jin kalman sa tayi kaman an soke mata wuka a kirji, me zata ce ma Ummi da Abba, ciki ta nufa tattara kyan ta cikin akwati biyu sannan ta dauki abubuwan da zata bukata ta bar sauran kayan, tana fitowa daga gidan tsaye tayi tana bin gidan da kalo daga bisani ta fara tafiya tana kuka.

😭SAD CHAPPY RIGHT

POOR ZARAH😥

IS LIKE I WON'T UPDATE TOMORROW DAN AM NOT SEEING YOUR VOTE AND COMMENT.

VOTE
COMMENT
SHARE PLS🙏

🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤🖤

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now