22

2.3K 323 12
                                    

Duk faran dake fuskar zarah ya koma ciki ta tamke fuska wani irin harara ta fara aikawa Aisha sai kuma ta kauda kai gefe tana kokarin mai da hawayen dake tasowa mata, "me yafaru ko dai baki son Ya khalifa ne" Aisha ta tambaye "hehe ya khalifa ne baza ta so bah" Batool tace cin mamaki

"Toh naga yanda ta tamke fuska ne yasa na tambaya" "mtsw wani babe zata gan ya khalifa tace bata so aii ni da ace shi zan aura" Batool tafada tana dariya, duka Aisha ta kai mata dasauri batool ta kauce tana ma Aisha gwalo.

Juyowa sukayi ga Zarah cikin sauri  jin sheshekan kuka tambaya suka Fara jefo mata aka me ya faru take kuka, shiru ta musu bata ansa ba suma ganin haka yasa suka Fara rarashinta wanda dakyar suka samu tayi shiru, duk tambayar duniya sun mata tafada musu me yasa ta kuka amma ta ki suma ganin haka suka barta
.................................

TWO WEEKS LATER (Karku gan kaman Ina komai a gurguje a'a, yanzun labarin yasoma so don't worry😘❤️).

Gidan cike yake da yan uwa da abokanan arziki da kuma makobta Dan yau za'a kawo lefen  Amira da Zarah.

"Zarah bazaki tashi kiyi wanka bah" Anty Fatima kanwar ummi tace cikin fada.

"Anty please ki barni mana haba" Zarah tafada kamar wace ke shirin kuka.

Cike da mamaki Anty tace "Ohh haka kike son yanuwan miji su tarar dake"

"Aii su Ammi ne" zarah tace tana sake gyara kwanciyar ta.

Wani duka Anty ta kai mata a cinya tafara magana cikin masifa "ko sune sai akace kar kiyi wanka wlhi zarah....."

Tun kamin Anty ta karasa zarah ta mike tsaye dasauri saboda tasan halin ta sarai, Anty Fatima kuwa bata bar dakin ba saida ta tabbatar da zarah ta shiga bayi a idonta.

Khalifa.

"Khalifa da zaka ji magana na wlhi don't do that, dan kara fushin da Abi ke da Kai zakayi, think fah how will Ammi feel" Samir yafada cikin tashin hankali jin abinda Khalifa ke shirin aikatawa.

wata uwar harara khalifa ya ma Samir yace "mtsw ai fushin su will just be for a main time, duk yanda za'ayi ni yaron sune kuma dole su yafe min" Khalifa yafada cikin tabata.

Girgiza kai Samir yayi lallai yanzun ya tabatar khalifa bai da hankali amma duk yanda zai yi toh dole yayi ya nime mafita, "ok toh naji zasu yafe ma amma baka tunanin kunyata su a idon su Abba da Ummi and also how will zarah feel"

"mtsw ni na aike ta yawon karuwan ci" khalifa yafada irin i don't care din nan.

uhmmn Samir yayi, ya kasa gane yanda khalifa ya canza gabaki daya kaman ba khalifar daya sani ba.

Suna cikin aka Khalifa ya mike yashiga bayi dan kara watsa ruwa ya bar samir zaune baki bude yana bin shi da kallo.

Can Samir yasaki wani murmushi tuna abu daya ne zai iya ana Khalifa zuwa ya aikata abinda yayi niya aii da sauri yamike ya nufi wurin kofa ya cire key din ya fita ya kule kofar Yana Yar dariyar cin nasara.

Bayan minti Arba'in Khalifa ya fito gani Samir baya dakin kuma yasa ya furta "thank God dan wa'azi ya wuce mtsw"

A'gaggauce yafara shiryawa yana gama shirinsa Tularensa mai kamshi yafesa sannan yanufi kofa, ya daura hannu a'handle zai bude ya jita a'kule,  da mamaki yabi kofar da kallo sannan ya maida idonsa wurin key ganin ba key din yasa yaja wata doguwa tsuka yana shafa kansa cikin bacin rai, "ohh Allah Samir mtsw" yace yana furzar da numfashi mai zafi.

Sai kuma kamar wanda ya tuna abu yanufi durowar dake gefen gado tuna nan yake ajiye spare key din sa




Khalifa zai gan spare key din ko kuwa👀........

Me Kuma yake son aikatawa??

kubiyo ni dan sannin ya zata kasance.......

And pls Comment dan ban ganin Comments din ku, i need you guys to be giving opinions, kuna son yanda labarin ke zuwa ko baku so.

in Kuma kuna da tambaya akan littafin ku tambaye ni zan amsa maku, and also if any corrections pls Comment dan am a person who loves correction but not in a rude way.

Masu voting da commenting nagode, and the readers to thanks for sparing your time to read, cause Writing with out you guys is nothing.

VOTE
COMMENT
SHARE

Thanks❤️❤️❤️

'Ya Mace (Completed)✅Där berättelser lever. Upptäck nu