30

2.3K 262 9
                                    

Cikin kuka da tashin hankali Zarah ta shigo gidansu, ganin yanda zarah tashigo yasa kirjin Ummi fara dukan uku uku, "zarah meya faru kika shigo haka" ta jefo mata tambaya a'kidime.

Sake akwatinta zarah tayi ta fada a jikin Ummi tana rera kuka da karfi, sake rudewa ummi tayi tana ki min magana me yafaru koh wani abun ya faru da khalifan ne, kai zarah ta girgiza alamar a'a

"Toh fada min kukan me kike, kodai fad'a kuyi ke dashi?" sake girgiza kai tayi alamar a'a.

"toh kiyi magana mana sakin ki yayi" Ummi tace tana addua Allah yasa ba saki bane "eh" Zarah tace tana sheshekan kuka

" Innalillahi wa ina illahi raji'un zarah saki.........

*★★★★★★★*
*★★★★★★★*

"Khalifa are you stupid, shin wai Khalifa baka da hankali ne, how could you divorce your wife Khalifa" Samir yafurta cikin  tsananin bacin Rai.

"But the paper was..........

Da sauri Samir ya katse shi yace "important, important, important, dan paper ka saki matar ka Khalifa da girman ka da hankalin ka da tunanin ka Khalifa ka bani kunya I never expected this from you" yana gama fadin aka ya juya zai wuce.

"Samir" Khalifa ya kira shi.

"Don't even dare call my name" Samir yace, ya bar Khalifa a gurin baki sake, karar da wayar sa yayi ne yasa ya ciro wayar yasa a kunne ko sunan wanda ke kira bai duba shiba saboda tashin hankali.

"Kazo gida yanzun" yaji muryar Abi cikin huci.

Wani irin faduwa kirjinsa yayi, jikin sa duk ya mace cikin sanyin jiki ya mike ya nufi inda motar sa yake yashiga yabar gurin.

Yana kaiwa gida  faduwan kirjinsa ya tsanata yafara dukan tara tara saboda yasan akan sakin da yama zarah ne yasa Abi ya kira shi, aka ya daure ya shiga ciki.

Yana shigowa falo Abi ya rufe sa da fada "Khalifa wato ban isa da kaiba kenan Koh"

"Abi kayi hakuri"

"karka kara kiran sunana tunda baka dauke ni a matsayin wanda ya isa da kai bah"

"Abi Kayi hakuri sharrin shaitan ne" yafada a'hankali muryarsa na rawa ganin bacin rai karara a'fuskar Abi.

"Tunda baka da hankali ai kace sharrin shaitan, Khalifa na baka amanar yarinya ka cutar da ita ka sake ta, aure koh wata bai kai ba"

"Abi..........

Dasauri Abi ya katse shi dacewa "you are very stupid Khalifa nace karka kira suna na"

Kaman zai yi kuka yace "wlhi ban San sanda na furta mata saki bah"

aii kalmansa kara ma Abi bacin rai yayi har bai san sanda ya dauka gorar ruwan dake kusa dashi ya wurga masa a kai bah yana "mara hankali, katon banza wanda bai san girman kansa ba"

Shafa wurin Khalifa yayi yace "Abi kayi hakuri"

"Uwarka fitar min a gida Shasha mara kunya kawai"

Takowa Khalifa yayi da niyar zuwa wurin Abi yaji Abi nacewa "karka ma kuskura kazo wuri na dan wallahi wallahi sai na tsine ma"

Cak khalifa ya tsaya, mamakin fushin Abi yake dan tun tsowar sa bai taba fuskanta wannan irin fushin daga Abi bah sai yau cikin sanyin murya yace "Abi plsss"

"Khalifa nace karka fa kara kiran sunana, oya get out of my house and karka kuskura kasa kafarka a wannan gidan tunda baka dauke ni a matsayin komai bah"

Jiki a sanyanye Khalifa ya juya ya fita, Ammi kuwa kuka take tana bin khalifa da kalo dan bata taba tunani zai aikata irin wannan abin bah.

Kamin kace maganar sakin ya zagaya dangi Khalifa ya saki Zarah...........

SURPRISE AN UPDATE 💃💃💃
VOTE
COMMENT
SHARE

LOVE YOU ALL FROM MEENARLEE🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡🧡

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now