15

2.5K 288 12
                                    

Bayan Abba ya Kai gidan Baba ya shiga cikin falo, tarar dasu Abi da daddy yayi harda Mommy gaida su yayi yanda Mommy ta gaida shi zaunawa yayi a kasa kusada yayan nasa.

taro aka bude da aduwa sannan Baba ya fara magana, jiya da dare Usman yazo min da wata maganar hada Zarah da Khalifa aure, shiyasa na Kira ku dan jin ta bakin ku, mukuma tatauna yanda abin zai kasance.

Gyaran murya Abba yayi yace "ni dai baba a gani na wannan hadin da kuke sonyi gaskiya bai min ba dan yanzun kun gan abin kunyar da zarah ta aikata mana toh kuna da tabacin Khalifa zai so ya aureta? a yanda take bama wannan ba wani da namijin zai so wace tayi ciki ba ta hanyar aure bah, ni dai Ina so ku Kara tunani kar a zo ayi abinda za'ayi danasani a baya, acuci bawan Allah"

Tsaki Abi yaja yace "Kai dai Muhammad muna so mu rufawa kanmu asiri kana wani Khalifa ba zai yarda bah aii ni na haife shi bashi ya haife ni bah" cikin fada inna tace "ban fa son shashanci shawara aka zo yi ba fada bah"

" Allah ya huci zuciyar ki" suka furta atare.

"Ni dai  wannan hadin gaskiya naji dadin shi, Kai kuma Muhammad da kake batun bai maka ba baka tunani za'azo a'sami matsala nan gaba in kace taje ta aure wani ba cikin family ba, ka gan yanzun wannan maganar mun barshi astakanin mu bamu bar mutane waje sun sani ba toh in kace kar ayi na Family baka tunani wannan maganar zai fito Kuma kaga sai a fara Bata mana suna aita mana gori ni yanzun ma nike shirin cewa a hada da Haidar amma tunda Yaya yariga ni yasa nayi shiru"

"Gaskiya nima wannan hadin ya min Allah ya sanya Alheri"

" Amin"

godiya sosai Abba ya fara musu duk da ba wai hadin yake so ba dan gani yake ana so a cutar da Khalifa ne kawai.

WAIWAYA

"Alhaji ni fa abinda yafaru yau ya ban mamaki dan ga duk alamar gaskiya nan wannan yaron shi ya mata ciki amma sai karyatawa yake ba shi bane"

"Uhmmn nima na san shine nadai yi shiru ne tunda yaki amince don ni tun farko ban gan laifin zarah ba duk da itama tana da laifi, kuma laifin ta shine yardar da tayi dashi har ta sake masa jiki, mu Kuma akwai namu laifin dan binciken da mukayi aka ce mana bai da wani munanan halaye shi yasa bamu saka musu ido ba duk inda zata da shi zuciyar mu bai kai ga wannan irin abin zai faru ba saboda agani tunda munyi bincike kuma bai da wasu halaye marasa kyau, bazai iya aikata irin wannan abin ba"

"Allah zai saka mana aii wannan abinda ya faru zai zame mana darasi mukuma Kara sanya wa yaran nan ido dan in ka haifi d'a toh kai dai haifansa kawai kayi baka haifi halinsa ba, Allah dai ya bamu ikon nisanta su daga abubuwa marasa kyau"

"Amin"

"Alhaji ina son magana da kai amma ban San ya zaka dauke shi bah"

"Ina jinki"

"me zai ana mu hada auren Khalifa dana Zarah mu rufawa kan mu asiri kar ace ta auri wani ba cikin family ba yazo yazame mata masifa, kuma kasan in za'a yi auren waje dole wannan maganar zai sake dawowa ka gani sai mutane su fara bata mana suna"

"tabass kin yi tunani mai kyau zan je gidan Baba yau karfe takwas sai mu tatauna akan lamarin"

"Allah ya kyauta ya Kuma sanya Alheri"

Amin.......

CIGABA.....

Jikin Abba a'sanyanye ya shigo gidan ummi kadai ce zaune a falon ganin yadda yanayin sa yake yasa tafara jefo masa tambayarsa me ya faru daki ya nufa yanna cewa "ki kawo min ruwa"

"Tohh" tace ta nufi firge ruwa mai sanyi ta dauka sannan ta nufi dakin shi zaunawa tayi kusa dashi, sai da yasha ruwan sannan tace "Alhaji lafiya" numfasawa Abba yayi yafara ziyano mata duk abubuwan da suka tatauna Allah sarki ummi harda yan hawayenta tana godewa Allah daya bata dagin miji masu kyaun halli da badan su bane yanzun wannan maganar abinda zarah tayi ya fito waje.......

ANOTHER UPDATE AGAIN💃💃💃

#VOTE
#COMMENT
*SHARE
*FOLLOW

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now