40 - Alhamdulillah

3.9K 268 28
                                    

Bayan Wata Daya🔻

Soyayya da kulawa sosai khalifa ke nuna ma zarah tun tana nokewa har ta bada Kai😜

Zarah na gani ta Kara kyau da jiki, fatar ta har wani kyali kyali take Dan hutu da Jin dadi.

"Heart beat na fa shirya" tace tana saukowa daga bene

"Ok heart drop Ina zuwa" Khalifa yace daga ciki

Uhmmn zarah tayi dan ta kagu ta gan ta a gida

Yana fito suka Kama hannun juna suka nufi wurin mota.

Sanda ya bude Mata kofa tashiga yayi mata sumba a kumatu sannan ya kule kofar ya zagaya ya shiga sannan ya tada motar.

Gidansu khalifa suka fara zuwa taraba Mai kyau Ammi ta musu sai nan da nan take da Zarah.

Ganin yanda Zarah ta Kara haske da kyau yasa Ammi cewa "Yar nan ba ciki ne da ke ba"

Akunyace Zarah tace "bana fah da komai"

"Toh Allah ya kawo masu Alheri"

Khalifa ko kunya babu yace "Amin Ammi na, aii yan biyu ma Nike so"

Dariya sukayi Ammi tace "toh Allah ya baka su" Zarah Kuma kunya kaman ya kashe ta.

Bayan kaman awa Daya suka mata salama, Ammi kuwa sai sa musu Albarka take Dan ta ji dadin yanda Khalifa ke kula da  Zarh Yana nuna Mata so a gaban kowa.

Sannan suka nufi gidan su Zarah nan ma taraba ta musanman Ummi ta musu, tana Jin dadi yanda jikin yarta ya Kara murmure Nan ma awa biyu sukayi.

Sannan suka nufi gidan Daddy, Baba, Ya nazir, Da ya Amira sun Sha yawo sosai sai da Bayan la'asar suka ma Amira salama.

Suna cikin mota Zarah tace heart beat zan Sha ice cream.

Toh khalifa yace, ya juya mota zuwa Havilah ice cream, ya siya musu suna fitowa sai ga wani mutum ya nufe su Yana ku taimaka dan Allah yau kwana na biyar rabo na da abinci.

Juya Zarah tayi zata ciro kudi daga bag Hama abinda ta gani yasa ta sake baki tana bin mutumin da kalo cikin mamaki tace "Sagir"

Da sauri Sagir ya dago ya kale ta duk da baya ganin fuskarta sosai Dan idon shi daya lalace dayar kuma bai gani da kyau, ga Kuma wani irin warin dake tashi a jikin sa.

Zarah kece yafada bakin sa na rawa sai Kuma ya fashe da kuka yace ki yafe min da Allah, Nasan alhakin ki ne ke bi na pls, wlhi nayi na dama, Yana gamawa ya durkushe a kasa Yana Bata hakuri sannan ya fara bata labarin Abinda ya faru dashi Bayan rabuwar su.

Abinda ya faru da Sagir shi ne, wata biyu bayan rabuwar su da zarah wata rana Yana dawowa daga clubing a buge, Yan fashi suka zo suka tare motarsa suka sace shi, suka Kai shi wani daji sannan suka kule shi a wani daki, ashe wata budurwar da yayi kamin Zarah ce ta sa aka Kama shi, sanda ta sa suka Mai dukan mutuwa, nan ne abu ya same shi a ido, Kuma ta karbi duk dukiyoyin sa, rashin kudi da kulawa yasa idon ya lalace, sai da yayi sati daya a dakin ba abinci ruwa ma zu biyu a rana suke bashi, Kuma yasha wahala kamin ya samu wani mutum ya taimake shi ya fitar da shi a dajin, da Kuma ya dawo Yan uwan sa suka ki shi Dan sanda yayi kudi ya mantar dasu Dan ko taimako suka zo nema a wurin shi sai dai ya koresu yace zasu shafa Mai jinin talauci. Abinda ya faru dashi kenan.

Allah sarki khalifa da Zarah sun tausaya mishi sosai tsoron Allah Kuma ya Kara shiga zukatan su.

"Na yafe maka" zarah tace jikin ta duk yayi sanyi .

Dubu goma khalifa ya ciro ya bashi, godia sosai Sagir ya masu Yana kuka.

Bayan sun Kai gida Koh ice cream din kasa Sha zarah tayi, tana mamakin halin da Sagir ke ciki.

🔻🔻🔻🔻🔻🔻🔻

Washe gari da safe zarah na tashi tayi wanka da sallah sannan ta nufi kitchen ta hada mu su abinda zasu karya da shi tana gamawa ta jere a dinning table, suka zauna suka fara ci.

"Wannan uban ci baby hanya banyi ajiya ba" khalifa yace Yana Kane Mata ido daya

"Wani ajiya" Zarah tace tana hararar shi sannan ta Kara cewa "uhmmn heart beat bakayi maganar komawa na makaranta ba Kuma tun last week aka fara lecture"

Oops sorry my Zarah na manta ne.

💠💠💠💠💠

Bayan wata biyar

zarah ce kwance a kasa tana Shan ice cream ga cikin ta ya Dan fito.

"Kina so cutar sanyi ta Kama min baby Koh" khalifa yace daidai shigowar sa falo

Cikin masifa Zarah tace babyn ka kawai ka sani daga dawowa ko Salama babu sai maganar baby Ni dake dauke dashi baka ma damu da abinda nake Ji ba.

Da sauri Khalifa yace kiyi hakuri maman baby.

Dan tunda cikin ya Kai wata hudu Zarah ta zama masifafiya.

💠💠💠💠💠💠

Bayan wata hudu zarah ta haifi yaranta Yan biyu mace dana Namiji masu matukar Kama da ubansu, ranan suna yaran suka ci sunnan Ammi da Abi Hama ana Kiran su da Yaseen da Yasmin.

Anty Amira ma ta haihu yarta mai sunnan maman Yusuf amma suna kiranta da ummul khair.

Aisha ma ta haihu namiji Mai sunnan Abba suna kiran shi da Ahmed.

Samir ma yayi aure da wata Yar kawun shi.

💠💠💠💠
ALHAMDULILLAH ALA KULU HALIN!!!

ALHAMDULILLAH A NAN NA KAWO KARSHEN LITTAFI NA MAI SUNA YA MACE.

NAGODE WA ALLAH SWT DAYA BANI IKON GAMA WANNAN LITTAFIN LAFIYA, UBANGIJI ALLAH YASA BAN RUBUTA ABINDA ZAI CUTAR DA ALHUMA BA, DUK KUSKURAN DANA YI ACIKIN WANNAN LABARIN YA ALLAH KA YAFE MIN, KUMA DUK WANDA WANNAN LITTAFIN YA BATA MA RAI YAYI HAKURI DAN ALLAH 🙏

ALLAH YASA MU DACE, YA SHIRYA MU, YA KUMA YAFE MANA DUK KUSKUREN MU, AMIN.

GODIA TA MUSANMAN GA MASOYAN YA MACE NAGODE SOSAI DA SOSAI, ALL THE VOTE COMMENT UBANGIJI ALLAH YA SAKA DA ALHERI YA KUMA BAR KAUNA, THANKS FOR ALL YOUR HELP AND SUPPORT.

FOR THOSE OF YOU THAT I WASN'T ABLE TO ANSWER THIER COMMENT KARKU GAN KAMAR SHARE KU NAYI LOKACI NE BAN DASHI, KUMA NA GODE SOSAI DA SOSAI I LOVE YOU GUYS SO SO MUCH 💋💋💋💋

GARGADI : BAN YARDA WANI KOH WATA TA CANZA MIN LITTAFI  BA. NAGODE

MEENARLEE LOVES YOU ALL 💋

I HOPE YOU ALL WILL SUPPORT ME THIS WAY OR EVEN MORE THAN IN MY UP COMING BOOK.

VOTE, COMMENT, SHARE.
❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️❣️

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now