25

2.3K 269 6
                                    

Bayan akw angama sa lalle, suka fara shirin zuwa kamu saboda bayan sallar Asr za'afara, saida suka kara wanka sannan sukayi sallah hakaci abinci suka shirya aka musu make up Aisha gown Ash tasa, na Amira sky blue, na Zarah navy blue ne, an gudunar da kamu lfy washe gari akayi walima karfe hudu, sai gobe daurin aure
✨✨✨✨✨

Kwance tashi babu wuya yau December/22/2018 aka daura Auren zarah da Khalifa, Amira da Yusuf, Aisha da Nazir da sadaki mafi karanci na kowa dubu talatin a harabar gidan baba, gurin cike take makil da jama'a saboda Masha Allah manya manya yan kasuwa dakuma masu rike da babbar mukamai a gomnati, da wasu sarakuna duk sun halara.

Khalifa na hango cikin shadda fari kal fuskar nan a tamke kamar wanda aka aikawa sakon mutuwa idon nan tayi ja duk jijiyoyin sa sun mirmike, sai Ya Yusuf zaune kusa da shi bakin nan har kunne sai washe hakora yake kamar wanda aka ma albishirin aljanna, sai ya Nazir shi bazaka tantance ko murna yake Koh sabanin haka ba.

ba wai bai son hada shi da aishan da akayi ba, shi dai ya kasa gane me zai yi murna koh bakin ciki, su abi, abba da daddy kuwa bakin su yaki rufuwa dan murna sai ansan gaisuwa suke.........

Da sauri wata tsohuwa ta shigo gidan tana rangada guda sannan ta sannar da su han daura Auren, aii labari na isowa kunnen Amaren suka fara kuka ba ma kamar zarah kuka take kamar wace akace mutuwa zatayi, sai ihu take iyakacin karfin ta rarashin su hake amma kowace taki shiru da kyar haka samu suka dan tsagaita kukan, sanda Anty Hajiya kanwar Baba ta zo ta musu masifa sukayi shiru, sai da ta sa suka wanke fuskokinsu, sannan suka canza Kaya.

Dakyar tayi suka nufi waje aka fara daukan hoto, bayan aka angama daki suka koma  suka Kara wanka sannan Anty Hajiya ta kawo masu wasu magugunan Mata a leader tama ko wace bayani yanda zayi amfani dashi sannan ta fesa musu humra da wasu Arabian perfumes masu kamshi da dadi, ta Kara basu wani abu a kwalba wai da zaran sun kai gidansu kowace ta shafa a jikinta, da toh suka Amsa saida ta tabbatar da ta shirya su sosai sannan tace suje falon Baba ana kiransu.

Cikin sanyin jiki  suka nufi falon wanda Baba, Abba, Abi, da Daddy ne zaune da wani abokin Baba, akasa suka zauna bayan sun gaida su, nasiya sosai aka masu, hadi da fada da jan kune suma mijinsu biyayya sannan haka dawo rarashi.

Sannan suka nufi Bangaren Inna inda su Ammi ke zaune aii suna shiga falo kowace ta fada a jikin mamanta, Aisha a jikin Mamie, sai su zarah a ajikin ummi basu ma bari, su masu nasiya ba, kuka suke kowa ya kankame mamansa da kyar Inna da Ammi suka rarashe su.

Sannan haka fara musu nasiya, Ummi da Mamie dai sun kasa cewa komai sai "Allah ya muku albarka ya baku zuria masu albarka" kowai suka iya furtawa Dan aurar da ya Mace is not easy, Mamie kuwa itama kuka take Dan yanda take ji da Aisha, kasancewa ita daya take da shi dake tayata komi agida saboda haidar bai cika zama a kasa ba saboda shi pilot ne, ga ta kuma autarta.

Ummi kuwa kukan zuci take, Anty Fatima kanuwar Khalifa ce tashigo falon tace "mota fa ya iso sai kuyi sauri" kara volume din kuka sukayi da kyar aka samu aka banbare zarah daga jikin Ummi duk da aka sai da mutane uku suka rike ta.

Amira aka fara kaiwa, sai Aisha sannan zarah,wani tangamemen gidan da Abi ya Gina ma Khalifa a maitama aka nufi da ita, gidan ya hadu iya haduwa, komin gidan dai sai Masha Allah ga haske kaman Rana, Anty Hauwa ce to fito da ita daga mota, daki suka kaita sannan suka zaunar da ita akan Italian bed dake dakin.

wanka da sallah suka sata sannan suka Bata wasu tsumi sai magungunan da Anty Hajiya ta bata ta shafa suka Kara Mata wasu sannan suka Bata wata arniyar farar rigar bacci iya cinya cikin kunya Zarah tace "Adda Ni yazun wannan abin zan saka" murmushi Anty Hauwa tayi tace "eh"

"Adda yayi karami sosai pls ki canza"

"Ban fa son gardama ki shiga bayi ki canza"

"Toh tace ta shiga bayi, shigowar ta da minti biyar Adda tayi saurin gyara komai sannan takali Umaira tace ki zo mu wuce kamin ta fito" dariya umaira tayi tace "uhmn Adda wayo, yanda ke da Anty Fatima kuka min zaki mata koh" dariya Adda tayi tuna lokacin da sauri suka fita a dakin........

Zarah na fitowa daga bayi ta gan dakin wayam ba kowa, bata Kuma ji hayaniyar mutane Kuma ba da sauri ta nufi closet dake dakin ta ciro riga da wando na bacci ta zura sannan ta mai da Wanda Adda ta ajiye mata.

Falo ta nufi koh Zata gan mutane amma shiru ba kowa, baki ta sake tana bin falon da kallo har tama mance  da zancen mutanen da tazo nima, Bata ankara ba taji ta buga kafarta da wani abu ta fadi, maimakon taji ta akasa sai ta ganta a saman wani fadaden kirjin ga wani kamshi dake tashi ajikin mutumin, Shaka kamshin tayi tana gyara kwanciya a kirjin sa harda lumshe ido.

"Ke" taji muryar ya Khalifa, da sauri ta bude ido tana zaro su ganin jikin Wanda take, aii da sauri ta mike, "mtsw kin aza ni irin mazan da kike bi ne koh, toh for your information Ni ba mazinaci bane"  yana gama fadin haka ya tako wurin ta yamata rankwashi sannan ya wuce dakin sa wurin zarah ta dafe saboda tsantsar azaba tafara jin ciwon kai, daki ta koma tacigaba da kukanta.........

VOTE
COMMENT
SHARE
💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜💜

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now