33

2.3K 241 8
                                    

Da salama ya shiga falon, amsa Masa Ammi tayi, kusa da Ammi yazo ya zauna a'kasa yasa Kai a cinyarta, Abi baki ya sake yana kalon shi, mamakin karfin hali irin na khalifa yake.

"Ammi" khalifa yafada hankali yana Kama hannun ta, kauda Kai gefe Ammi tayi kaman Bata ji shi bah, ganin yanda Ammi ta basar da shi yasa wasu hawaye fara safa da marwa a fuskar sa.

"Ammi" ya Kara cewa cikin rawar murya, ganin har yanzun Bata tanka Masa ba yasa yafara kuka, yace "Ammi kiyi hakuri" da sauri Ammi da Abi suka kalle shi sannan suka Kali juna Dan zasu iya shaida tun da Khalifa ya Kai shekara goma Basu taba ganin shi Yana kuka bah.

"Ammi, Abi kuyi hakuri" yakara cewa cikin kuka.

Jin Basu ce komai ba yasa shi cewa "Ammi plsss, ki taimake Ni zan mutu, ku yafe min ko zan ji saukin Abinda nake Ji zuciya na, Ammi nayi nadama"

Baki Ammi ta bude da niyar magana sai Kuma Abi ya katse ta yace "khalifa ban Isa na baka umurni ka bi ba, nace karka sa kafarka a wannan gidan amma......

Kamin Abi ya karasa ya mike yace "Abi kayi hakuri" sannan ya juya yafara tafiya jikin shi a sanyanye, shi ma Abi sai yaji ba dadi hama Yana so khalifa ya ganee kuskuren shine.

Zarah ✍️

Tsaye take a daki tana zagaya dakin, tunanin abinda ya faru da zun take, me Khalifa da Samir suke nufi son ta suke ko me uhmmn ai ko son ta suke ba zata taba amince bah Dan tsoron maza take.

Ggiirr wayar ta ya fara kara da sauri ta dawo daga tunanin da take ta dauka.

"Asalamu Alaikum" taji muryar Samir

"Walaikum Salam" ta Ansa

"Zarah" ya kira Sunanta cikin wani irin murya

Da sauri zarah ta cire wayar daga kunnen ta, tana bin wayar da kalo saboda yanda ya Kira Sunanta, taji want iri mai da wayar tayi tace uhmmn

"Akwai maganar da nake son mu tattauna ni da ke gobe"

Jin tayi shiru yasa shi Kara cewa "plsss in kina da free time gobe"

Zarah dai shiru tayi can tace "toh insha Allah"

"Toh nagode gimbiya"

A firgice zarah tace "Eh me kace"

Dariya yayi cikin rada yace "ba komai sai mun hadu gobe darling" daga nan ya katse wayar, ya bar zarah baki bude kaman tana gaban shi, hmmmn Zarah ta sauke ajiyar zuciya ta zauna a gado, toh me Samir yake son tatauna da ita.

BAI DA YAWA HAMA KU SA RAI ZAN YI UPDATE ANJIMA INSHA ALLAH.

VOTE, COMMENT, SHARE.
✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛💛

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now