10

3.5K 433 34
                                    


💫💫WRITTEN
                    BY💞💞
                              MEENARLEE😘

Washe gari da safe tana farkawa daga bacci da kyar ta mike daga gadon ta nufi toilet, wanka tayi ta gasa jikin sosai sannan tayi alwala tana fitowa tasa doguwar riga mara nauyi sannan ta shimfida sallaya tatada sallah, ta dade sosai akan sallayar tana aduwa Allah ya rufe mata asiri ya Kuma saka mata da abinda sagir ya mata daga bisani ta tashi ta cire hijjabi ko sallayar bata nade ba tabi lafiyar gado tafara bacci, ba ita ta farka ba sai karfe goma da sauri ta mike bandaki tashiga ta yi brush sannan ta fito daga daki yanzun tafiyar ta ya dan daidaita amma duk da haka za'a San ya canza.

falo ta wuce dan wani irin yunwar dake adabbarta, ganin Ummi zaune ta buga uban tagumi tana tunani, yasa kirjinta fara dukan uku uku kaman ya hito, waro ido tayi tana dafa kirji, jikinta na kirma kamar tasake fitsari a wando, dak'yar ta hada kalmar "Ummi i-n--a k---w--a--n--a" bakinta na rawa Ummi kuwa bata ma san zarah ta shigo falon ba. saida taji gaisuwarta ahankali ta dago ta kale zarah har ta bude baki zatayi magana sai Kuma tafasa ta dauke kai tamaida shi wurin tv.

Itama Zarah ganin aka ta wuce dinning tana addua Allah yasa an rage mata nata abincin, ganin abincin datayi yasa ta saki dan guntun murmushi da ya tsaya iya lebenta sannan taja kujera ta zauna, abincin ta zuba a plate harta Fara ci sai kuma ta mike ta nufi falo ta zauna.

Duk da Ummi tagan dawowarta falo amma ko uffan bata ce mata ba saima kara tatara hankalinta datayi ta maida shi wurin film da take kallo duk da ba fahimtar abinda ake take ba, shiru falon yayi bazaka ma zata mutane na zaune ba in ba karar tv dake tashi ba, duk ba wanda yayi ma juna magana har Zarah ta gama cin abinci, suna cikin aka suka ji sallamar baba maigadi amsa mai suka yi tare da bashi izinin shigowa.

Shigowa yayi sannan yace "Hajiya dama sagir ne yazo" uhmmn kawai ummi tayi shima ganin aka ya juya zarah kuwa sai satar kallon ummi take bata San ummi na lura da ita ba saida taji Ummi nacewa "meye kike ta kallo na" a subule ta tashi  ta koma daki ta dauko hijabi tana a yana aranta irin rashin mutuncin da zata yi mishi.

Bayan tasa hijjabi Kitchen ta nufa, ta dauki juice mai sanyin gaske wanda har kankara tafara ta zuba a'kofi sannan ta nufi waje dan kada ummi ta zarge akwai wani abu tsakanin su, tsaye yake a garden yasha shadda fari sai murmushi yake ta faman zabgawa ganin fitowarta harda abinda zata tarbesa da shi, a'zuciye zarah ta iso wurin shi, cikin jin dadi sagir ya mike tsaye yana cewa "baby....." bai kaiga karasawa ba ta zuba mai juice din gabaki daya tana mishi kallo mai cike da zallar tsanarsa.

Baki sake cikin mamaki yafara bin jikin shi da kallo duk kayan jikin sa sun bace ransa a dan bace yace "meye aka zaujat" tsaki tayi tana masa wani irin kallo cikin tsiwa tace "meye haka? toh hakan na nufin karka kara zuwa gidan mu"

" why zaujat me na miki" tambayarsa ne yakara  mata haushinsa wato bayan ya gama lalata mata rayuwa shine zai tambaye ta me ya mata, ji kake tasss ta kai mishi mari "meka min fa kace aii tunda kasamu abinda kake so dani aii kace meka min, duk da ban gan laifin kaba laifi nane dana yi trusting dinka but you no what you don't worth my trust you don't worth it sagir" tafurta hawaye na ambalaya a kuncinta.

Sagir kuwa mamaki ne ya cika shi Dan bai zata fushin ta ya Kai haka ba amma da yake namijin duniya ne yasa ya boye mamaki da bacin ransa yace "haba cutie i still love you darling"yana cikin magana bai ankara ba ta wurga mai glass cup din a goshi tana cewa "you love me uhhh is that what you call love" ta fashe da dariya tacigaba dacewa "I don't love you any more, you don't worth my love i hate you na tsane ka na tsane ka kuma ban sanka, stick that to your stupid mind" tafada mishi dakarfi ta juya tayi hanyar falo tana kuka mai cin rai, sagir kuwa mutuwar tsaye yayi ga goshin sa dake mai zafi kamar me, har tafara kumburi.

Aka tashiga cikin falon ko, takan ummi dake falo tana tambayar ta meye faru bata bi bah Allah sarki abinka da uwa harta manta fushin da take daita ta shiga damuwa ganin yanda zarah tashigo, ganin inta zauna barata samu nutsuwa ba yasa tabi bayan ta, a gado tasame zarah kwance tana kuka kaman ranta zai fita a hankali ta zo kusa da ita ta zauna tama kasa rarashin ta don yanda kukan ke taba mata zuciya ji take kama ta tayata can dai tayi karfin halin cewa "zarah"

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now