27

2.2K 256 8
                                    

A haka ta nufi bayi ta dauro alwala tazo tayi sallah, tana gamawa ta dauko Al Qur'an tafara karatu ahankali cikin sanyin muryarta mai dadin sauraro sanda ta gama sannan ta nade sallayar da Qur'ani sannan ta ajiye ko wanne a majiyar sa, ta dawo gado ta kwanta dan bacci bai ishe taba........

Kwanciyar ta da awa daya taji an banko mata kofa da karfi, a firgice ta mike dan baccin ta bai yi nisa sosai ba "ke" taji muryar Khalifa, tasan sarai daita yake amma dan karfin hali irin nata sai ta basar dashi taki ansawa.

"Ba dake nake magana bah" yace cikin fada, sunkuyar da kai tayi kasa kamar wata kurma, ganin har yanzun bata ansa masa ba yasa ya nufe ta da karfi ya kama gashin ta yafara ja yana cewa "sai na cire wannan rashin kunyar taki, ina kiranki kinki amsawa koh"

"aii suna na ba ke bah"

Kara jawo gashin yayi yace "rashin kunya zaki min" aii saboda tsantsar zafin da kanta kemata zarah bata San sanda ta furta "wayo Allah na Ya Khalifa kayi hakuri dan Allah bazan kara ba pls" sake ta yayi yace "better and make sure kin share duka gidanga and mop it"

Kai zarah ta daga alamar taji murmushi Khalifa yayi yace "good girl" sannan yafita a dakin

Shafa kanta zarah tayi ta nufi wurin madubi ta fara dubawa ganin yanda jijiyoyin kanta suka mike ga idonta yayi ja yasa ta cewa "shege kawai mugu ban yafe bah"

Aka ta nufi wurin da hulan kanta ya fadi ta dauka ta sa, sannan ta nufi falo isowarta falon yayi dai dai da shigowar Anty Fatima da umaira cikin salama amsa musu tayi tana kirkiron murmushi  dan karsu gane akwai damuwa atare da ita, "Ina kwana" ta gaishe dasu cikin fara suka ansa, suka zauna akujera

"Ina ya Khalifa koh bai nan ne" dariyar da bai kai ciki ba tayi tace yana ciki in kira muku shi, "a'a yi zaman ki abinci muka kawo.... Sauran magana makalewa Anty Fatima tayi saboda ganin yanda fuskar zarah ya kumbura ga idonta har yanzun yayi ja "me ya same ki a fuska aka" ta tambayi Zarah, murmushi Zarah tayi tace ba komai tana sunkuye kai kasa.

Umaira tace "toh meya same ki a goshi nagan kamar wurin ciwo yayi"

Uhm uhm suka ji Khalifa na gyaran murya dan tundazun yake tsaye yana kallon su, "lah ya Khalifa Ina kwana" suka gaishe dashi tare "lfy"

"uhmmn ya Khalifa nace meye samu matar taka agoshi" jin tambayar yayi cikin bazata, da sauri ya dago ya kali zarah ganin yanda goshin ta yayi kumbura da ciwo yasa yafara ehem ehem dan shi harga Allah bai san taji ciwo a wurin bah kuma yagan kallon tsuma da Fatima ke binsa dashi, wani karya zai musu yanzun dan yasan in suka fada ma Ammi sai tayi fushi da shi sosai.

ya Khalifa da uhmmn ya ansa yana kallonta "baka fa amsa tambayar mu bah" jin muryar zarah sukayi tace "faduwa nayi daga bathtub.................. 

VOTE.
COMMENT.
SHARE.
💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚💚

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now