21

2.4K 483 6
                                    

This page is dedicated to every fan of this book love you guys so much😩😘❤️❤️❤️❤️

Zarah

Bayan ta gama kuka mikewa tayi, tashiga bayi ta wanke fuska sannan tafito ta gyara fuskarta sannan ta nufi falo. Amira da Ummi tatarar zaune suna tatauna akan kayan dakin daza'a siya ma Amira.

A'hankali tazo ta zauna a daya daga cikin kujerun, wanda yasa ummi dagowa hadi dacewa "yauwa zarah ke ma kizo ki zaba naki" tana mika mata iPad din dake hannunta

"Ummi me zan zaba" Zarah tace cikin rashin sanin abinda tace ta zaba.

"Kayan daki mana" ummi tace tana murmushi dan wani dadi take ji zata aurar da yan matan ta

"Wait ummi me zanyi da kayan daki bayan ya Amira ce zatayi aure" tafada tana dan waro ido, dariya Amira tayi tace "ke ma aii Amarya ce, dan next month za'ayi naki auren  da ya Khalifa kuma hadawa hakayi da nawa"

Cikin ruduwa tace "ban fa gane me kuke nufi ba" tsaki ummi taja tace "toh ina ruwana da ganewar ki da rashin aka nawa dai ki zauna ki zaba duk wanda ya miki dan Abban kune yace a mishi total din komin da kuke so"

"No ummi ku zabar min duk wanda ya muku" tafada idanuan tana kawo ruwa daga nan ta nufi daki....

Khalifa

Zaune yake a garden shi da abokinsa "khalifa me yasa baka jin magana ne, have been telling you times without number just live that girl alone ka rungume kaddarar ka, saboda ni duk abubuwan da ka fada min yafaru, ba laifinta bane laifin Sa...."

Katse sa khalifa yayi cikin zafin nama ganin Samir na son Kiran sunan wanda yafi tsana a duk fadin duniya, wani zafi yafara ji a zuciyar sa, "Samir just stop" yace cikin tsawa

Tsaki Samir yaja yace "stop what" kau da kai Khalifa yayi gefe ya cigaba da latsa waya "man don't decieve your self you're in love with this girl" Samir yafada yana kallon sa.

"mtsw for goodness sake Samir would you just live me alone" yafada a fusace, girgiza kai Samir yayi yace "ni dai abinda zan fada ma shine kayi ma su Abi biyayya da wannan Auren kuma.....

Bai karasa ba khalifa ya mike a'fusace ya nufi ciki dan wani tsanar Samir ya fara ji taya ma zai ce ya auri karuwa mtsw kuma wace bata da kunya.

Kalon mamaki Samir ke binsa dashi shi dai bai gan me yace a nan da bai dace bah girgiza kansa kawai yayi yace "khalifa Allah ya shirya ka"

Daganan shima ya mike ya nufi motarsa saboda yasan, ko ya bi khalifa daki fada zasuyi shi kuma bai son hakan tafaru..........

Sai safa da marwa khalifa yake a daki, ya kasa gane me yasa kowa ke son ya auri Zarah, duk da shima wani bangare na cewa ya amince amma he doesn't want to accept the fact, babbar abinda ke cin ransa shine ba budurwa bace,  maganar samir ne ya dawo masa

*Man don't decieve your self you're in love with this girl*

"Mtssww ban son ta" yafada kaman wani mahaukaci kansa yafara shafawa ganin har yanzun bai bar tunani bah, yasa yadauki wayar shi yashiga Muslim pro yayi playing qurani suratul Baqara ya kwanta ya lumushe ido yafara bin karatun hankali...

. ★★★★★ .

Kwance take agado idon ta lumushe kamar wacce ke bacci duniya duk ya mata zafi da kunci, dukan mazan dake afamilyn su an kasa hada ta da kowa sai ya Khalifa wanda ke mata kalon karuwa.

firgit ta tashi jin an mata duka a cinya, Aisha da Batool ne tsaye suna dariya cikin shagwaba tace "wlhi sai na rama"

"haba toh kiyi hakuri" batool tafada cikin roko tana hade hannuwanta.

"uhmmn me kike ta tunani aka baki ji salamar mu bah" Aisha tace tana zaunawa abakin gadon

"bakomai fah just laying down and resting" tafada tana Sosa kai.

"Ina chocolate din nan dakika ce zaki bani" batool tace kamar wata karamar yarinya, dariya suka fara zarah nacewa "wlhi yakare sai Ya Ahmed ya kara siyowa" murmushi Aisha tayi tace "aii Amarya bata laifi" nan da nan farar dake fuskar zarah ya koma ciki ta tamke fuska.

Yayyy 3k reads and 446 votes💃💃💃 thank you so much guys i really appreciate ❤️❤️❤️

VOTE
COMMENT
SHARE

Love you all💋💋💋

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now