9

3K 398 22
                                    

    BISMILLAH RAHMANI RAHIM

            Masoyan 'YA MACE kuyi hakuri da rashin update din da banyi kwana biyu bah ku ne baku voting yanda ya kamata shiyasa nake jin sanyin guyiwar posting duk da haka masu voting da comments ku cigaba nagode sosai .......

Abba ne yayi karfin halin cewa "me ya faru kike salati" jin abinda Abba yace yasa ummi juyowa cikin tashin hankali, ganin sunyi cirko cirko suna kallonta, yainda jikin zarah ke kirma, tana aduwa Allah yasa kar Ummi ta gane, in koh aka toh sagir ya gama daita kenan dan tasan ummi da nazari akan abu musanman akan 'yayanta mata.

Bata gama tunani ba taji ummi tace "kar dai kuce min baku gan yanayin tafiyarta ba" duk juyowa sukayi kowa ya zuba mata ido domin tabbatar da abinda ummi tace zarah kuwa sai zufa ne ke ta faman karyo mata, innalillahi wa inna ilayhi rajiun na shiga uku ni zarah Allah gani a gare ka karufa min asiri, taketa nanatawa a'ranta.

Kura mata ido Abba yayi sosai yana nazarin ta, can sai kuma yace "zarah" wata numfashi zarah taja cikin tsoro tana dafe daidai zuciyarta, rawar jikinta na dada karawa, ba wasa Abba yace "zonan" ahankali tafara takowa kusa da Abba kirjinta na wani irin bugu kaman yahito, tana kokarin daidaita yanayin tafiyarta, ido ta runtse sosai jin wani irin zafin da ya ziyarce ta, har bata san lokacin da ta saki wata kara ba.

A'arzuke ummi ta mike dama tun dazun take zargin wani abu duk da tana addua Allah yasa zargin taba gaskiya bane ganin ta kasa tafiya ne yasa zuciyar ta tayi wani irin bugawa bata San lokacin data tashi ta isa gurin ta bah ta gaura mata wani irin gigitacen mari da yasa zarah ta dauke wuta tana cewa "daga gidan ubanwa kike" Abba ne ya taso dasauri yana kokarin janye zarah daga wajen juyowa tayi tana ma Abba wani irin kallo duk da ya gan kallon da take mai baice mata komai bah illa janye zarah da yayi, ya zaunar da ita a wurin shi Dan yasan halin ummi sarai akwai hakuri,juriya da saukin Kai da wuya kaga fushin ta amma duk  ranar da kayi nasarar kullar da ita toh za kuyi ba dadi.

"Zo ki zauna" Abba ya fada,  bata musa ba tadawo kujera ta zauna tana girgiza kafa da alamar masifa girgiza Kai kawai Abba yayi Dan yasan yau an tabota kenan Abba ne ya kirata cikin taushin muryarsa zarah na'am ta amsa kirjin tana dukan uku uku dan bata San tambayar da za'a mata ba.

"ina kika je da har zuwa wannan lokacin kike dawowa kuma da wa kika fita" Abba ya fada ba alamun wasa acikin muryar sa cikin inda inda tace "da sagir duk da wata zuciya nace mata tayi karya tace da suka gaida abokin sagir da matarsa. Agidan sunar saita nufi gidan su batool.

Abba yakara cewa "daku ka fita Ina ya kaiki Dan mun zagaya gidan Yan uwa Kuma kowa cewa yake basu san inda kike ba asalin ma Basu ganki yau ba" wani irin boyayar ajiyar zuciya ta sauke tana hamdala a ranta da batabi shawarar zuciyar ta bah da'ata tona wa kanta asiri ummi kuwa ji take kaman ta jawota ta lakada mata duka in zai yiwu ma ta hada da Abban dan gani take suna ba'ata mata lokaci.

Zarah: gidan abokinsa da matarsa ta haihu

Abba: "me ya tsayar dake awurin"
Zufa ce tafara karyo mata kota ina cikin sosa Kai tace Uhmmn ehmn eh dana ga magrib ta kusa shine naje wurin matar abokinsa nace ni zan wuce sai ta tace wa zai maida ni Dan sagir sun fita da mijin ta nace toh ni zan hau adaidaita tace na tsaya mana su dawo nace toh haka na yita jiran su basu suka dawo bah sai takwas da rabi Kuma anguwar akwai nisa

Abba: toh mai yasa kika kasa tafiya

Wani irin bugawa zuciyar ta yayi ta adiye wata yawu mai matukar dacci tace a gidan sunar ne ban San wuka na gurin bah na taka.

Abba ya juyo ga ummi yace "kin dai ji koh ba abinda kike zargi bane"

Ba tsamani ta tsinkiyo muryar ummi tana fadin muga wurin da sauri zarah tace "i..n..a" bakin tana wani irin rawa kaman zasu fado.

Harara Ummi ta bankaro mata tace "kafar" ahankali ta daga skirt ta nuna musu kafar da aka nanade sa da bandage,  uhmm kawai ummi tayi tatashi ba dan ta yarda ba. Abba ma yabi bayanta Yana fadin "Allah ya kyauta" suka ce Amin daga nan kowa ya tashi Yana mai jinjina wannan alamarin tana ganin kowa ya ta tashi itama ta mike da kyar ta nufi daki tana jinjina ma kanta yanda ta shara wannan karyar cikin minti na kalilan tana mai jawa sagir Allah ya isa

na san zaku so kuji yanda ta  samu bandage toh sagir ne ya samata a kafa dan in an tambayeta me ya sa tafiyar ta ya chanza ...

wannan daren ummi da zarah ba wanda yayi bacci cikin su ita ummi tana ji a jikinta ba gaskiya Zarah ta fada bah akwai abinda take boyewa zarah kuwa tunanin mijin da zata aura nan gaba take dan baza ta iya auran sagir bah yaci amanar soyayyar da take masa, ji take duk duniya bah Wanda ta tsana kaman sagir Kuma ta san komin daren dadewa sai gaskiyar ya yito
sagir kuwa bacci yayi mai dadi dan rabon da yayi irin wannan baccin harya manta gani yake fushin ta is just for the main time gobe zai je yamata dadin baki ta yafe mai.

KUNA JIN DADIN YANAYIN LABARIN ???

IN KO HAKA TOH KUYI VOTING DA COMMENT DAN WANNAN LABARIN ZAI ZO DA SABON SALO DAN YANZUN LABARIN YA FARA

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now