24

2.3K 292 10
                                    

Washe gari Ummi ta kawo musu Mai gyaran jiki daga Maiduguri, nan da nan matar ta fara aikin ta, in Amira da zarah zasu makaranta sai su sa hijabi har kasa da nikab, kamin sati ya zagayo duk jikin su ya canza, yayi wani smooth Yana wani walkiya da sheki.

kullum kuma suna cikin kasuwa suna siyayya, yau a gajiye suka dawo daga kasuwa dasu batool da Aunty kareema dan tun last week da suka zo basu koma bah.

Cikin gajiya Anty Karima tace "Wash jikina duk Yana min ciwo nagaji"

"Wlhi ni ma jikina duk yayi laushi" Amira tace tana kawanciya a gado.

Zarah ce tayi karfin halin, kawo musu abinci, sanda suka ci suka koshi sannan suka mike duk suka dauro alwala kowa ya fara rama sallolin sa...............

Gobe za'a yi sa lalle da kamu Kuma yau su Zarah suka gama exams din su saboda tun wata dayan da ya wuce suka fara. Gidan ya fara cikawa, Da yanuwan duk da gobe zasu gidan Baba dan a can za'ayi komai.

"Zarah kun karbo dinkunan ku duka Koh" ummi ta tambaya, "eh ummi tun jiya muka karba, "toh yayi kyau sai ku fara shirya kayan ku Dan gobe da zaran angama sallar fajr zamu gida Baba.

"Ok ummi aii mun kusan gamawa" "toh" ummi tace daidai fitowar ta daga dakin "Wai Anty yanzun bazan yita ganin ki kullum kuma bah" zarah tace cikin sanyin murya "eyya sorry my Zarah zamu yita waya koh" Amira tace itama jikin ta a'sanyanye Dan she just can't believe she's living Zarah, Ummi, Abba, da su ya nazir she's going to miss them all.

Uhmmn kawai Zarah tayi saboda tun kamin a daura Auren tada ya Khalifa tafara tausayawa kanta, abu dayan dake damunta shine taya zatayi zaman aure da mutum dake mata kallon  mazinaciya.

Cigaba da dauka kayan da zasu sa agidan baba sukayi basu suka kwanta ba sai karfe Sha biyu. Washe gari bayan sallar fajr a dadafe kowa yayi wanka ya shirya suka shiga mota sai gidansu Baba.

Suna kaiwa gidan faka mota akayi suka fito, duk da gari bai gama wayewa ba amma gidan cike take da jama'a sai Kai da kawo ake ana hayaniya, ciki suka shiga, gaishe gaishe suka fara wasu na tsokanar su, sanda suka gaida Inna da Baba sannan suka koma mota suka ciro akwatunan su, suka nufi bangaren da aka ware musu da kawayen su, part din dauke yake da daki uku duk wace da toilet a'ciki sai falo daya.

Da salama suka shiga falon, da sauri batool tazo ta rungume zarah tana "at last kun zo wlhi I thought jiya Zaku zo" murmushi Zarah tayi bata ce komai ba dakin da su Aisha ke ciki, suka shiga ajiye akwatunan ta Zarah tayi a gefe daya sannan tazo ta kwanta a gado, dan bacci bai ishe taba.

Khalifa 💞

Mtssww ya ja dogon tsaki dan yakasa samun mafita yanda zai dakatar da wannan auren, duk wace mafita ya Samu sai Samir ya toshe Masa hanya wani irin haushin Samir yake ji, gashi Kuma dauren Aure ya rage kwana biyu, yanzun ya zai yi, wata bangare a zuciyar sa tace toh in ka aure ta ka sake ta Mana, wata tace kar kayi haka su Ummi da Abi zasuyi fushi da Kai mtsw shi babbar matsalar sa shine yanda zai hada inuwa  daya da ita Dan wani irin tsanar da yake Mata..


Ammi ce to shigo dakinsa tana "Khalifa kayi sauri mana have been waiting for you"

" oh sorry Ammi Ina zuwa" yace yana saukowa daga gadon sannan ya dauki key in motarsa ya bi bayan Ammi.....

Sai karfe tara zarah ta tashi wanka tayi, sannan aka fara masu makeup, shiryawa sukayi cikin wata atamfa mai tsada komin jikin su iri daya harda Aisha, sunyi kyau sosai hotuna aka fara daukawa sannan aka yafa musu mayafi mai net net sai da aka kara daukan hoto sannan suka nufi wajen sa lalle a harabar gidan.

Don't forget to Vote.

ANY MISTAKE OR CORRECTIONS COMMENT BELOW

Share pls.❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️❤️

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now