2

7.4K 640 13
                                    

Zarah 'ya ce a gurin Alhaji Muhammad da Hajiya halima wace suke kira da Ummi. su hudu iyayenta suka haifa itace auta Zarah yarinya ce yar kimani shekara sha takwas, a yanzun tana ABU zariya in da take karanta nursing, Zarah fara ce amma ba can bah, fatarta mai sheki ce tsabar hutu da kulawa tana da kyau sosai fuskar ta dauke yake da dogon hanci da idon ta daidai misali tana da bakinta daidai mai dauke da pink lips siririya ce hama bah sosai bah tana da shape dinta mai kyau da daukar hankali.

*Asalin su*
Alh Mahmud shi ne sunan kakan Zarah Yana da mata daya mai suna Fatima auren soyayya sukayi sun hadu ne a kasuwa inda Mall. Mahmud shi mai saida kayan miya ne ita kuma mai saida fura ce, haduwar su ta kasance ne ran da innarta ta aike ta siyan kayan miya daga haka suka fara zumunci har ya Kai ga soyayya suka yi aure.

Alh Mahmud dan garin kastina ne a karamar hukumar daura, ita Kuma Fatima 'yar garin malunfashi ce suna zaman lfy da mutunta juna suna da yara biyar mallam Mahmud kuma yayi iya baki kokarin sa dan ganin sun Sami ilimin addini dana boko.

D'ansu na farko Alhaji Usman Dan kasuwa ne mai zaman kansa Yana da mata daya Hajiya zurha, wace ake Kira da Ammi, mace ce mai kwaici da sanin ya kamata Kuma bata da hayaniya ko kadan, suna da yara uku khalifa shi ne babban d'an su sai kanen sa biyu Fatima da umaira duk sunyi aure.

Mai biye mai Hajiya Rahma tana aure a kano da yaranta hudu hauwa, Faisal, Mahmud,sai auta karima.

Mai biye mata Alh umar 'ya'yansa biyu haidar da Aisha.

Sai Alhaji Muhammad matarsa daya Hajiya halima suna da yara hudu Nasir, Ahmed,Amira sai auta Zarah.

Sanna Hajiya bilkisu itace auta yaranta biyu yaseer da batool.

Duk shekara sai sun biya ma iyayen su hajji da umra Kuma kullum cikin kyautata musu suke dan yanzun sun dawo da iyayen su kaduna da zama kasancewa dukan su a kaduna suke ban da Hajiya Rahma dake aure a kano duk cikin su ba talaka dan kowa nada arzikin sa daidai gwargwado.

Amma Alh Usman ya fisu kudi nisa ba kusa bah a familyn suna da hadin Kai dan hana zumunci sosai suna kuma taimaka wa juna dan tun da suka taso har sukayi aure basu taba samun sabani ba a haka basu nuna babanci cikin yaransu wannan kenan.

*******
Yan matan familyn ne zaune a gidan Alhaji Usman wato Abi dan haka dukan su suke kiransa gashi da son yara kamar me, masu chatting nayi ,masu hira nayi ya inda wasun su suke hira a waya sallaman da suka ji hanyi ne ya jawo hankalin su
ga kofa.

Alhaji Usman ne tsaye a bakin kofa ga jakar aiki a hannun sa  da alama daga office yake, dasauri suka mike dukan su suka nufe shi suna Abi oyoyo yainda wasunsu ke Abi sannu da dawowa, fuskarsa dauke da fara yace "yauwa yaku ke" duk suka amsa da "lfy"

Murmushi yayi yace "toh madallah Allah ya muku albarka" suka ce "amin" ya karacewa "Ina amaryata" zarah dake tsaye a baya tana kiciniyar zuwa garesa amma ba dama tace "gani nan magida sun hana ni ganin ka" ta idasa maganar cikin shagwaba duk suka fara dariya dan haka take ce mai in ya kirata amarya ita kuma tace maigida.

Dan tun lokacin da take karama yake kiranta da amarya tun bata fahimtar ma'anar sunan har ta fahimta lokacin zaune suke a family house dinsu dake kaduna yace mata "amarya ta" tafara kuka har da bubuga kafa, tana ita fa ya daina ce mata amarya ita ba matarshi bace Kuma ya mata tsufa.

Dukan su dake zaune a falon suka sa dariya jin abinda tace shima dariya yayi mummy wato Hajiya balikisu tace "ka dai ji koh yarinya tace bata so kamata tsufa" tun daga lokacin haka fara tsokanarta da amaryar Abi sai tafara kuka itafa ba amaryar shi bace wasu lokaci ta gudo wurin ummi tafara mata kuka tace "mata ummi kin gansu koh suna ce min amaryar Abi" haka ummi zata rarashe ta.

A lokacin da ta Kai 12yrs ta dan yi wayo in suka ce amaryar Abi sai ta share su, in kuma Abi ne ya kirata da amarya sai ta daure fuska tana zunburo baki ganin haka bai sa ya fasa ce mata amarya bah itama tafara ce me mai gida.

**********

Murmushi Abi yace "toh a bari na je nayi wanka" a sauko lfy suka masa haka ya dawo ya same su har matarsa shima ya zauna haka cigaba da hira sai gab da magrib suka ce za su wuce yace toh ya ciro bandir din dubu daya ya basu suraba godia suka mai a haka suka yi ma juna sallama kowa ya nufi gida

Don't forget to vote and comment because they are needed
For votes and comments you just have to tap that little star🌟over there for voting and 💬 this for comment.. Thank you 😘
Vote 💞 AND Comment 🙏

'Ya Mace (Completed)✅Waar verhalen tot leven komen. Ontdek het nu