36

2.3K 247 10
                                    

Sai Bayan ishai aka samu khalifa ya farfado, duk likitocin sun jigata dan sun Sha wahala, Bayan ya farfado suka mishi duk abinda yake bukata sannan aka mishi allurar bacci dana pain killer.

Ammi ce zaune a kujera kusa da shi ta zuba mishi Ido tana kallon shi yanda duk kamanin sa ta sauya duk ya canza, a'hankali ta share hawayen ta tacigaba da godewa Allah.

Washe gari khalifa karfe takwas ya bude ido dasauri yakara runtse su ya saki wata razananiyar Kara sannan ya dafa zuciyar shi, da sauri Ammi dake  zaune kan sallaya ta mike ta taho gare shi tana cewa "khalifa"

Yana ganin Ammi ya kama hannun ta gam yace "Ahhh Ammi zan mutu zafi nike ji, Ammi zafin yayi min yawa"

Abi da shima dawowar sa kenan daga masalaci yayi saurin fita a dakin Dan sannar da likitan khalifa ya tashi ko.

Bayan barin Abi dakin ya Kara damke hannun Ammi yace "Ammi ki yafe min, mutuwa zanyi ahha" sai Kuma jikin shi ya sake lagwab numfashin sa ya dauke.

Khalifa!!!  Ammi tace atsorace tana girgiza shi, da sauri Abi ya shigo da likitan da wata nurse, ganin Ammi na girgiza Khalifa yasa su cewa "me ya same shi?" Ammi na ganin su tace "Baya fa numfashi" yanda tayi maganar jikin ta duk yana kirma yasa kirjin Abi bada dam, da kyar aka fitar dasu daga dakin.

Bayan minti talatin sai ga likitan ya fito, ya taho wurin su, cikin dashashiyar murya Ammi tace "ya mutu" tana kalon likitan hawaye na safa da marwa a fuskar ta, murmushi likitan yayi yace "madam calm down yaron ki yana nan bai mutu bah" wata  wawiyar ajiyar zuciya suka sauke atare sannan suka ce "Alhamdulillah Allah mun gode ma"

"Toh me ya Same shi dazun" Abi ya tambaya

"Toh zamu iya cewa the pain was unbearable shi yasa"

"bazaku iya wani Abu akan shi bah"

"Eh toh mun mishi allurar rage zafi Ko, duk da in ya farfado zai ji zafin amma bazai kai irin wannan  ba"

"Toh mun gode Allah ya saka maka da Alheri"

"Amin"

......................

"Samir ba zanyi ko wani event ba that's final"

"Haba sweet heart ko dinner baza'a yi bah"

"Ko kamu nace ba zanyi bah, walima kawai zanyi shi ma dan ya zame mun dole" Zarah tace ranta a'dan bace

"Baby please ki........

Aii kamin ya karasa Zarah ta katse wayar tana "haba mutum sai nacin tsiya mtsw" mamakin naci irin na Samir take tace batayi dole ne, toh ita yanzun ya zatayi zama dashi a gida daya Dan ta tsani in tace Bata son Abu a yita damun ta.

###########

"Ammi wai bazaki daina wannan kukan ba" Aunty Fatima tace cikin damuwa, ganin yanda fuskar Ammi ya kumbura saboda kuka ga idanuan ta sunyi ja, duk ta hargitse kaman ita ke ciwon.

"Ammi" su kaji muryar khalifa.

"Uhmmn khalifa" Ammi tace tana kokarin taya shi ya zauna

Ouch yace Yana dafa zuciyar shi.

Da sauri Ammi tace "kana jin zafi ne"

Kai ya gyada Mata alamar "eh"

Dai dai nan likitan  da Aunty Fatima suka shigo, matsa gefe Ammi tayi likitan ya fara duba shi Yana gamawa ya rubuta masu magungunan da za'a siya da abubuwan da zasu bukata, karba paper din sukayi suna mishi godia.

Kamin kace asibitin ya cika da yan uwa da yan dubiya, khalifa kuwa sai baza idanua yake ko zai hangi sahibarsa tunda  yann gidan sun zo, har saida Ammi ta tambaye shi wani abu yake nema, yace "a'a"







Nasan zuciyar wasu nata dukan Tara tara kar khalifa ya mutu🤣🤭😜

Vote, comment Share 🙏🤎🤎🤎🤎🤎
🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎🤎

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now