18

2.4K 294 14
                                    

A haka ya shafa mai ya zura riga da wando ta bacci ya kwanta amma sai me bacci ya ki dasukan sa, juyi juyi ya fara ganin har yanzun bacci bai dauke shi ba, yasa ya lumshe ido ko bacci zai dauke shi, da sauri ya bude ido yana Jan tsaki dan in ya lumshe ido ba abinda ke zuwa masa sai hoton fuskarta, shi wai meke damun sa ne, duk sanda yazo bacci sai yayita mafarkai da ita, hanya Wannan yarinyar ba magani ta maka bah wata bangare a zuciyar sa ya tambaye shi, wani irin dogon tsaki ya ja yace taya ma zata min magani
🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ZARAH.

Karfe bakwai ta tashi daga bacci da sauri ta mike tayi wanka da alwala sannan ta fito tayi sallah, a gaggauce tayi shiri kasancewa ta kusan latti, da sauri ta nufi falo isowarta yayi daidai da fitowar ya Ahmed, kallon mamaki ya Ahmed ya fara aika mata saboda yau ne ranar farkon da ya gan zarah tasa hijabi har kasa harda nikab, dan ko zata sa hijabi toh iyakaci guyiwar ta yake tsayawa nikab kuwa bai taba ganin ta dashi ba, duk da zuciyar sa cike yake da mamaki bai ana shi tumurmuke fuska ba, "Ina Zaki" yafada fuskar sa tamke, "uhmmn Yaya Ina kwana" tace cikin tsoro, dan daga murya ya Ahmed yayi yace " nace ina zaki koh nace gaisuwar ki nake so" muryar zarah na rawa tace "kayi hakuri Yaya makaranta zani"

"toh sai kizo na sauke ki" yafada Yana nufar waje sum sum zarah ta bi bayan shi.

Tuki ya Ahmed yake ahankali ya inda zarah ke wasa da biron dake a'hannunta, har suka isa makarantar motar shiru yake, bamai magana daidai wurin department dinsu zarah yayi parking karfe nawa zaki gama lectures ya tambaya fuskarsa ba tamke, karfe uku tace tafita a motar jikin ta a'sanyanye, tafara tafiya cikin nutsuwa zuwa lecture hall.

********

Karfe uku Bayan sun gama lectures da zasuyi ran fitowa tayi dan tunda ta shiga hall din bata fito ba sai yanzun ko break bata jeba, cafe inda ta gan Aisha da batool zaune ta nufa tana isowa garesu salama tayi musu hadi da zaunawa, ciki ciki suka amsa kamar basu taba sanin taba, cikin karayar zuciya tace "me na muku, kuke min haka"

duk da sun ji sanyi ajikin su yanda tayi magana bai ana su kau da Kai ba kaman basu san da zamanta a gurin ba.

"ba daku nake magana bah" tace cikin rawar murya.

"Me kike son muce miki" batool tace cikin baccin rai, kuka zarah ta fashe musu dashi tana shesheka tace " baku Sona kuma ko, kuma kun tsane ni baku son ku gan ni kamar sauran, na san na muku laifi pls dan Allah ku yafe min" tafada cikin kuka ta sauka daga kujera ta durkushe akasa tana kuka iya kacin karfin ta, da sauri Aisha da batool suka mikar da ita ganin yanda hankalin mutane suka fara  dawowa kansu suna kallon yanda zarah ke kuka.

Wurin wasu bishiyoyi da mutane basu cika wucewa ba suka nufi da ita suka zaunar da ita a kujerun dake a wurin, suma zaunawa sukayi kusa da ita Aisha tafara magana "bamu tsane ki ba, bamu kuma daina sonki ba mun dai yi fushi ne dake yanda irin wannan abin zai faru kuma baki sannar damu ba and you know we are besties, aii dole muyi fushi dan yanda bamu boye ma juna komai, bamu zata zaki boye mana wannan maganar ba, duk da dai mun san, lokacin kina cikin tsoro baki so kowa ya gane but we still love you the way we always do"

batool tace "and pls dan Allah kiyi hakuri kinji muma munyi kuskure" cikin kuka ta rungume me su ji take kamar han cire mata rabin nauyin da take ji azuciyar ta suna cikin haka suka ji horn da sauri suka dago ganin ya Ahmed ne yasa zarah tace "to sai gobe tana daukar Jakarta" dadan gudunta ta nufi wurin motar ta shiga tana "Yaya Ina wuni"

Kalon tausayi ya Ahmed ya bita dashi, saboda tun dazun yake kalon su har sanda ta durkusa a kasa shima yana matukar tausayawa kanwar tashi amma he just want her to realize her mistake which she has dan haka bazai din ga takura mata kuma ba su Aisha ne suka katse shi daga tunanin da yake dacewa "Ya Ahmed Ina wuni"

"lfy ya makaranta"

"Lfy kalau" suka amsa

"toh Ku shigo mu sauke ku mana"

"a'a ka wuce dai"

"Ku shigo kun san ban fa son gardama and am pretty sure baku zo da mota ba" dariya sukayi suka shigo, hira suke jefi her da ya Ahmed suna dariya, har gida ya sauka kowanen su sannan suka nufi nasu gidan.

********

Tana zauna a daki tana magana dasu Aisha a waya, ummi ta shigo da sauri ta katse wayar tana cewa "ummi lfy me yasa baki Kirani nazo ba" tafada cikin ladabi kanta a kasa, murmushi ummi tayi dan tana son wannan sabon canjin da take gani a tare da Zarah yanda ta Kara hankali da nustuwa " kiyi sauri ki shirya khalifa ya zo wurinki" zaro ido zarah tayi tace "KHALIFA" ............

Masoyan ya mace wannan shafin naku ne nagode da kulawarku Yan uma, i just want to thank you all

Love you guys so much for

I know the chappy is boring but next will be fun inshallah

VOTE
COMMENT
SHARE

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now