34

2.4K 242 17
                                    

Tun rannan da abin ya faru, khalifa bai Kara zuwa gidan ba, kullum Yana cikin daki Yana kuka rayuwa ta Masa kunci, aiki ma ya dai na zuwa, rabon sa da abinci kwana biyar kenan, duk ya rame, yanzun ma kwance yake a daki Yana fitar da numfashi, sama sama, ga jikinsa duk ya bace da amai dake tare da jini, duk kamanin sa ya canza kaman ba khalifa bah.

Bangaren Ammi kuwa Jin khalifa shiru, Koh Ta Kira ba'a dauka ta shiga damuwa, data tunkuri Abi da maganar cewa yayi ta kyale shi iskanci ne irin nasa.

"Toh Alhaji baka tunanin akwai abinda ke damun shi, shiyasa bai dauki waya taba" ummi tace cikin tsananin damuwa Dan tana ji ajikin ta danta ba lfy yake bah.

"Nace ki bar shi sanda ya gama iskancin sa zai kira"

"Ni dai Ina ji ajiki na Khalifa is not safe, Koh muje mu duba shi"

"Wai zu nawa Zaki tambaye ni, nace a'a no means no Kuma in kika je ba da sani na ba ban yafe ba" Abi na gama fadin haka ya mike ya bar dakin.

Ammi Kuma kaman tayi kuka ta rasa meyasa Abi ke aka kamar ba Dan shi ba, Kuma tana ji ajikinta something is about to happen to her son, da sauri ta dauki wayarta ta danawa Umaira Kira.

"Asalamu Alaikum Ammi ya gida, ya Abi" Umaira tace cikin Jin dadi

"Walaikum Salam, Abi na lfy, Umaira kina gida"

"Eh Ammi me yasa kika tambaya"

"Dan Allah Umaira kije gidan Yayan ki ki duba min lafiyar sa, I don't know but am having some bad feelings about his health Dan Allah kiyi sauri kije" Ammi tace cikin roko

"Ok Ammi insha Allah"

"Nagode, maira ki fa yi sauri kije"

"Toh" daganan suka katse wayar
Ajiyar zuciya Ammi ta sauke, tunda ta samu Wanda zai duba Mata lafiyar shi.

Zarah ✨🧕

Kullum sai Samir ya Kira yayi ta damun ta akan ta amince da soyayyar shi, Kuma ta ki duk da tana son ta amince amma tsoro ya ana in ta tuna yanda Sagir yaci amanar ta da yanda khalifa yayita bata wahala a gidan shi, sai taji ta tsani kowani na miji.

Yau ma zaune take a daki tana waya da Aunty Amira tana labarta Mata yanda sukayi da Samir, Dan yau ma yazo har kuka ya Mata da ta amince.

"Zarah if you love him then why not give him a chance,na San kina Jin tsoro kar ki aure shi ya ci amanar ki, but karki Bari zaman da kika yi da ya khalifa da Kuma yanda Sagir ya ci amanar ki, ya cuce ki life is all about taking risk"

"Toh Anty Amira insha Allah i will think about it"

"Ok Allah ya baki zabi na Alheri"

"Amin" sannan suka katse wayar.

✍️✍️✍️✍️✍️

Ya Khalifa!! Umaira ce ke Kiran sunan khalifa tun dazun, tayi salama har ta gaji, sunan sa ma ta Kira ya fi a kiga, har Mai gadi ta tambaya ko ya gan fitowar sa amma yace yau sati daya kenan bai sanya shi a idon shi ba, ga motar shi a harabar gidan da alama yana ciki, daga karshe dai ta Yanke shawarar zuwa dakin sa.

Da salama ta shiga dakin ganin ba kowa yasa ta zauna a bakin gado da tunanin ko Yana cikin toilet, har ta kwashe minti Ashirin zaune Bata gan ya fito ba Kuma Bata ji motsin ruwa ba yasa ta mike ta bude toilet din tagan ba kowa, tafara duba ko Ina a dakin ganin ba kowa yasa ta nufi wurin kofa da niyar barin dakin sai kawai ta gan wani kofa a gefe, da sauri ta nufi kofar ta bude, ganin mutum kwance Yana nishi sama sama yasa ta nufe shi a tsorace, abinda ta gani yasa ta cewa "Innalillahi ya Khalifa"

Vote, Comment, share pls 🙏

See you guys next week 🙈

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now