31

2.3K 264 5
                                    

Juyi juyi yake a gado ya kasa bacci, ji yayi gidan ya masa fadi, me yasa yake ji ajikin sa Kaman abinda ya aikata bai dace bah, lumushe idonsa yayi, fuskarta ne ya fara masa gizo da sauri ya bude su, sai Kuma yaja tsaki..

✨✨✨

Har yanzun kuka zarah take, Ummi tayi rarashin duniya ammpa taki shiru, kuma taki fada musu me ya faru ya sake ta, wani irin ciwo take ji a kasar zuciyar ta, me tayi ta cancanci wannan wulakanci, yanzun ta yarda Maza suna da son Kai, kansu kawai suka sani Kuma Basu da imani da hakuri.

Bayan kwana biyu daga zarah har shi Khalifa ba Wanda ke da walwala cikin su.

"Zarah nagaji da wannan rashin cin abincin da ba kiyi" Ummi ce ke magana cikin fada

"Ummi ban Jin yunwa ne" zarah tace cikin muryar rashin lafiya

"Zarah baki da lafiya ne" Ummi ta tambaya cikin tashin hankali

Kirkiro murmushi Zarah tayi tace "Ummi ba komai fah am okay"

Girgiza Kai ummi tayi tace "Toh sai ki tashi ki ci abinci"

"Toh ummi" tana gama fadin aka ta mike a hankali zata shiga bayi Dan yin fitsari sai ji ummi tayi Abu ya fadi Tim, juyowan da zatayi tagan Zarah a kasa sume.

Zarah!!! Ummi ta Kira Sunanta da karfi, tanufi wurin ta, a rikice Abba da ya Amir suka shigo Dan falo suke suka ji muryar ummi, ganin Zarah akasa a sume ga ummi kusa da ita tana kuka yasa suka nufe su, ya Amir ya dauki zarah Abba da Ummi suka mara mi shi baya..........

Khalifa✨✨✨

"Meya same ta" ya tambaya cikin tashin hankali

"Gaskiya ban sani ba" aka ce daga dayar bangare

"Toh wani asibiti suke"

"Garkuwa specialist hospital kaduna"

Ok yace ya katse wayar key din motar sa ya dauki ya nufi waje mtsw yaja ganin daga shi sai boxers ciki ya koma, brown jalabiya ya dauka ya zura sannan  ya nufi wajen motarsa, ya shiga ya bar gidan da mugun gudu, tuki yake cikin tashin hankali, sanda ya tsaya a wani supermarket ya siya mata abubuwan sannan ya wuce asibitin.

Yana isowa ya faka motar duk da Yana cikin tashin hankali Yana son ya gan yanda jikin ta yake, Hama ya kasa fitowa daga motar da wani irin ido zai kali Abba da Ummi, aka dai yayita tunani daga karshe ya daure ya fito ya nufi ciki, wurin receptionist ya nufa ya tambaye ta, sanda ta duba files din dake gaban ta sannan tace mishi inda suke a hankali ya fara tafiya zuwa dakin jikin sa asanyanye, Yana isowa yagan su zaune a wani kujerar dake a wurin, gaida su Abba yayi cikin kunya Yana sunkuye Kai kasa amsa Masa sukayi fuskar su ba yabo ba fasala, wata nurse ce ta fito daga dakin da Zarah take ta sanar da su ta farfado Hama tana bacci yanzun.

Jin haka Khalifa ya mike da sauri zai shiga dakin sai Kuma ya ja baya, ya tsaya "ka shiga Mana" Abba yace Dan ya lura kunyar su yake ji, dakin ya shiga ya ajiya kayakin da ya kawo a gefe daya sannan ya nufi wurin ta, kujera ya ja ya zauna, ya zuba Mata ido Yana bin fuskarta da kalo, shi dai ya kasa Gane me yasa ya damu da ita haka cikin kankanin lokaci, ji yayi Yana son taba kyakyawar fuskarta, hannu yasa ya fara shafawa a hankali
   

Zarah ❣️

Tana cikin bacci taji wani hannu Mai taushi na shafa Mata fuska cigaba da bacci tayi Jin har yanzun hannu mutum na nan yasa ta bude idonta, ganin Khalifa yasa ta Kara lumshe su ta bude dasauri ta mike ta cire hannun shi daga fuskarta "me kake yi a nan" ta tambaya tana aika Masa kalon tsana, sada Kai kasa khalifa yayi ya kasa cewa komai Dan kalon da take masa kowai yasa yaji mutuwar jiki "nace me kake a nan" tace tana daga murya.

A sanyanye yace"na zo duba lafiyar ki ne"

Wani murmushin ba ka da hankali zarah tayi tace "yaushe ka fara damuwa da lafiya ta, in ce bamu da wani alaka tsakanin mu koh"

Ran shi ya Dan Sosa da maganar ta Hama sai ya dake yace "Dan haka sai akace ba zan iya zuwa duba lafiyar ki ba"

"Ehehe wata sabuwa baka damu da lafiya ta sanda Nike a gidan ka ba sai da ka sake ni"

Cikin bacin rai khalifa yace "Zarah would you just stop this"

"Yaushe na zama zarah in ce sunana ke koh, and for your information da kake zancen in yi shiru baka da damar da zaka yi yanda ka so Dani Kuma, remember am not more your wife" zarah tace tana bude Masa ido ba alamar tsoro a tare da ita

Samun Kan shi yayi Yana cewa "am sorry"

Wani shumin murmushi tayi tace " Why sudden Apologize hmmmn if you know what is good for you don't even waste your time apologizing to me, don't even try because i will never forgive you, all the torture, pain, insult, kuma kira na da kayi da karuwa ban yafe ba"

Ido Khalifa ya kura Mata kaman yana Gane abinda take cewa, Hama Sam bai ji ko daya daga cikin abubuwan da take cewa bah Dan ya tafi duniyar tunani, mamaki yake yanda bai lura da kyaun ta ba sai yau.

Tsawan da Zarah ta daka Masa na ya dawo dashi da ga duniyar tunanin da yake "Baka ji na ne nace ka fitar min a daki"

Gyara zama khalifa yayi kaman bai ji ta ba Yana Kara zuba mata idon sa.

Da karfi zarah tace "get out nace ban son ganin ka"

Khalifa bai San sanda ya furta Mata "Ni Kuma Ina son ganin ki"

Da iya kacin karfin muryarta zarah tace "Ni Kuma na tsane ka, ban son ganin ka, i hate you"

Ganin tana son Tara Masa mutane, Kuma ran shi ya fara bacewa yasa ya fita a dakin da sauri, ya ma su Ummi salama ya bar asibitin.

NOTE: NA SAMU MISTAKE A PAGE 25, GIDAN DA ABI YA GINA MA KHALIFA BA A ABUJA YAKE BA A KADUNA YAKE. SORRY FOR THE MISTAKE.

VOTE
COMMENT
SHARE.

'Ya Mace (Completed)✅Onde histórias criam vida. Descubra agora