16

2.4K 286 15
                                    

Wannan shafin naku ne
HajaraMusaIliasu
aysherahmaddanlami

Thank you for your love and support dearies i really appreciate....

Karar da wayarsa keyi ne ya farkar da shi daga tunanin dayake hannu yasa ya dauki wayar, ganin Abi ke kira yasa yatashi zaune da sauri, sai da ya daidaita nutsuwar shi sannan ya daga wayar "ka same ni a'falo yanzun" abinda yaji Abi yace kenan sannan ya katse wayar, da anzari ya mike ya nufi falon yana tunanin ko me yafaru Abi ke neman sa cikin gaggawa..

Da salama ya shiga cikin ladabi ya rinsina har kasa ya gaida su sannan ya zauna a kasa kusa da Abi hade da cewa "Abi gani"

"Khalifa ya batun aurenka" Abi ya tambaye shi, sosa keya yayi yace "Abi pls ka dan kara min lokaci"

"Khalifa!" Abi ya kira sa ba wasa, "na'am Abi"

"wani matsayi ka dauke ni kuma waye ni a gare ka" Abi yace yana kalon sa.

"Kai mahaifi nane wanda nike alfari dashi" yafada yana kara kalon Abi cikin mamaki me yasa Abi ke masa irin wa yannan tambayoyin.

"Shin zaka so na wulakanta a idon mutane"

"a'a Abi" yace cikin rashin kuzari

"Toh alfarma nike son kamin zaka amince"

Kai ya sada kasa yace "mutukar bai fi karfina ba Kuma bai sabawa ubangiji bah"

"toh Masha Allah na zabar maka matar aure" dago kansa yayi da sauri, magana yake sonyi sai kuma yayi shiru me yasa Abi zai masa aka aure shi da baiyi shirin aure yanzun ba wacece wannan yarinyar da za'a auro masa tana da kyau da diri yanda yake so ko sabanin hakan bai gama tunani ba yaji Ammi tace "ba kowa bace face Zarah" ido ya zaro kaman zasu fado sannan yace "wacce zarah" babu tsamani yaji tace "yar uwar ka mana"

Baki bude yake binsu da kallo hanya sunsan abinda suke cewa, shi suka zabawa karuwa a'matsayin matar auren sa,  jikin sa ne ya fara rawa saboda bacin rai bai san sanda ya furta "Abi wlhi ban sonta kaji na rantse ba zan iya auren karuw.....

bai karasa ba Abi ya kifa mishi mari biyu a jere dafa kunci Khalifa yayi Abinka da farar fata har wurin yayi jajur ga shafin hannun Abi kwance, cikin bakin ciki Abi yace "Khalifa abinda zaka saka min dashi kenan ba komai tunda kunyata ni kake sonyi a idon mutane"

"Abi...." katse sa Abi yayi dasauri cikin daka masa tsawa data tsorotar dashi har Ammi yace "kar na kara Jin sunana a bakin ka" yafada ya fita afalon amugun fusacep juyowa yayi ga Ammi itama mike wa tayi tace "Am very disappointed in you son" sannan tabi bayan Abi.

Khalifa kuwa ji yake kaman ya kurma ihu shima daki ya koma so yake yayi kuka aa hawaye sunki fitowa, ji yake kamar ya mutu why all him of all people yanzun Ammi da Abinsa sunyi fushi dashi mutane da baison ya gan wani ya bata musu rai yau shi da kansa ya bata musu rai duk saboda ya fada gaskiya bai son karuwa dan ita Abi ya mare sa.

Abi da baison komi ya taba lafiyar jikin shi yau ya mare shi saboda wata karuwa shi dai ya san bai taba Zina ba "ya Allah ka kawo min mafita......

VOTE
COMMENT
SHARE.

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now