14

2.4K 305 14
                                    

Wannan shafin naku ne Masoyan ya mace Thank You all for your advices i really really appreciate i just want to tell you guys that I LOVE YOU guys so so much....

*YA MACE**

Sai kalon idanun juna suke hawaye na safa da marwa a fuskar zarah ga kuma kalon mamaki mai hade da tsana datake aikawa Sagir din, sai motsi bakinta suke magana take sonyi hama ta kasa, shi kuma sagir wata bangare a zuciyar sa na gargade shi da ya amince shine ganin yanda zarah ta koma wata kalar abin tausayi cikin kankanin lokaci, yanda wata ke gargadin sa da kar ya amince aii in ya amince mutuncin sa zai zube, ko yace bashi bane ba zasuyi wani bincike kuma bah, tunda cikin yariga ya zube bare suce za suyi DNA test

kallo ya koma kansu ganin yanda suka tsura wa juna ido Abi ne yayi karfin halin cewa 'Sagir" dagowa yayi ya kalli Abi Cikin sanyin murya yace "Na'am Abi" magana Abi ya fara masa ba wasa cikin muryar sa, "Sagir Dan girman Allah ka fada Mana in Kai ne ba abinda za mu yi maka muna dai so mu san waye Mata cikin ne"

Jiki amace Sagir ya sunkuyar dakansa yace "wlhi Abi bani bane"

"toh ranan da abin ya faru da Kai tafita Kuma Kai ka dawo da ita ko ba aka bah"

"akane nina dawo da ita"

"toh shin wani lokaci abin ya faru ba tare da sanin kaba?"

Ido Sagir ya waro yana zufa saboda bai zaci za suyi wayennan tambayoyin bah, sai da yayi kaman minti biyu sannan yace "wlhi Abi ban san wani lokaci abin ya faru ba itama tace muku ran dana dawo da ita dadare na fita da aboki nane toh shi yasa mukayi dare"

Dan numfasawa yayi sannan yacigaba dacewa" ni Kuma damuka dawo wurin dana raka abokina ban ganta a gidan ba nayita neman ta sai karfe takwas da rabi na ganta agurin gate din gidan tana tafiya ahankali tana dingishi shine na tambaye ta tace min bata San wuka na gurin ba ta taka ya yanke Mata kafa"

"Sagir ka dai ji tsoron Allah" zarah tafada cikin kuka mai tsuma xuciya hadi da danasanin karyar da ta shara ma iyayen ta tun farko.

"Sagir abinda muke so da Kai shine ka fada Mana gaskiya Dan darajar iyayenka kaji tsoron Allah da ranar da zaka koma gare sa zamu Kara tambayar ka a karo na uku shin kai ne ko bah Kai bane"

" Bani bane" Sagir ya furta atakaice Dan shi yafara gajiya da wayennan tambayoyin kai kace wasu lawyer.

A'fusace Khalifa ya mike ya shako sa yana "Dan Uwarka in bah Kai bane wa nace wa?? Me yasa Kuma tun ranar tarabu da kai"

Kirma jikin  sagir yafara "wlhi bani bane" yafurta dakyar wata kyakyawar mari Khalifa ya mashi yana kara shako sa yana cewa "bakai kadai bane saurayinta taya abin ya faru ba tare da sanin kaba"

"wlhi ban sani bah"

"Ok har yanzun ba Kai bane Koh"

"eh"

girgiza Kai Khalifa yayi ganin in bai masa aika aika ba, bazai  fadi gaskiya ba, daga kafa khalifa yayi da karfi zai takesa da sauri Abi yace "Khalifa sake shi"

Kamar ba dashi ake magana ba kafa ya kara dagawa sai take shi, "kai ba da Kai ake magana ba" Baba yadaka mishi tsawa Sagir kuwa sai zufa yake yana raraba idanuwarsa da sukayi ja kamar gauta suka wani firfito kamar ka tabasu sufado.

Sake sa yayi da karfi ya hankade sa gefe goshin sa ya buga da tiles yar Kara yasaki, shi Kuma Khalifa ko a jikinshi komawa yayi ya zauna.

Shi kuwa Sagir wuyarsa ya fara shafawa yana tari abinka da farar fata har wuya da fuskarsa sunyi ja ga kuma shafin hannun kalifa kwance da goshinsa da yafara kumburi, wani irin kallo mai wuyar fasarawa cike da tsana zarah take aika masa, shin me yasa baba yace a sake shi, ji take in tana da wuka ne agurin ta soka mai ya mutu kowa ya huta, zuciyar ta zafi yake mata wata irin radadi zuciyar ta ke mata da kunci ganin yanda Sagir ke rantsuwa ba shi bane.

"Sagir, sagir, sagir zu nawa na Kira ka"

"Zau uku ne Baba"

"Toh wannan shine damar da zan baka na karshe in kaine kayi gaggawar fada mana in ba haka ba, wallahi duk ranar da muka tabbatar dacewa kai ne toh sai kayi danasanin kawo ka duniyar da Uwarka tayi" Dan shiru yayi sannan yacigaba da "na gama zaka iya wucewa"

Aii sagir najin aka ya mike dasauri har yana neman faduwa ya fita a falon kamin a halaka shi, bayan fitar sagir nasiya sosai Baba da inna suka ma yara da jikokin su suka Kuma bama Abba hakuri ya yafewa zarah sannan aka rufe taro da aduwa kowa ya nufi gidansa.

*****

Tana kwance a'gado sai rizgar kuka take kamar ranta zai fita tunda suja dawo gida take wannan kukar, ta kasa hada ido da kowa duk kunyarsu take ji musanman yanda ta gan abinda ta aikata ya saka iyayenta kunci,  saboda kaf cikin yaransu sunfi ji da ita komai suka samu sai suce Zarah.

Yanzun kuwa ta kunyatar dasu ta zuba musu kasa a'ido tayi abinda da kyar su yafe Mata bude kofar akayi da sauri ta hadiya kukar da take ta boye kanta a blanket kaman mai bacci, ummi ce ta shigo ganin tana bacci yasa ta zo kusa da ita ta fara shafa kanta hawaye na ambalaya a fuskarta ita dai komi zarah zata yi mata bata taba iya fushi da ita sai dai ta nuna a fili tana fushi amma a zuciyar ta bata iya wa Dan duk cikin yaranta Allah ya hora mata soyayyar zarah duk da Bata nuna ma yaranta babanci.

Sai data share kusan awa daya tana shafa kan zarah sannan tabar dakin, zarah kuma tun dazun tayi bacci jin ummi kusa da ita tana shafa mata kai dan gani take kamar a'mafarki ne, wata irin sanyi taji a zuciyarta har bata san lokacin da bacin ya dauke ta ba.

KHALIFA
Kwance yake a gado yakasa bacci sai juyi juyi yake wai shi me ke damun shine kwanan nan kullum cikin tunaninta yake har mafarki yake da ita sunyi aure harda yara mtsw ya ja tsaki ganin bacci bai dauke Saba yasa ya tashi yaje yayi alwala ya shimfide sallaya ya fara nafila.

Washe gari da safe zaune suke a dinning table suna karyawa sai ga Kira ya shigo wayar Abba dagawa yayi sukayi magana kaman na yan mintina sannan ya kaste wayar ya mike da sauri ya nufi kofa "Alhaji Ina zaka baka fa gama karyawa ba" Ummi tafada cikin kullawa "eh in na dawo na karya baba ne ya kira yana son gani na yanzun"

"toh Allah yakiyaye hanya Amin yafada yafita......."

TOH ANA WATA GA WATA ME YA FARU ???ME YASA BABA KE NEMAN ABBA CIKIN GAGGAWA WACECE KUMA WANNAN YARINYAR DA KALIFAH KE YAWAN MAFARKI DA ITA....

TOH NI DAI GASHI NA MUKU UPDATE KAR A MANTA A BAR MIN SAKON COMMENTS WAYENDA ZASU SANYA NI NISHADI KOH NAYI YAJI 😅😜

VOTE
SHARE
COMMENT
FOLLOW MY ACCOUNT Meenarlee

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now