37

2.3K 246 8
                                    

Washe gari khalifa ya tada rigima shi fa zai koma gida sai an salame su, da kyar likitan ya Basu salama bayan dogon gargadin da ya Masu akan karsu Bari ya shiga damuwa, kuma kar ya cika tunani, ya Kuma sha maganin da abinci akan lokaci.

Bayan sun Kai gida wanka yayi, Ammi ta taya shi ya shirya sannan ta kawo Masa abinci, ya kwanta amma bai yi bacci ba, tunanin zarah yayita yi yanda bai da lafiya Kuma Bata damu zuwa ta duba shi ba, yasan yayi Mata laifi amma aii komin ya, ya kamata ta yafe mi shi, Koh baza ta yafe mi shi bah ya kamata ta zo ta duba lafiyar shi tunda itama ya je ya duba nata lokacin da bata da lafiya.

Can yace "Ammi ya Zarah take"

Murmushi Ammi tayi tace "tana lafiya aii gobe ma za'a yi walimarta"

Aii kusan kwarewa khalifa yayi yace "Ammi me yasa zatayi walima aii tayi lokacin Auren mu koh"

"Eh aii Aure...... Bai Bari Ammi ta karasa bah dan yasan inda ta dosa yace "waye mijinta"

Bai gama mamaki ba sanda Ammi tace "Abokin ka Samir"

Ido khalifa ya ware sannan ya fara tari, Sannu Ammi ta ma shi tana Mika mishi ruwa

Bayan ya sha ruwan ya kwanta, Ammi Kuma tausayin yaronta ne ya kama ta dan kalo daya zaka masa ka hango tsantsar kishi a kwayar idon shi.

Hira Ammi ta fara Jan shi dashi Dan Bata son ya shiga damuwa ko yayi tunani tun Yana Amsa da eh a'a uhmmn har ya sake jiki, sanda Ammi ta tabatar yayi bacci sannan ta bar dakin.

8:30pm

Bayan an gama sallar ishai, sunci Abinci khalifa yaje ya samu Abi da Ammi yace "Abi"

"Na'am khalifa kana bukatar wani abu ne"

"A'a tambaya nake so na maka"

"Toh Allah yasa na sani"

"Uhmmn Abi matar da mijin ta ya sake ta, ba tana bukatar tayi wata uku bah, kamin ta auri wani"

"Eh toh aii Sai tana da idda"

"Toh me yasa za'a daura Auren zarah da Samir Bayan Koh wata bai yi bah Dana sake ta'

Murmushi Abi yayi yace "aii tace Bata da idda"

"Wlhi Abi karya take" khalifa yace Yana daure fuska da alamar gaskiya

Ido Abi da Ammi suka zuba mishi suna karanta Yanayin shi.

Can Abi yace "khalifa ban fa son iskanci kace tana da idda zarah Kuma da bakin ta tace Mana Bata da shi"

"Aii Abi karya ta muku wlhi gaskiya nake fada"

"Uhmmn toh ka wuce zamu tatauna Akan maganar"

"toh" khalifa yace ya bar dakin Yana murmushin cin nasara

Bayan khalifa ya bar daki Ammi tace "Toh ya za'a yi kenan tunda khalifa yace tana da idda Koh za'a daura Auren ne haka"

Ajiyar zuciya Abi ya sauke yace "ki Bari dai zamu tatauna akan maganar gobe"


********

"Khalifa ka tabatar tana da idda ba karya kake ba"

"Eh Baba" khalifa yace da duk alamun gaskiya

Cikin kuka Zarah tace "Baba karya yake ban fa da shi"

"Wlhi Baba karya take tana da shi'

Ido Baba ya kura musu ya rasa bakin magana gashi Kuma lokacin daurin aure na matsowa

Tunda yace kina da Shi ke Kuma kin ce baki dashi yanzun bamu San wake da gaskiya ba Kuma dole baza'a daura Auren Yau ba sai an Kara bincike Akan wannan lamarin.

......... 

"Kuyi hakuri" Abba yafurtq cikin tsananin tashin hankali jin Yan uwan Samir sun ce in ba daura Auren yau ba toh Samir ba zai Aure zarah bah kenan.

"Wlhi in baza'a daura Auren yau bah to kusa ran yusuf  ba zai Auri 'yar ku bah." Yanuwan Samir suka ce cikin baccin rai, tun dama ba son auren suke bah

"Kuyi hakuri wani dan uzuri ne ya same mu amma.......

"Mstw wani irin wulakanci ke ga bazawara ma sai han ja Mana Rai" Wani kawun Samir yace cike da masifa

Ransu Abi ya dan sosu amma sai suka boye, Daddy ne yayi karfin halin cewa "malam aii ba fada muke ba, bamu Kuma ce baza mu baku yar mu bah cewa mukayi a bamu lokaci akwai wani bincike........

Katse shi wani kawun Samir yayi da cewa "me kuke nufi da bincike, aii ya kamata bincike kamin ranan aure za'a yi shi ko"

Wani yayi carab yace "a toh abinda na gani kenan, muda ya kamata muce zamu yi bincike bamu yi ba, yarinya tayi cikin shege kamin aure tazo tayi aure, auren ma ko wata bai Kai ba, yanzun Dan mu dake shirin aurenta dan ya rufa mata asiri fisabilillahi sai han ja mana rai, aiko budurwa ma sai dai a'akan"

Abba zai yi magana Abi ya katse shi cikin fushi yace "Alhamdulillah kun nuna mana halin ku, ba sai kun mana gori ba, yar muce Yusuf ba zai aura ba then it fine, mu kuma baza mu baku yar mu bah dan ba zata auri wahala ba, alhaji  ibrahim ka fi bani kunya da girman ka, amma ba komai mun fasa Auren"

A fusace suka juya suka wuce suna masifa, aii gara da kuka fasa tunda ma wa zai so hada dangi da karuwa.

"toh ya zamu yi kenan, mu sannar da mutane han fasa auren" Abi ya tambaye Abba da Daddy

Ganin yanda mutane suka cika wurin, yasa Abba cewa "Yaya tunda khalifa ya nuna yana sonta kuma sakin da ya mata kuskure ne me zai ana a'daura auren da shi.

Uhmmn kawai Abi yayi ba dan yaso bah dan gani yake khalifa doesn't deserve Zarah.

Aka dai aka sake daura Auren khalifa da Zarah a karo na biyu.

Labari na isowa kunan Samir kuka ya fashewa iyayen shi, Yana sun cuce shi.

Khalifa kuwa kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna, sai washe hakora yake yana ma Abba godia.




TEAM SAMIR KUYI HAKURI NASAN NA BATA MUKU RAI😥🤧

VOTE, SHARE, COMMENT🙏🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍
🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍🤍

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now