11

2.9K 288 21
                                    


"Innalillahi wa inna ilayhi rajiun" shine abinda Bakinsu ya iya furtawa, cikin mamaki likitan ke binsu da kallo ganin yadda duk sun firgice yasa ya Kara cewa "kuyi hakuri nasan..... Katse shi ya Khalifa yayi cikin anzari yana cewa 'Kai kasan abinda kake cewa" kallonsa likitan yayi sannan yace "tabass nasan abinda nake cewa saboda bari tayi, kayi hakuri amatsayin ka namijinta nasan zaka ji ba dadi" yakarasa maganar cikin tausayawa, wani mugun kallo ya Khalifa ya wasta mishi yace "hakalinka daidai kuwa" Abi ne yayi karfin halin dafa kafadar shi yace "calm down son" sai kuma ya juyoga likitan yace "likita Kana nufin wannan yarinyar da muka kawo ce tayi bari anya kun bincika da kyau" Ajiyar zuciya likitan ya sauke yace "eh mun bincika da kyau, ga file dinta nan ku Kara dubawa" ya mika musu file din, karba file din ya Khalifa yayi, ya bude yafara dubawa, dayake shima likitane Kuma  tafanin mata ma'ana gynecologist, abinda ya gani yasa ya Kara zaro idanuwansa domin tabatar abinda ke rubuce a file din gaskiya ne, cikin wata biyu da sati daya ne a rubuce ganin yanda yake wani zazaro idonsa yasa jikin Abba na rawa ya karbi paper din shima ya duba idanuwansa ne suka Fara canza launi zuwa ja ganin abinda ke rubuce kura ma file din ido yayi har bai san lokacin da hawaye suka fara safa da marwa a fuskar sa ba file din ya mikawa ummi itama karba tayi idonta bai sauka koh ina ba sai pregnat with two months one week baby sake file din tayi tasa duka hannun a Kai ta fashe da wani irin kuka mai sauti.

Bakinta na rawa tace "na shiga uku ni halima 'yar adamu jikan shehu, zarah kin cuce ni wannan bakar kaddara har Ina"  ganin yanda take kuka yasa Ammi da Mamie suka fara bata hakuri tayi shiru tadai gan a asibiti suke, ita kuma Ummi ko jinsu batayi sai karfin kukan data kara, fita sukayi a offis din, shi kuma likitan kallo ya bisu dashi can wani tunani ne ya ziyarce shi, koh dai bata da aure ne baki ya tabe ya cigaba da ayukan sa, a waje kuma yaran na ganin yanda iyayen nasu suka fito dukansu jikinsu a'sanyanye ga ummi tana kuka zarah ta cuce ta, Abba kuwa hawaye yake duk da sai k'okarin ganin baiyi kuka ba yake, cikin tsananin tashin hankali suka fara jefo ma iyayensu tambayar me yafaru.
 

Abi ne yazo kusa da Abba ya zaunar dashi akujerar dake gurin, ya fara bubuga masa baya yana cewa "haba Kai kuwa Muhammad meye na kuka sai kace bah jarumi ba kayi hakuri kaji bara naje a bamu transfer zuwa wani asibitin kila basu bincika da kyau ba"  ran Abba a'bace yace "Yaya wani irin basu bincika da kyau bah kaima kasan wannan asibitin is best among all in kaduna and kuma kun gani a rubuce cikin ne da ita"  zaro ido yaransu sukayi Suka furta "CIKI" da karfi.

KALUBALE GARE KU YAN MATA
KARKU BARI SOYAYYA TA CUTAR  DAKU YANDA YA CUTAR DA ZARAH DAN SOYAYYA YANZUN TANA DA BABBAR ILLA BANCE KAR AYI SOYAYYA BAH A'A AMMA DAN ALLAH KUYI MAI TSABTA WANDA BARAKU ZO KUNA DANA SANI DA NADAMA DAGA BAYA BAH

DA SAMARIN YANZUN SUKA YUNKURIN TABA KI KIKA HANA SU SAI SUCE BAKI SONSU YANDA SUKE SONKI KE KUWA UWAR SOYAYYA SAI KI YARDA YAFARA TABE TABE DA LASHE LASHE WATARAN YA ZARCE YA CUTAR DAKE YA RABAKI DA MUTUNCIN KI,KIMAR KI DA KUMA DARAGAR KI

SOYAYYA YASA KIN MANTA DA TARBIYAR DA UWARKI TAYI WAHALA SHEKARA DA SHEKARU TA GINA SAURAYINKI KUMA IN YA SAMU ABINDA YAKE SO YA BARKI WASU SU DIRKA MIKI CIKI SU GUDU SU BARKI DA WAHALA WASU KO BASU GUDU BA SUCE SHARRI KIKA MASU KUMA ZA'A YARDA DASHI TUNDA CIKIN BA'A JIKIN SHI YAKE BA

WASU SU YARDA SU AURE KI  AAMA KINA TUNANIN ZAI BAKI DARAGAR KI YANDA YA KAMATA?? TOH BAZAI BAKI BAH DAN CE MIKI ZAIYI KILA MA ABINDA KIKEYI DASHI SHI KIKE DA WASU MAZAN LOKACIN YA MANTA SHINE YA RABAKI DA BUDURCIN KI.

MASU KARFIN SHA'AWA DAN ALLAH KU DINGA SANNAR DA IYAYENKU KOH DA YAKE WASU IYAYEN NE DA MATSALA YARO KO YARINYA YACE MIKI YANA DA KARFIN SHA'AWA SAI KICE NAWA YAKE DA ZAI SAN KAN ABIN TOH YA MA AJIYE MAGANAR SAI ITA KO SHI YAGA KARSHEN BOKO KANKU KUKE CUTARWA BAKU TUNANIN IN ABIN YA MASU YAWA ZASU BI WATA HANYAR SABAWA ALLAH WAJEN BIYA BUKATUN SU AKWAI WASU IYAYE CIKIN DAYA  KO KUMA DUKA SU BIYUN SUNA DA YAWAN SHA'AWA TOH BAKU TUNANI AKWAI CIKIN YARANKU DA ZASU GADO KU DAN ALLAH ADINGA KULA

SHIYASA CASE DIN FYADE YAYI YAWA WASU IYAYEN KUMA SUNA DA SAKE SAI SU BAR YARINYA YAR SHEKARA BIYAR TANA TALLA KOH KUMA KU KAI YARINYA MAKARANTA KARFE SHIDA LOKACIN BA KOWA A MAKARANTAR SAI MAI GADI KOH MALAMI NA MIJI SAI KU BAR MUSU YARINYA A KULA MAKU DA ITA SAURIN ME KUKE DA BARAKI/KA JIRA KARFE BAKWAI BA KOH ZAKI KAI YARINYA A KULA DA ITA AII YA KAMATA MALAMA MACE KO NANNIES DIN MAKARANTA YA KAMATA KU BAH BAKU TSORON A MUSU FYADE KUN GANI SHIKENAN KUN CUTARDA YARKU TUN TANA KARAMA

MATA MASU TAUYE MA MAZAJEN SU HAKKI DAN ALLAH KU GYARA BAKU TUNANI ZAI NIMI MATAN BANZA KOH YA MA YAR MUTANE FYADE SAI KU DAWO MIJIN KU YA CUCE KU YA JA MUKU ABIN KUNYA TOH KE KIKA CUCE SHI DAN DA KIN ADANA ABINKI BARE JA MIKI ABIN KUNYA BAH

YAWANCIN MAZAJEN YANZUN IN SUKA AURE KI BA BUDURWA BA TOH KOH KIN CE MISHI FYADE HAKA MIKI BARASU YARDA BA DAN SUNA GANIN YANDA MATA KE TALLAR JIKIN SU MA MAZA DAN KUDI CEWA ZAIYI KIN SIYAR DA BUDURCIN KI SHIYASA BAZAWARAI SUKA YI YAWA

AKWAI WAYENSU IYAYE SUNA DA SHI AMA MAKO BASU IYA BAH MA YARAN SU BAKU TUNANI ZAI NIMI DA KANSHI TA WANI HANYA MARA KYAU SHIYASA YAN FASHI DA KARUWAI SUKA YI YAWA KUMA MASU TURA YAYANSU KARUWANCI DAN KUDI DAN ALLAH KU DAINA AKUMA KULA DA FITOWA DA DAWOWAR YARA

YAN MATA DA IYAYE MATA ADINGA KULA

DAFATAN BAN RUBUTA ABINDA ZAI CUTAR DA ALUMMA BA, ALLAH YASA A'AMFANA DA DUK ABINDA NA RUBUTA DUK ABINDA NA RUBUTA BA DAI DAI BA YA ALLAH KA YAFE MIN YA KUMA YAFE WA JAMA'A GA BAKI DAYA ALLAH YASA MU DACE AMIN...

EVERYONE HURT BY MY STATEMENT KUYI HAKURI DAN ALLAH DIDN'T MEAN TO HURT ANY ONE PLS🙏
NAGODE.........

Vote and comment

Meenarlee ❤️

'Ya Mace (Completed)✅Where stories live. Discover now