12

2.7K 291 11
                                    

Cike da mamaki Nazir yace "Abba zarah ce ke da ciki ko kuwa" a'sanyanye Abba ya gyada mishi Kai Wanda yasa ya tabattar dacewa lallai kanwar tashi ce ke da ciki daskarewa sukayi dukansu abu daya kawai ne ke ci musu kwai akwarya shine waye mata cikin? basu gama tunani bah wata nurse ta fito tace musu ta farfado aii ummi bata bari ta karasa bah ta hankade ta gefe tashiga dakin.

zarah dake xaune a'gado irin ta Marasa lafiya bata gama dawowa hayacinta ba, ummi ta nufa batayi wata wata bah ta dauke ta da wasu mahaukacin marin guda biyu masu mugun zafi Wanda yasa zarah kusan faduwa daga gadon, ta sake daga hannunta zata Kara mata taji an rike mata hannu juyowa tayi daniyar ma mutum rashin mutunci sai taga Ammi ce, kai ta sada kasa dan Ammi bah dai kawarjini bah dan ba mamaki nan Khalifa ya gado tasa.

Ammi tace "meye haka haba yarinya bata gama farfadowa ba sai ki hau ta da duka" ummi kuwa sai motsi bakinta yake da alama magana take sonyi amma ta kasa wani kuka mai cin rai ne yaci karfinta zarah kuwa sai ido take binsu dashi ganin wani irin kallon da suke mata mai wuyar fasarawa yasa ta maida kanta kasa ga zafin mari da cikinta dake dan mata ciwo Abba ne yazo ya ja hannun ummi suka fita a dakin kalifah kuwa sai kallon ta yake how can this innocent soul do this uhmmn yayi tuna yanda mata ke ma maza tallar kansu saboda abin duniya baki ya tabe irin i don't care din nan ya fita ya Ahmed kuwa bakin ciki ne yarufe shi ji yake kaman yaje ya mata dukan mutuwa ta bata musu sunna a idon mutane mtsss yayi ya fita a dakin ya nazir yabi bayanshi aka dai kowa yafita a dakin ya rage Amira da taje ta rungume zarah tana kuka dan shi can't just believe it zarah ce da ciki har tayi bari ooh Allah ta furta a hankali zarah Kuma bata san abinda ke faruwa bah dan har yanzu hankalin ta bai gama dawowa daidai bah.

kwana biyu Zarah tayi a asibiti Wanda cikin wannan kwana biyun ya zame mata abinda bazata taba mantawa ba, duk tsawon rayuwarta tun ranar da ummi suka kawota aka tabattar da bari tayi basu Kara dawowa bah, sai Ammi da Amira da suke kula daita Kuma har yau ta kasa gane laifin me ta musu suke mata haka amma ta kuduri aranta sai ta tambaye su mai yasa suke mata haka bata gama tunani ba Anty fadila ta shigo, cikin Fara zarah ta gaida ita kamar wace aka tilasta ta ansa ciki ciki sannan ta Sami wuri tazauna tana wani daure fuska, cikin rashin kuzari zarah tace "Wai Anty DanAllah meya faru ina su ummi"  hararanta Anty Fadila tayi tace "wato baki ma San abinda kika aikata ba ko? sanda kika gama yawon banza da iskancin ki kice me ya faru" Dan Jim Zarah tayi kamin tace "anty ban fa fahimce abinda kika nufi ba"

Wani kalon raini Anty Fadila ta aika mata sannan taja tsaki "mtsw toh abinda nike cewa shine ciki ne dake kika yi bari" zaro idanuwanta Zarah tayi kaman zasu Fado kasa tace "ciki... bari" Nan da nan jikin ta ya dau rawa ta saki wani kuka mara sauti, suna cikin haka Ammi ta shigo tana cewa 'kuyi sauri mana ba nace Miki an Sallame mu ba" a'hankali ta tashi tasa hijjabin da aka ajiye mata agefen gadon ta nufi waje, tafiya take kaman wacce kwai ta fashewa ajiki fuskar ta dauke da hawaye kana ganinta zaka san tana cikin tarin bakin ciki da damuwar da yakasa boyuwa a fuskar ta abin dai sai ta baka tausayi, ahaka ta isa wurin mota Ammi ma ta zo suka shiga gidan Abi suka nufa dan Abba yace karsu ma kuskura su dawo da ita gidan sa dan ba abinda zai ana shi tsine mata

Kwance take a dakin sai ruzgar kuka take tun dasuka dawo daga asibiti taki cin komai tun suna rokan ta taci har suka gaji suka kyale ta duniya ta mata zafi ita bata ma ganin laifin sagir laifin ta take gani saboda da bata yarda ya fara taba ta bah bare yunkurin rabata da budurcinta ba har ya gaiga mata ciki yanzun da wani irin ido zata kali ummi da Abba ta San da kyar su yafe mata aka tayita tunani har bacci yayi awo gaba daita.

Washe gari tana gama sallah addua ta fara Allah ya yafe mata dan ta tafka babban kuskure da yayi sanadiyar jefa ta cikin wannan mumunan hali kofar dakin aka bude Ammi ce tashigo tare da plate din abinci, da sauri ta shafa adduar ta durkusa har kasa ta gaida ita dan yanzun kunyar matar ta keji sosai, cikin fara Ammi ta amsa tare dace mata tayi sauri ta shirya dan zasu gida Baba Kai kawai ta gyada dan tasan wannan zuwan akan tane a haka ummi ta ajiya mata abincin ta fita da sauri ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa da hijabi taci abincin dake plate din kadan ta rufe  ta fito falon cike da kunya tace "Abi ina kwana" murmushi Abi yayi yace "lfy amarya an tashi lfy" kaita ta sada kasa dan bazata iya amsawa bah a haka suka fito suka shiga mota ya Khalifa da Abba a gaba sai zarah da Ammi a baya.

Suna isowa gidan horn ya kalifah ya danna Wanda yasa gaban Zara yayi mumunan faduwa, jikin ta yafara rawa,ammi dake kalonta tun dazun tace "yata kwantar da hankalinki kinji" kirkiro murmushi Zarah tayi tace "toh" kalifah kuwa wani mugun kallo ya aika mata ta gefen ido yana tabe baki.

bude masu gate mai gadi yayi suka shiga, a'hankali suka fito daga mota suka nufi babbar falon gaisawa sukayi da kowa sannan suka zauna, Zarah Kuma kasa gaida kowa tayi Dan wani irin nauyinsu take ji, bayan minti biyar koina ya nutsu kowa yayi shiru, bude taron akayi da addua suka hada da godewa Allah da yakawo su wanan ranar sannan Baba yayi gyaran murya Wanda yasa dukansu maida hankalansu gare shi, "Zarah" ya Kirata  muryar Zarah na rawa kamar ta fashe da kuka tace "na'am" ajiyar xuciya Baba ya sauke yace "Zarah DanAllah karki ji tsoro ki Gaya Mana wa yamaki ciki?" Ido Zarah tazaro takasa magana bakinta sai rawa yake hawaye duk sun wanke mata fuska yainda kowa yayi tsit suka zuba mata ido jiran ta Kira sunnan Wanda ya mata ciki.

muryar tana rawa ta fara labarta musu komai daga farko har karshe.

ZASU YARDA DAITA SAGIR NE YA MATA CIKI ??

IDAN SUKA KIRA SAGIR SUKA TAMBAYESHI, SHI YA MATA CIKI ZAI AMINCE SHI NE KO ZAI KI??

KARKU MANTA DA👇
                               VOTE
                           COMMENT
                               SHARE
                               Follow

'Ya Mace (Completed)✅Opowieści tętniące życiem. Odkryj je teraz