35

2.3K 244 12
                                    

"Ya Khalifa" takara Kira Sunan shi a kidime, ganin kaman numfashin sa dake sama sama ma dazun ya dauke, yasa ta kurma wani ihu, hannunta na rawa ta ciro wayarta daga jaka ta danawa Ammi Kira ringing daya Ammi ta dauka.

Bata ma amsa salamar Ammi ba cikin kuka tace "Ammi ya Khalifa baya numfashi"

Aii kusan sume wa Ammi tayi tace "maira kin san me kike cewa Kuwa"

"Wlhi Ammi baya numfashi"

"Innalillahi wa ina illahi rajiun" Ammi tace wayarta ya fadi a kasa da sauri ta fito daga dakin ta nufi dakin Abi dan sanar da shi.

💠💠💠💠💠

Sai safa da marwa suke a kofar dakin da khalifa yake sun fi awa biyu da kawowar shi amma har yanzun likitocin basu fito ba, Ammi da Umaira Kuma kuka suke, Abi ma kallo daya zaka masa kasan akwai damuwa atare dashi.

Sun kwashe minti talatin a haka, ba wanda yama dan uwansa magana, zuciyar kowa cike da tunani kala kala,can wani likita ya fito, da sauri suka nufe shi suna tambayar sa ya jikin shi yake "kubi ni offis" yace da  toh suka ansa suka mara mishi baya.

Zaune suke a offis din sun zuba ma likitan ido suna jiran ya fada musu wani hali tilon dan su yake ciki, gyara murya likitan yayi yace "ku ne iyayen sa"

"Eh" suka amsa da sauri dan sun kagu ya sanar dasu me ya same shi.

Fada sosai likitan ya rufe su dashi Akan me zai sa su Bari damuwa ta mishi yawa, kuma sun San zuciyar sa bai da karfi Yana da rauni tunda aka haife shi, in this young age ya kuma samu highblood pressure har Yana gab da illata mishi rayuwa gashi Kuma Baya cin abinci Yana gama musu fada yace "gaskiya rayuwar yaron ku Yana cikin babbar hatsari ba za mu iya ce muku zai rayu ba, because his condition is very critical and his chance of survival is low"

Cikin kuka Ammi tace "yanzun ba abinda za'a iya"

"Am sorry ba abinda zamu iya ku dai taya shi da addua"

Cikin sanyin ciki suka mike, suka fita a offiis din, suna fitowa Ammi tafara sabon kuka ta juyo ga Abi tace "ka gan abinda ka jawo Mana Koh, wlhi Alhaji ka cuce ni yanzun yarona yana gab da mutuwa"

"Wa zai mutu" Inna da isowar su wurin kenan tace dan taji Ammi na cewa "Yana gab da mutuwa"

Da sauri Ammi da Abi suka juyo suka Gaida ita, har yanzun Kuma Ammi na kuka

"Baku fah Amsa tambayata bah"

"Inna Khalifa.......

Aii Inna Bata Bari Abi ya Kara sa ba ta doka salati tace "innalillahi wa ina illahi rajiun, khalifa ne akace zai mutu"

"A'a Inna ba cewa akayi zai mutu ba kawai dai jikin shi yayi tsanani ne"

"Toh Allah ya bashi lafiya"

"Amin"

Zarah 💠💠💠
Soyayya sosai Zarah da Samir suke amma Mai tsabta yanda adinin muslunci ya kiyatar, har an kawo lefe saboda Samir yace Yana son a yi komai cikin gaggawa, da aka tambaye Zarah tana da idda Kuma tace musu a'a tunda ba abinda ya taba shiga tsakanin ta da Khalifa.

********


Bayan kwana biyu, jiya likitocin suka sa ran zai farfado amma har yau shiru har sun fara shiga damuwa.

Yanzun ma likitoci sun kai biyar a dakin, sai dube dube suke a jikin sa, suna so su tabbatar ko coma ya shiga.

A waje Kuma masu kuka nayi masu bada hakuri nayi, Abi kuwa idon sa yayi ja kaman hawaye zasu zubo, zuciyar shi cike da tarin nadama, Dan ya manta lokacin da aka haife khalifa likitan yace musu karsu bari damuwa ta mishi yawa dan zuciyar shi mai rauni ne.

Surprise🙈💃💃

Vote
Comment
Share

'Ya Mace (Completed)✅Onde as histórias ganham vida. Descobre agora