HAYATUL ƘADRI! PAGE 1-2

879 51 2
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 1-2

https://chat.whatsapp.com/EykycDYZDn64yObhFIA7WC

Da sunan ALLAH mai rahama mai jin ƙai; tsira da aminci su ƙara tabbata ga shugabanmu Annabi MUHAMMAD (S A W) da alayensa da sahabbansa.

"Rayuwa kowa da irin tasa, labari kowa da irin nasa, haka nan k'addara da jarrabawa sukan sauya rayuwar Bawa daga asalin yadda take, zuwa wani fanni na daban...Anti Hassana na karanta litattafan da ba su da adadi, na yi nink'aya cikin rayuwar mutane da dama domin na samu ilimi akan tawa rayuwar, sai dai hakan bai sa na hango wata halitta da tayi irin rayuwata da na yi wa lak'abi da HAYATUL K'ADRI ba. Akwai buk'atar jama'a su karanci rayuwa ta zahiri irin tawa, shi yasa na zab'e ki cikin dubban marubuta na sakar miki ragamar bayyanawa duniya LABARINA."

Bayan sallama, wannan sak'on na ci karo da shi a lokacin da na bud'e wayata don riskar sak'onnin da ke jira na, zuciyata ta zurfafa wajen tunani da kai komon ma'anar da sak'on ya k'unsa; kafin na kammala nazari na ji shigowar kira cikin wayata. Na yi jim ina kallon bak'uwar lambar da ke kan fuskar wayar, ba ni daga cikin mutanen da ke share d'aga kiran bak'uwar lamba don wani dalili nasu; amma duk da hakan sai na samu shakkun d'agawa ban san dalili ba, tana dab da katsewa nayi namijin k'ok'arin ture shakkuna gefe na danna wurin amsa wa tare da kanga wayar a kunnena.
Tun kafin na ce komai wata kamilalliyar murya ta ratsa kunnuwana a yayinda ta rangad'a sallama, ta zarce da yiwa kalaman da za ta furta togaciya ta hanyar tausasa murya da fad'in,
"A yi mini afuwa, ban nemi izinin kira ba, Allah ya sa ban shiga cikin uzurorinki na yau da kullum ba Anti Hassana."
Na saki murmushi duk da ban wanye da mai maganar ba, na ce "Na saba da hakan a mabambanta lokuta, don haka kar hakan ya dame ki, sai dai ban gane mai magana ba."
"Ayya!... ta furta hakan, sannan ta d'ora da ce wa,
"Rahama suna na, ni ce na aika miki da gajeren sak'o ta akwatin sirrinki na (Watsapp), ina neman amincewarki bisa sakar miki ragamar bayyanawa duniya labarina."
"Na'am, ina sauraronki Rahama." Na ambata tare da mayar da wayar gefen kunnena na hagu.
Ta sauke numfashi "Na karanta GARKUWA BIYU (Labarin Ya Hamza da Hidaya) na ga irin sharud'an da Hidaya ta cika kafin ki amincewa rubuta labarinta, ni ma a shirye nake domin cika wad'annan sharud'an, har ma da k'arin wasu idan akwai, domin ki rubuta labarin rayuwata ta zahiri don fad'akar da tarin al'umma kamar yadda ki ka fad'akar a labarin Hidaya."
Na yi murmushi na ce "Madalla! Idan haka ya tabbata ina maraba da ke Rahama, amma wani hanzari ba gudu ba, labarin GARKUWA BIYU ba gaske ba ne, na yi amfani da salon ne kawai don ankarar da masu son na rubuta labarinsu cewar sai sun cika wasu k'a'idoji kafin na amincewa k'udurinsu, gudun samuwar wata matsala a gaba."
Ina jiyo sautin murmushinta, cikin taushin murya ta ce "Madalla! Amma kina nufin labarin ke ki ka k'irk'ire shi kenan har ki ka rubuta?"
"Kin yi tambaya, kuma kin ba wa kan ki amsa." Na mayar mata da amsa ina murmushi.
Ta sauke numfashi "Kina da tarin baiwar da ke kan ki ba ki santa ba Anti Hassana." Ta furta mini kalaman yabo.
Na ce"Ba ni kad'ai ba, duk wani marubuci yana da wannan baiwar, ya rage gare shi ya yi amfani da ita ta kyakkyawar hanya ko akasinta."
Ta ce "Tabbas haka ne Anti Hassana, ina jinjinawa tarin baiwarku wajen sarrafa alk'alumanku domin gina labarai masu tsayawa a zukatan masu karatu, kamar yadda na fad'a miki labarina na daban ne da ban tab'a cin karo da irinsa ba, shi yasa nake so ya shiga jerin labaran da jama'a da yawa za su karanta, k'ila ni ce ban sani ba ko akwai wad'anda za su tsinci wani ilimi a cikin labarin, ko kuma ya yi kamanceceniya da rayuwarsu, daga nan za su yiwa kansu alk'alanci."
Na sauke ajiyar zuciya na ce "Madalla da ke Rahama! Zan duba yiwuwar hakan, zan miki magana da zarar na kammala wani nazari."
Cikin murnar da ta bayyana a muryarta ta ce, "Na gode Anti Hassana."

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now