HAYATUL ƘADRI! page 75-76

120 15 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 75-76

*HASSANA ƊANLARABAWA FANS, DA HAYATUL ƘADRI FANS 1, JIYA TATTAUNAWARKU TA YI MINI SUKARIN DAƊI TABBAS, 'YAN ƁANGAREN AHMAD DA 'YAN ƁANGAREN MUSTAFA A CIGABA DA KAFTAWA, INA TARE DA KU JAMA'ATA, SHAFIN YAU GABAƊAYA NA SADAUKAR MUKU DA SHI KU GIDIDDIBA KU RABA SHI A TSAKANINKU.*

"Yau dai ALLAH ya bayyana mana Ahmad, ya dawo gida." Abin da hasashena ya hasaso za ta faɗa mini kenan, amma kuma buɗar bakinta sai akasin hakan ne ya fito.

"Ƙaiƙayi koma kan masheƙiya, na zo miki da labari a kan sharrin da su Hajiya suke aiko miki tuni ya fara koma musu kansu, daman kin san shi sharri ɗan aike ne, duk daɗewa zai komawa wanda ya aiko shi."

Har lokacin idanuwana suna kanta, kuma ɗoki da zakwaɗina tuni sun ƙaru wajen son jin abin da ya faru da su Hajiyar, ina shirin magana sai Umman Fati ta riga ni cigaba da magana.

"Aka ce duk abin da ka yi sai an maka, tabbas na yarda da hakan, domin kuwa ashe bayan Ahmad ya yi miki saki uku a bisa ƙulle-ƙullensu Hajiya, sati biyu da hakan ita ma aka sako mata ɗaya daga cikin 'ya'yanta saki uku rigis! Da yara guda goma cif! Ya ɗebo su a mota ya zo ya zubewa Hajiyar su ya ce bai yarda da 'ya'yan ba kamar yadda bai yarda da matar ba."

Na ƙwalalo idanuwa ina sauraron Umman Fati ina jin batun tamkar almara, tayi murmushi ta riƙo yatsun hannuna ta ce.

"Wannan masifar da ta fara tunkaro Hajiya ita ce musababbin da ta haifar mata da matsanancin hawan jini da wasu irin cututtuka marasa kai da gindi, ta fara girbar abin da ta shuka tun a duniya kafin a je lahira wajen bajeta a faifai. A yanzu haka maganar da nake miki Hajiya dai hawan jini ya zamar da ita summun!  Bukumun! Umuyun! Domin ta ragargaje, ba ta tafiya ta zama gurguwa, ba ta gani ta zama makauniya, haka nan ba ta ji ta zama kurma, a yanzu haka masifu sun fara bainaye duniyarta, bamu san kuma abin da zai faru da ita a gaba ba kafin ta koma ga ALLAH ya tuhumeta kan abubuwan da ta shuka a bayan ƙasa, domin har yanzu da nake ba ki wannan labarin na masifun da suka afka mata matar nan bata tuba ba, bata ajiye makaman shu'umancinta ba, saboda wanda ya yi nisa ba ya jin kira..."

"Ina Atika?" Tambayar da ta zo bakina kenan bayan Umman Fati ta dire a kan bayanin Hajiya. Umman Fati ta kama kai tana girgizawa fuskarta ɗauke da wani irin yanayi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce mini.

"Atika lamarinta mai girma ne, domin bayan barinki wannan gari idan zan faɗa miki abubuwan da ta aikata zuwa yanzu za mu kwana muna yi bamu gama ba, ga shi ke na ganki cikin hidima, kuma ni ma ina sauri ne na koma saboda na bar wasu abubuwa, amma in sha ALLAH idan na samu sukuni zan zo na warware miki lamarin Atika da abubuwan da suka sarƙafe tata duniyar a halin yanzu."

Ban so hirarmu ta tsaya nan ba. Haka mukai sallama da Umman Fati ta tafi, jikina a sanyaye ina godiya ga Allah da ya fara saka mini kan zalinci da tozarcin da waɗannan mutane suka yi mini.

*******

A kwanakin duk jikina a sanyaye, ga kuma haushin Mustafa da ya cika raina, ya rasa ina zai tsoma ransa saboda naƙi sauraren shi, ga shi yana son magana da ni kuma idan ya kira ni sai naƙi ɗagawa. Kawai sai ya samu dabara ya kirawo wayar Ramlat, ina kwance kawai sai ganinta na yi ta shigo ta maƙalamun waya a kunne, na ɗago ina kallon ta da alamun tambaya, sai ta gyaɗa mini kai alamar na riƙe wayar, ina riƙewa ita kuma ta sakar mini tayi saurin ficewa daga ɗakin ta barni da waya a kunne.
Saukar ajiyar zuciyar da ya yi can ƙasan maƙoshi da yadda ya ambaci sunan da ya raɗa mini su suka tabbatar mini shi ne, sai a lokacin na tabbatar lallai na zama shagwaɓaɓɓiya, na zama alallaɓa auren zamani, domin a take kawai sai na fashe masa da wani irin kuka irin mai shessheƙar nan, ya tsaya shiru yana saurarena sai sakin ajiyar zuciya yake yi, sai can ya saki wani numfashi ya yi magana cikin sigar kyautatawa da wata irin murya da ta saukar mini da kasala.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now