HAYATUL ƘADRI! page 55-56

103 19 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 55-56

SADAUKARWA:
*NA SADAUKAR DA WANNAN SHAFI GA 'YAN UWANA 'YAN ƘUNGIYATA TA EXQUISITE WRITERS FORUM, MARUBUTA MASU CIKE DA FASAHA DA HAZAƘA, ALLAH YA HAƊA KANMU YA BA MU LAFIYA DA ZAMA LAFIYA*

*KU YI HAƘURI SHAFIN YAU BA SHI DA YAWA, NA ƘOƘARTA NA YI MUKU NE MA DON KAR KU JI SHIRU, NA SAN KUMA JIRANA KUKE YI*

Na ji ya fashe da wani irin azababben kuka tare da mirginawa gefe yana buga kansa jikin allon gadon cike da tashin hankali da rawar jiki. Na zabura a gigice na dawo duniyarmu daga duniyar da na afka, jiki na rawa na miƙe na matsa kusa da shi ina riƙo kafaɗun shi hankalina a matuƙar tashe, ya bar buga kansa da yake yi, sai dai bai fasa kuka ba a lokacin da ya waiwayo gare ni, duk da duhun da ya mamaye ɗakin bai hana ni ganin ƙyallin hawayen da ke saraftu a kan fuskar shi ba.
Tuni ni ma na fara kukan, saboda masifar tashin hankalin da na samu kaina, jin shessheƙar kukana ya saka shi juyowa gabaɗaya ya kama ni ya rungume ni da ƙarfi kamar zai mayar da ni cikin ƙirjin shi.
"Mami wane irin masifu ne suke bibiyar rayuwarmu? Wane irin ƙalubale ne ya cika duniyarmu, zuwa yanzu na fara tunanin an ya za mu dawwama cikin jin daɗin rayuwa Mami? Daga wannan sai wancan! Wace irin jarabta ce wannan?" Sambatun da yake yi kenan cikin kuka da sartun hawaye yana ƙanƙame da ni, na kasa cewa komai domin ni kaina abin ya fara girmama tunanina, ban za ci a yadda muke rawar jikin raɓar juna zai kasa aikata komai ba, domin na kai minzalin da babu abin da nake buƙata sai kasancewa da shi, ni kaɗai na san yanayin da nake jin jikina kawai.
Ya yi baya ya faɗi kwance kan gado, yana riƙe da ni a tsakiyar ƙinjin shi, a haka ya cigaba da magana cikin rauni da saddaƙarwa.
"Wallahi Mami ba don kar na tafi na barku a filin duniya ke da Muhibba babu ni ba, da na roƙi ALLAH ya ɗauki raina na huta da wannan gararin rayuwa mai cike da ƙalubale...
Hannu na miƙa na rufe masa bakin shi, ilahirin jikina na rawa, haka na riƙa matsawa har na samu bakina ya kai dab da kunnen shi, ina wata irin shessheƙar kuka na raɗa masa kalmar.
"Ka yi haƙuri!"
Ya waiwayo ya mirgina ni ƙasa shi ya koma samana, ya kife fuskar shi kan tawa, hawayen shi na fitowa suna sauka kan nawa idanuwan suna gangarawa gefen fuskata, muna shaƙar numfashin juna.
"Ni ne ya kamata na ba ki haƙuri Mamina! Domin na sani ina cutar da ke, babu wani abu da za ki ɗorar na jin daɗi tunda kika aure ni, amma a hakan kike so na, kike ɓoyewa kowa laifina, kike nunawa duniya mijinki ya fi na kowa. Mami a tarihin rayuwata ban riski tarihin wata mace a zamanin nan da tayi biyayyar aure kamar ki ba, ke ɗin ƙarshe ce! Ke ɗin maƙura ce! Mami ina tausayin ki, idan ba na tare da ke tunanin ki kaɗai yakan saka ni zubar da hawaye, ba don komai ba sai tsananin tausayi da ƙaunar ki da suka yi mini yawa a zuciyata, sai dai a yanzu son ba shi da amfani, ƙaunar ba ta da alfanu, tunda ta kai gargarar da na fara kasa biya miki buƙatar aure, bayan ci da sha da kayan more rayuwa da nakan kasa samar miki, ina kunyar ki Mami, wallahi ina tsananin jin kunyar halin da na jefa rayuwar ki...

Zuwa lokacin tuni jikin shi ya ɗauki zafi saboda zazzaɓin da ya rufe shi, Ahmad ya kasa kwantar da hankalin shi balle ni ma na samu nawa hankalin ya kwanta, sai kuka kawai yake yi da sakin sambatu, na yi iya ƙoƙarina wurin nuna masa ya mayar da komai ba komai ba, amma ya kasa ganewa, shi dai burin shi kawai ya biya mini buƙata wanda kuma hakan ba zai yiwu ba, ba zai iya komai ba.
"Mami a yadda jikin ki ya nuna kin gama kaiwa maƙura, zan miki 'yan dabaru domin ki fitar da abin da ke damun ki kin ji."
Ni kuma na ƙi amincewa, ba na fatan na samu jin daɗin da shi ba zai samu ba, shi ya sa na riƙe shi sosai na ce.
"Buƙatata tana biya ne a lokacin da farincikina ya samu biyan buƙata, kaine farincikin Rahama, ba ka samu biyan buƙata ba, ta yaya ni zan samu?"
Ya sake rungume ni ya ce.
"A'a Mami, za ki cutu idan  na bar ki a haka."
"Ba zan cutu ba, kar ka damu." Na mayar masa da amsa ina sake ƙanƙame shi.
A haka muka cigaba da kwanciya, zuciyoyinmu a birkice, ban san abin da ke cikin ta shi zuciyar ba, tunda 'zuciyar mutum birninsa' Ni dai tawa kam abubuwan da suka cika ta suna da yawa, ba na son ɗora zargi ko zato a kan wannan matsalar, saboda zato zunubi ne ko da ya kasance gaskiya, sai dai ina ji a raina tabbas akwai lauje cikin naɗi.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now