HAYATUL ƘADRI! page 21-22

103 15 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 21-22

Sosai kukansa ya rik'a tab'a mini zuciya na rik'a sharar hawaye ni ma, ya fi k'arfin minti goma yana kuka ina jin sa ban ce masa kanzil ba, har dai ko gajiya ya yi da kukan sai na ji ya fara sassautawa yana ta sakin ajiyar zuciya, daga nan kuma ya murje idanuwansa ya waiwayeni a hankali da idanuwa jajur.
"Don Allah kiyi hak'uri ki yafe mini kinji Mami." Ya ambata da rawar murya kamar ya kuma fashe wa da kuka.
Sai lokacin na iya furta abin da ke zuciyata.
"Me yasa ka yi mini k'arya bayan na yarda da kai?"
Ya girgiza kai tare da runtse idanuwa yana dafe kai.
"Na rantse da Allah ban miki k'arya ba Mami, kuma ba na fatan na yi miki har abada."
Na fara yi masa wani kallo na kar ka raina mini hankali, k'walla ta ciko idanuwansa ya share, ya kuma matsowa dab da ni ya ce.
"Ki yarda da ni, ki amince da ni, zan iya rantse miki kuma na dafa Al'k'ur'ani a kan cewa duk abin da na fad'a miki a baya gaskiya ne, kuma duk abin da ya faru a yanzu ba da sanina ba ne, sai bayan komai ya cab'e na san komai, kawai ba ni da yadda zan yi ne, akwai abin da ya yi mini katanga daga d'aukar mataki a kan abin da ya faru."
Na saki ajiyar zuciya na kalle shi, muk'a tsurawa juna ido yana ta marairaice mini fuska, na hana zuciyata tausaya masa na fara k'alubalantar sa.
"Kana ji ko! Da ni da kai aure za mu yi wanda nake fatan ya d'ore har abada, mu zama mutu ka raba takalmin kaza, kana ganin tun yanzu idan muna b'oye wa juna abubuwa tafiyar za ta yi kyau kuwa? Kayi nazari a kan maganata, ni yanzu abin da nake so na sani shi ne, me ya kawo sauyi a komai."
Ya sauke nannuyar ajiyar zuciya, har lokacin idanuwansa na kaina, sai da ya yi k'asa da kai sannan ya fara magana cikin sigar rauni.
"Mami ni ban san me zan ce miki ba a yanzu, an riga an cutar da ni ne, duk abubuwan nan da suka faru kar ki dubi komai, abu d'aya za ki duba, ki kalle ni a matsayin maraya wanda ba shi da uwar da za ta tsaya masa a kan komai nasa, mai uba talaka wanda ba shi da muryar da zai fad'a domin a ji, me y'an uwan da basu isa komai ba, wanda ba ya tak'ama da komai sai Ubangiji, kuma Ubangijin nake fatan ya isar mini ga duk wanda ya zalunce ni."
Maganarsa ta ratsa ilahirin jikina, duk da ban fahimci karatun kurman da yake mini ba, amma wasu maganganun nasa na d'ora su a sikeli na tantancewa. Bayan ya d'ago ya kalle ni idanuwa cike da hawaye ya cigaba da cewa.
"Ni dai fatana kar ki guje ni, kar ki juya mini baya, ke nake kallo na ji dad'i Mami, duk wani abu da zai faru da ni da na tuna ina da ke a duniyata damuwata ma fi tsoka takan zaftare, don Allah ki yarda da ni Mami, kiyi hak'uri muyi aurenmu komai zai dai-daita, na yi miki alk'awarin ba ki kulawa fiye da tsammaninki, zan miki komai, zan gatantaki, zan zama garkuwarki, ina son ki Mami, don Allah don manzon Allah (S A W) kar kiyi fushi da ni."
Sai na rasa yadda zan yi da shi, saboda yadda ya kalallameni ya rik'a min magiya da rok'ona Allah Annabi, ni na san Ahmad yana masifar so na da k'aunata, ni ma ina masa k'aunar da zan iya zama da shi a duk inda Allah ya nufi zamana ni da shi.
Kalaman da ya rik'a karanta mini suka gusar da haushinsa da nake ji a raina, na ba shi tabbaci a kan shikenan komai ya wuce tunda har ya rantse da Allah a kan ba k'arya ya yi mini ba. Sosai ya ji dad'i ya rik'a godiya yana kwaso mini sambatu.
"In sha Allahu sai kin yi alfahari da aurena Mami, ni ba butulu ba ne, zan nuna miki halacci a bisa zab'a ta da kika yi cikin dubban maza."

***********

Haka aka ci gaba da shagalin bikina babu wani armashi saboda kowa jikinsa ya yi sanyi, da yawa daga cikin dangina auren ya fice musu a ka, amma iyayena sun ci gaba da ba ni k'warin gwiwa ne, musamman da na biya musu karatun da Ahmad d'in ya biya mini, nan take Abbana ya ce da ni.
"Wallahi Rahamatullahi ban hango k'arya ko munafurci ga wannan bawan Allah ba, duk yadda aka yi dai akwai wani abu da ya faru, kuma na san ko a nan gaba za ki san shi, ke dai ki ci gaba da kyautata masa zato, Allah ya tabbatar da alheri kan aurenku ya ba ku zaman lafiya."
K'warin guiwar da Abbana ya ba ni kenan. Har na ji kaso mai tsoka na damuwar da nake ciki ya yaye.
Duk wani kud'i da ango ke ba wa amarya domin tayi gyaran jiki da kitso da k'unshi ni dai Ahmad bai ba ni ba, haka nan kud'in da zan yi walimar bikin da k'awayena, Sa'adatu da ta zo daga Kano ta tarar da abin da yake faruwa tamkar ta rusa ihu, ta rik'a jaraba da masifar wannan wane irin aure ne zan yi, komai a tsiyace, haka k'awata Asiya ma ta rik'a masifa a kan Ahmad ya ba ta mamaki, bata tab'a tunanin haka zai mini ya wulak'anta aurena ba.
Ni dai duk jin su nake, ina ta addu'ar Allah ya cigaba da ba ni hak'uri kuma ya sanya alheri a auren, domin na tattara na bar masa komai shi ne ya san dai-dai.
Iyayena ne suka mini komai, hatta suturar da zan saka a bikin su ne suka d'inka mini tunda na lefen ba kaya ne masu kyau ba, Mama ta saya mini sark'a da duk wasu kaya na ado na gani na fad'a, haka nan ta tanadi duk wasu abubuwa da ta san zan rabawa k'awayena, ta biya kud'in gyaran jiki da lalle da gyaran gashi, aka yi mini komai ba tare da sisin Ahmad ba wanda ban san dalilinsa na k'in bayarwa ba.
Sosai mahaifiyata tayi namijin k'ok'ari a bikin nan ta yadda ta kulle k'ofofin da mutane da yawa basu san abin da ke faruwa ba.
Abbana ya tanadi kayan gara mai matuk'ar yawa, wanda maganganu suka yi yawa a kan ba za a kai kayan garar ba saboda su ma dangin ango babu wata tsiya da suka yi, ko irin kud'in nan na kamu ba a kawo ba, Abbana ya ce.
"Ba za a yi haka ba, ni don Allah na yi ba don wani abu nasu ba."

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now