HAYATUL ƘADRI! page 3-4

240 32 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 3-4

https://chat.whatsapp.com/EykycDYZDn64yObhFIA7WC

Muna dab da fita tsakar gidan muka yi kacib'us da Goggo Halima k'anwar mahaifina da kuma d'iyarta Sa'adatu da ta kasance kusan tsarata wajen haihuwa, duk da ta girme mini da kad'an,kuma tana da girman jiki don ta zarta ni sosai. Na yi farinciki sosai da ganin  Sa'adatu a wannan lokaci, farincikin da ya ninku a raina a lokacin da na ji albishir d'in ce wa Sa'adatun ta dawo gidanmu da zama, ma'ana za mu ci gaba da zama tare,  kowa ya shaida tsananin murnar da na samu kaina a lokacin, wanda murnar da Sa'adatun ta yi ta ninka tawa sau ba adadi,  saboda matuk'ar k'aunar da take yi mini.
Makarantar da nake zuwa mai suna 'Usman bin affan li tahfizul Qur'an Primary & Junior Secondary school Had'ejia' nan Abba ya saka Sa'adatu muka ci gaba da karatu a tare, ajinmu d'aya, komai namu d'aya tamkar y'an biyu da ni da ita, mun yi kamanceceniya a wasu d'abi'unmu, yayin da muka yi hannun riga game da wasu, ina da matuk'ar hak'uri, yayin da Sa'adatu ta kasance mara d'aukar raini , yadda nake da k'ok'ari haka take da k'ok'ari, sai dai na fita mayar da hankali a karatu, saboda wani zubin nakan b'uya na yi karatu na iya sosai, yayin da zan barta tayi ta surutun ta da wasanni, sai mun je makaranta ta ga na iya, a nan ne takan yi fushi da ni har ma tak'i kula ni, sai na yi bambaki da rarrashi sannan takan hak'ura mu jone.
Yarintarmu zuwa fara girmanmu ta zama abar sha'awa ga sauran jama'a, bamu tab'a wayar gari duhu ya riskemu ba ba tare da wani d'an Adam wala mace wala namiji sun saka mana albarka ba, mun sha fitowa daga gida za mu tafi makaranta koda kuwa mun makara idan muka ga wani ko wata suna buk'atar taimako mukan tsaya mu taimaka, ko tsofaffi ko yara muka ga ni za su tsallaka titi sun kasa mukan tsaya mu tsallakar da su koda kuwa za mu tarar da bulala a makaranta. Na sha hak'ura da cin abincin break d'ina ko kud'in makaranta na ba wa almajirai ko wanda na fuskanci talaka ne, mun yi tarayya a wad'annan kyawawan halayen ni da Sa'adatu, shi ya sa ma ba ni da wata k'awa ko aminiya da ta kai ta.

Ko a makaranta da nake samun yawan tsangwama daga y'an uwana d'alibai dalilin k'wazon da nake da shi da kuma fifikon da na samu a gun malamai. Sa'adatu ce tsanin da ta zame mini garkuwa wajen kare ni daga harinsu, da gasken gaske na sha fama da hassadar d'alibai, domin ba zan manta ba akwai watarana muna (JS 2), malamai za su shiga mitin sai malamin ajinmu ya shigo ya ba mu umarnin kowacce ta d'auki littafinta ta duba tayi karatu saboda za su shiga mitin na gaggawa da malamai  don haka ba sa son surutu da hayaniya, Malam Umar yana fita ashe ba su ji gargad'insa ba nan da nan suka kaure da hayaniya, har zan musu magana Sa'adatu ta ce "K'yale su Rahama, ai su ba kurame ba ne sun ji abinda Malam ya ce, duk wanda bai ji bari ba kuma zai ji wowo." Daga nan ta tashi ta tafi band'akin makaranta domin tayi fitsari, ni kuma na ja littafina na jingina da taga ina karatu, duk sun cika mini kunne da surutu amma ba damar magana sai su hayayyak'o mini.
Dukkanmu bamu san lokacin da Malam Umar ya zo kan tagar ajin ya tsaya ba, ya gama k'are mana kallo tas sannan ya koma ya d'auko bulala mai baki biyu ya shigo ajin, dukkan d'aliban cikin ajin babu wadda bai yiwa bulala goma cif ba, masu kuka na yi, masu jan ido na yi, ni kad'ai ya tsame bai doka ba saboda ya ce ni mai bin doka da girmama maganar malamai ce, sai Sa'adatu da yana cikin dukan ta shigo ajin, hakan ya sa ya ce ita ma ta koma gefe babu ita a dukan tunda bai ganta cikin masu surutu ba, ashe su rashin dukana da Malam Umar bai yi ba shi ya fi bak'anta musu rai, nan take suka k'ulla aniyar idan aka tashi daga makaranta sai sun had'u sun mini dukan tsiya.
Ban san hawa ba, ban san sauka ba, ji na yi kawai an shak'o ni ta cikin hijabina ta baya, a lokacin da muke gab da fita daga cikin makaranta bayan an tashi, gayyarsu guda d'irma-d'irma da su a kan ficiciya da ni, sai da Sa'adatu tayi musu kaca-kaca, dayake suna matuk'ar jin tsoronta, ta nuna su da yatsa cikin matuk'ar fushi ta ce musu.

HAYATUL ƘADRI!Où les histoires vivent. Découvrez maintenant