HAYATUL ƘADRI! page 9-10

137 15 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 9-10

https://chat.whatsapp.com/JqZ3K5n1VZL6wvbC98Myfd

Matashiyar budurwar da na tarar a d'akin da aka kaini. Ta sakar mini murmushi ta mik'o mini hannunta ta ce "Mu k'ara gaisawa ko y'ar uwa?" ni ma sai ban juyawa muradinta baya ba na zaro hannuwana daga cikin burmemen hijabina na mik'a mata, muka yi musabaha fuskokinmu d'auke da fara'a.
Ta bi d'ima-d'iman y'ammatan da ke tik'ar rawa da kallo, wad'anda suka had'a da musulmi da kirista, sannan ta saki murmushi ta waiwayo ta sake dubana.
"Ashe kina nan kina shan kallon rawa, tunda kika ajiye kayanki kika fito ban sake jin d'uriyarki ba."
Na yi murmushi na gyara zama na yi magana cikin sanyin murya,
"Ina nan ina kallon ikon Allah. Sai ka ce wurin party ba makaranta ba."
Ita ma ta yi murmushi "Rayuwar y'anci kenan! Wadda ta bambanta da rayuwar firamare da sakandare, mu ma farkon zuwa haka muka kasance cikin mamaki, sai da muka fara sabawa sai komai ya bi jikinmu, muka gane ce wa kowane muhalli akwai irin rayuwar da ake gudanarwa."
Na gyad'a kai na ce "Tabbas haka ne, shi yasa kowa yake yin yadda ya ga dama kenan?"
Ta ce "K'warai kuwa! Am...Ban tambayi sunanki ba, ya ya sunan malamar?"
Na yi murmushi "Kin sab'a lamba, wannan d'aliba ce ba malama ba, sunana Rahama Ahmad Mai Salati, kuma na zo makarantar nan ne don na karanta Arabic medium; ke fa?" na k'arasa da tambayarta.

Ta yi k'aramar dariya ta ce "Ahaf! Ashe dai ban sab'a lambar ba, duk wanda ki ka ga yana karanta Arabic ai malami ne....
Muka kwashe da dariya, ta cigaba da ce wa,
"Ni kuma sunana Saudat Tahir, tare da y'ar uwata nake wato Kadija Tahir, kuma mune mak'otanki a d'akin da za ki zauna a wannan makaranta."
Sosai na ji dad'i, har na bayyana shi ta hanyar sakin murmushi da magantuwa.
"Ayya! Amma na ji matuk'ar dad'i. Allah ya ba mu lafiya da zama lafiya da juna."

Ta amsa mini da "Ameen ya Allah." Muka ci gaba da d'an tab'a hira muna kallon d'alibai da ke ta watayawa. Har y'ar uwarta Kadija Tahir ta fito ta iske mu inda muke zaune, muka ci gaba da hirarmu.

***********

Rayuwar makaranta akwai wuya sannan akwai dad'i. Wata irin rayuwa ce da idan baka mayar da hankali ba tuni sai ka shiririce ka zo a banza ka tafi a wofi, na d'an samu tangard'a kafin na fahimci komai, musamman wajen gane hall d'in da zan d'auki lecture, ya d'an ba ni wahala, wani zubin sai na fita lecture tun safe na je na kama guri a gaba, sai malami ya zo zai fara karatu sai naga ai ba ma nan ne gurin da zan d'auki nawa karatun ba. Haka zan fita nayi ta bulayin neman hall d'in da y'an Arabic za su zauna. Kuma dayake makarantar babbar kwaleji ce tana da yawan d'alibai, a garuruwan da ke cikin Najeriya kusan ko ina akwai d'alibai da suka zo karatu a cikinta, tun daga kan Musulmai zuwa kiristoci. Haka nan akwai y'ay'an masu kud'i da y'an siyasa, wanda lokacin ma ba wayoyi ne a hannunsu ba computers ne, ni a lokacin ma da k'aramar waya Nokia na tafi, domin ita aka ba ni a gida saboda jin halin da nake ciki a makaranta.
Daga baya da na gane komai tare da taimakon Saudat sai ga shi komai ya dai-daita na fahimci komai.

Ban san abinda ya sa duk inda na samu kaina sai kambun d'aukaka ya hau kaina ba, ban jima da zuwa wannan makaranta ba sai sunana ya fara fita, ni ba ni da rawar kan da za a sanni, amma k'ok'arina da jajircewata kan karatu da kula da addinina da shigar mutunci sai ya janyo mini k'ima da mutunci a wajen sauran y'an uwana d'alibai har ma da lakcarorinmu.
Ya zuwa wannan lokaci kuma shak'uwata da Saudat da Kadija tamkar wad'anda suka fito ciki d'aya, komai namu ya zama d'aya duk da ba fanni d'aya muke karanta ba, su y'an boko ne, y'ay'an gidan mutunci da tarbiyya, shi yasa ma lokaci d'aya abotarmu ta yi girma, don ba a jima ba da mahaifiyarsu ta zo suka gabatar da ni a gareta, ta nuna mini soyayya k'warai da gaske, tare da godiya a kan yadda na shige gaba wajen koya wa yaranta abubuwan da suka shafi addini. Sai da ta kai hatta abincinmu sai da ya zama d'aya, duk wadda ba ta da lecture ita za ta zauna tayi mana girki, haka nan duk lokacin da ba mu da lecture gabad'aya nakan zauna na koyar da su karatun addini ko na koya musu karatun Al'Qur'ani mai girma, cikin lokaci k'alilan da wasu d'alibai suka ankara da kyawawan manufofina, sai ga shi suna barin shashanci suna zuwa wajena domin d'aukar karatu.
Duk da bambancin halayya ta wanni fannin na iya zama da su, domin  Saudt y'ar ak'idar boko ce duk da (Hausa islamic) take karanta. iIta kuma Kadija miskila ce ta gaske don ko magana bata dameta ba, tana karanta (Biology& geography)

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now