HAYATUL ƘADRI! page 33-34

110 14 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 33-34

*AISHA ALIYU GARKUWA, INA MIƘA SAƘON TA'AZIYYATA ZUWA GARE KI NA RASUWAR MAHAIFIYA, ALLAH YA JADDADA MATA RAHAMA YA GAFARTA MATA, ALLAG YA BADA HAƘURIN RASHI*

*ƘAWATA FATIMA(UMMU AƊFAL) KE MA INA MIƘA SAƘON TA'AZIYYATA GARE KI NA RASUWAR MIJINKI, ALLAH YA JIƘANSA DA GAFARA, ALLAH YA BA KI HAƘURIN JURE WANNAN BABBAN RASHI*

"Wannan ƙuduri naki yana da kyau Rahama, sai dai akwai buƙatar kiyi ta-ka-tsan-tsan wurin yadda za ki tafiyar da al'amuran koyarwar. Mutanen gidan nan da kike gani iya musu sai ALLAH, ina roƙon ALLAH subhanahu wa ta'ala ya yi miki jagoranci a kan lamarin."
Sosai na ji daɗin addu'ar da ta yi, tare da ƙwarin guiwar da ta ba ni, na yi mata godiya ina ji a zuciyata zan jajirce wurin ganin na kawo sauyi a rayuwar mutanen gidan in sha ALLAH.
Alhamdulillah! Na fara jan ra'ayin matan gidan a kan karatun da nake so na riƙa koya musu, sai ga shi cikin ikon ALLAH makaranta ta kafu sosai har ma wasu daga cikin maƙota suna shigowa domin su ɗauki karatun su ma, wurin zamansu da suka mayar dandalin gulma nan muka mayar ya koma dandalin karatu, mukan shimfiɗa tabarma duk a zazzauna, dayake lokacin ina da wasu 'yan kuɗaɗe da na samu lokacin da na je gida sai na sa a ka zo aka kafa mana allon bango wanda zan riƙa yi musu rubutu a jiki domin su fi fahimta, muka fara karatu tiryan-tiryan, wasu daga ciki suna fahimta, yayin da wasu suka saka wasa ba sa mayar da hankali, saboda duk suna ganin sun girme ni ni ce ƙarama a cikinsu babu wani hukunci da na isa na ɗauka a kansu, a haka dai ban yi fushi ba muka ci gaba da karatun domin yana ɗauke mini kewar rashin mijina a kusa da ni.
Kusan watanmu biyu da farawa makaranta ta haɓaka, ɗalibai manyan mata sukan kusa cika tsakar gidan duk da girmansa, hakan ya ƙara mini ƙwarin guiwa sosai, tunda fari sai da na fara koyar da su yadda ake tsarkin bawali da gayaɗi, zuwa alwala da yadda ake gudanar da ita, sannan muka gangaro kan sallah da karatun fatiha da na sura, ba ƙaramin ƙaruwa suka yi ba saboda babu abin da suka iya sai shirme. A lokacin ne kuma muka shiga watan Ramadana, ba mu daina karatun ba sai ma ƙaimi da muka ɗora, kuma a lokacin ne idan zan musu karatu nakan shigo musu da wa'azi cikin karatun, ko a kan tsoron ALLAH, ko a kan imani, ko a kan muhimmancin addu'a, ko riƙe gaskiya da gujewa ƙarya.
A kan hakan ne watarana na shigo musu da wa'azi kan batun bin bokaye da 'yantsibbu, saboda yawancinsu akwai masu aikata hakan, sai na shigo da batun ta sigar wa'azi ta yadda masu aikatawa za su ankara su tuba su daina.
Dukkaninsu suna zaune kan tabarma suna saurarena ne, ni kuma ina zaune kan kujera ina fuskantarsu a lokacin da nake karanta musu.

' Yana daga cikin abin da aka jarrabi mutane da yawa da shi a yau, maza da mata, manya da ƙanana, sai wanda ALLAH ya kuɓutar da su, wato zuwa wurin matsafa da bokaye da 'yanduba da 'yan tsibbu, don neman taimako a wurinsu ko don sanin abin da zai zo nan gaba, su kuwa waɗannan bokaye da 'yantsibbu, sai su riƙa yin ƙarya ga mutane, suna cin dukiyoyinsu a banza, kuma suna kare su daga bin tafarkin ALLAH. Duk mai bin bokaye da matsafa kamar ya yi shirka ne, domin ya haɗa wanin ALLAH da ALLAH. Manzon ALLAH(S A W) ya ce:
"Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa." Sai aka ce, "Waɗanne ne ya Ma'aikin ALLAH?" Sai ya ce, "Haɗa ALLAH da wani da tsafi, da kisan kan da ALLAH ya haramta, sai da gaskiya, da cin dukiyar maraya, da cin riba, da tserewa daga fagen yaƙi, da yin ƙazafi ga tsararrun mata."
Kuma manzon ALLAH(S A W) ya yi bara'a daga wanda ga yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi bokanci, ko aka yi masa bokanci, kamar yadda Imran ibn Husain ya rawaito. Ya ce, "Wanda ya yi camfi, ko aka yi masa camfi, ko ya yi tsafi, ko aka yi masa tsafi, ko ya yi bokanci, ko aka yi masa bokanci, duk ba sa tare da mu; duk wanda ya je wurin boka, ya gasgata shi da abin da yake faɗa, haƙiƙa ya kafirta daga abin da aka saukarwa Muhammad." (Bazzar ya rawaito shi, da salsala ingantacciya).
Hukuncin mai tsafi da ɗantsibbu , shi ne a fille musu kai da takobi, kamar yadda wasu daga cikin sahabban Manzon ALLAH(S A W) suka yi.
Ku sani, illar da waɗannan fasiƙai, bokaye da 'yantsibbu suke yi a cikin al'umma, tana da yawa. Daga ciki akwai abubuwa kamar haka:
Na farko, zare imani ga waɗanda suke zuwa wurinsu, waɗanda suke gasgata su cikin abin da suka faɗa.
Na biyu, yawaita kisa da yaɗa shi a cikin al'umma. Duk abin da muke gani ko muke ji na ɓatan wane ko wance, ko ganin ƙaburbura a tone, ko ganin sassan jikin ɗan Adam ana sayar da su, duk aikin matsafa ne da bokaye, waɗanda suke umartar mabiyansu da aikatawa.
Na uku, yaɗa neman mata da fajirci a tsakanin mutane. Sau da yawa  oka yakan sadu da mace, kafin ya yi mata aikin da ta zo nema, ta sanadiyyar hakan ya lalatawa mijinta ita, kuma ga buɗe mata ƙofar ɓarna da yaɗa fasadi a bayan ƙasa.
Na huɗu, cin dukiyar mutane a banza, saboda duk wani abu da boka zai karɓa a maimakon aikinsa ɓarna ne. Abdullahi inb Mas'ud ya rawaito cewa, Manzon ALLAH(S A W) ya haramta kuɗin kare da sadakin karuwa da ladan boka. (Bukhari ya fitar da shi).
Na biyar, ɓatar da mutane, da ɗora su a kan tafarkin fasiƙanci ta hanyar hana su bautar ALLAH: Wasu a hana su Sallah, ko gabaɗaya, ko wani yanki nata; wasu wankan janaba; wasu a hana su alheri, a umarce su da duk wani munkiri.
Na shida, suna jawo azabar ALLAH da fushinsa ga al'umma. Zainab bint Jahsh, ALLAH ya yarda da ita, ta ce, "Ya Ma'aikin ALLAH! Yanzu za a halakar da mu, a cikinmu akwai mutanen ƙwarai?" Ya ce, "Idan datti ya yi yawa!" (Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi).
Na bakwai, asarar duniya da lahira. ALLAH ya ce,

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now