HAYATUL ƘADRI! page 23-24

115 14 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 23-24

TALLA! TALLA!! TALLA!!!

*BAK'AR MASARAUTA*

*Hausawa kan ce 'Ana bikin duniya ake na k'iyama, lokacin da wani yake kuka, wani dariya yake, kamar misalin yadda Uwa ke d'aukan ciki ta raine shi da wahalhalu kala-kala, tayi burin ta haife cikin domin ba wa jariri ko jaririyar duk wata kulawa da za su samar da tagomashin tarbiyya da kyawawan d'abi'u ga abin da ta haifa, ku hasaso yadda wannan uwa bayan duk ta gama wad'annan wahalhalun za ta tsinci kanta a bak'in yanayin da za a raba ta da abin da ta haifa ta hanyar zalunci, a yayin da ko cibi ba a yanke masa ba, shin da me za ku kwatanta?*

*Tana da k'arfin ikon da kwarjininta kad'ai kan girgiza jama'ar da take mulka har su kasa nutsa idanuwansu cikin nata, shi kad'ai ya yi zarrar da yake ji ya isa jera kafad'a da ita, shin me ya taka ne duk da kasancewar sa bawa?*
*Mata na rububin kasancewa da shi duk da bak'ak'en d'abi'un da suka yi wa rayuwarsa k'awanya, izza da guguwar mulki ta taka muhimmiyar rawa wurin kasancewarsa haka*
*Da shi take kwana da shi take tashi! Tamkar Sallar farilla haka mafarkinsa ya zame mata wajibi a duk daren duniya, ta yi namijin k'ok'ari wurin gano shi amma sai dai kash....*

*SABON SALO NE MAI GIRGIZA ZUKATAN MASU KARATU, DUK A CIKIN LABARIN BAK'AR MASARAUTA, ZA A FARA SAKIN FREE FAGES A RANAR 1st OCTOBER 2021 IN SHA ALLAH. GA DUK MAI BUK'ATA YA TUNTUB'I MARUBUCI UMAR FARUQ A WANNAN NUMBER 08038135929 DOMIN KU MALLAKI NAKU A KAN 300 KACAL👌 KAR KU BARI A YI BABU KU🥰*

Ban san duniyar da na tafi ba a lokacin da Ahmad ke yin yadda ya ga dama da ni, mun d'auki tsawon lokaci cikin yanayin da babu abin da ke tashi a d'akin sai saukar numfashinmu da ajiyar zuciyarmu, da bakinsa ya rik'a bautawa fuskata wurin d'auke hawayen da ke kwaranya daga idanuwana, a cikin mamayar da ya yi mini kuma sai ga ni saman cinyoyinsa babu ko da mayafi a jikina.
Tunda na tashi a rayuwata ban tab'a riskar kaina cikin wata fitinanniyar kunya ba kamar lokacin, jikina mazari ya rik'a yi tamkar wadda zazzab'i zai kama, ko y'an uwana maza da suka kasance muharramaina ban saba had'a jiki da su ba dalilin tarbiyyar da ta ratsa jikinmu, amma yau ga ni a jikin babban mutum yana yin yadda ya ga dama da ni.
Duk yadda na so na zame k'i ya yi, yana rik'e da ni yana wani irin cusa kansa cikin wuyana da ya d'auki d'umi, danshin da na ji a wuyana ya tabbatar mini da hawayensa ne ke zuba, duk yadda na so na zame jikina ban samu dama ba, rik'e yake da ni k'am yana sake nutsa kansa cikin jikina, da k'yar ya iya fizgo magana cikin shesshek'a.
"Mamina d'an tsaya mana, daure ki bar ni na samu nutsuwa."
Tsaf na lafe a tsakiyar k'irjin shi saboda na san k'arfina ba zai k'wace ni a lokacin ba, mun fi minti biyar a haka yana ta ajiyar zuciya har ya samu nutsuwa ya d'ago ni daga jikinsa a hankali ya tallabi kumatuna ya rik'e, ya tsura mini idanuwa a yayin da na runtse nawa idon domin ba zan iya kallonsa ba, jikina babu inda ba ya rawa, hucin maganarsa na ji kawai a kan fuskata.
"Ina ma za ki iya bud'e idanuwa ki kalleni, domin  a cikinsu ne za ki hangi zallar farincikin da nake ciki a yau, tabbas duniyata tayi haske, rayuwata za ta cigaba da kyau tunda ta samu tagomashi da ke." Irin wad'annan kalaman ya rik'a furta mini da suka sake k'arar da ragowar kuzarin da nake da shi.
Duk yadda ya so na saki jikina kasa wa na yi, domin a lokacin zuciyar da ke d'amfare a k'irjina cikin matuk'ar k'unci take,  kuka na rik'a yi sosai na rabuwa da dangina da iyayena, duk wani rarrashi wanda ya san zai faranta raina sai da ya yi mini shi, da jikinsa da kuma bakinsa, a haka da k'yar ya samu na yi shiru yana ta lallab'a ni kamar k'wai.
Ya shigo da kaza irin wadda a al'ada ango kan shigowa da amarya a daren farko, kuma ni ma na bi ayarin amaren da ba sa cin wannan kazar, domin ni ba ni da nutsuwar cin komai a wannan lokacin, duk yadda ya yi domin na ci ban ci ba, da ya takura mini ma kuka na sake fashe masa da shi tilas ya hak'ura jiki na rawa ya hau aikin rarrashi.
Muka gabatar da sallah raka'a biyu ta ma'aurata kamar yadda Annabi (S A W) ya koyar da mu, ya kama kaina ya yi mini addu'a.
Ina takure a bango har ya kammala komai ya je ya rufe kewayenmu ya dawo, ya umarce ni da na je na kwanta a gadon, shi ya rik'e mini hannuwa ya raka ni na kwanta, bai ma takura mini kan na cire kayan jikina na sauya ba saboda kar na tsorata da shi, bayan na kwanta na cure wuri guda shi kuma ya fice ban san ina ya yi ba, ina daga kwancen hawaye ya sake b'alle mini har na rik'a jik'a filon da nake kwance a kai. Ya d'auki tsawon lokaci kafin ya dawo d'akin, ina jin takunsa na yi hanzarin runtse idanuwana ina sakin ajiyar zuciya, ya hawo gadon ya kwanta dab da ni, kunnuwana na jiyo mini muryarsa yana karanta addu'o'in tsari da na bacci, ya tofa ya shafe mini jikina da nasa, sai da wata mak'alalliyar ajiyar zuciya ta kufce mini lokacin da yake shafa mini addu'ar a ilahirin jikina, sai kuma ya kwanta ya ja bargo ya lullub'e mu, ya matso sosai ya rungumeni tare da cusa kaina tsakiyar k'irjinsa, k'irjina ban da dukan tara-tara babu abin da yake yi, sosai na runtse idanuwana saboda a matuk'ar tsorace nake.
"Mamina! Kin yi bacci ne?" Ya tambaye ni.
Babu amsa na yi gum! Ina jin yadda yake ta wasu abubuwa da sassan jikina tsawon lokaci, kukan da na fashe da shi ya ba shi damar dakatawa yana sauke ajiyar zuciya.
"Shikenan kiyi shiru, kiyi baccinki kawai kinji Mami."
Ya ambata cikin shak'ak'k'iyar murya, tare da sake nutsa ni cikin jikinsa, na jima idanuwana biyu har na fara jin saukar numfashinsa alamun ya samu bacci, da k'yar ni ma na samu baccin ya kwashe ni.
Da Asuba shi ne ya tayar da ni muka yi sallah, saboda ya makara sosai har an idar da sallah a masallaci, tare muka zauna muka yi karatun Al'k'ur'ani tare da azkar har gari y fara haske, muka kammala sai ya ce mini yana zuwa, ya tashi ya fita.
Can na jiyo kusur-kusur d'insa a tsakar gida, na tashi na lek'a ta tagar d'akin sai na hango shi yana ta kici-kicin had'a risho yana gyara lagwani, ina ta kallonsa har ya kammala ya d'auka ya shiga cikin ktcheen d'ina da ke kewayen, da dawo na zauna ina sakin ajiyar zuciya.
Can ya dawo ya iske ni zaune, ya k'araso yana murmushi ya kamo hannuna.
"Mami na dafa miki ruwa, ki zo kiyi wanka."
Haka ya tasa ni gaba ya raka ni har band'aki, da yaga shigewata shi kuma ya koma ktcheen.
Kafin na fito har ya dafa shayi, ya turara kazar jiya,  shi ma ya shiga wankan inda na sake a d'akin ganin baya nan na shirya sosai.
Ya yaba da adona sosai da ya fito ya tarar da ni ina walwali sai k'amshi nake, kusan sai da ya shanye janbakin da na saka tsaf kafin ya gyara mini kwalliyar da na b'ata, ya ja ni falo domin mu karya kumallo.
Ban wani sake na ci abincin sosai ba kasancewar har lokacin ina d'ar-d'ar, amma da hilata da tarairaya sai da Ahmad ya tabbatar na k'oshi sannan ya rabu da ni.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now