HAYATUL ƘADRI! page 27-28

137 16 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 27-28

Na d'aga kai a zabure ina kallon mai shigowa falon, saboda sallamar ta zo mini a bazata, na yi k'ok'ari wurin sakin fuskata sosai na mik'e ina nuna mata wurin zama, ita ma fuskarta da walwala sosai, ta zauna tana duba na, na yi mata sannu da zuwa sannan na wuce zuwa ktcheen na d'ebo mata ruwa cikin kofin jug na kawo na ajiye a gabanta. Ta dube ni cikin fara'a sosai ta ce.
"Rahama ni fa ba bak'uwa ba ce, don na zo wurinki ba sai kin kawo mini ruwa ba, du-du-du taku nawa zan yi daga kewayena zuwa naki kewayen?"
Na yi murmushi ina wasa da yatsun hannuna, kaina a sunkuye ina durk'ushe na amsa mata.
"Umman Fati ai bak'onka annabinka, don na karramaki da ruwan sha ba wani abu ba ne duk da muna zaune muhalli d'aya."
Tayi dariya "Haka ne kuma Rahama, zancenki gaskiya ne."
Na yi murmushi na gaishe ta, ta amsa mini cike da kulawa, sannan na koma kujera na zauna. Ta d'auki ruwan ta sha sannan ta ajiye ta dube ni tana murmushi.
"To na sha ruwa, don kar Rahama ta ga rashin kyautawa ta ko?"
Na rufe idanu ina y'ar dariya, ina matuk'ar ganin girman matar saboda kusan kaf gidan ita ta fita zakka a hangena, mace ce mai karamci da mutunci, ina tausaya mata saboda yadda take da marayun yara kuma ita ce komai na su.
Ta d'an yi gyaran murya tana kallona.
"Rahama na zo ne na yi miki godiya kan hidimar da kike yi wa su Fati, ba kya gajiya kullum idan kika girka abinci sai kin ba su, duk da cewar mijinki ba ya nan, na gode sosai Allah ya saka miki da alheri, Allah ya ci gaba da kare ku daga sharrin mak'iya da ke da mijinki."
Na kalleta na girgiza kai na ce "Haba dai Umman Fati mene ne abin godiya? Ai su Fati tamkar k'anne na d'auke su, koma na ce miki kamar y'ay'ana tunda ke mahaifiyarsu yaya ce ga mijina."
Ta sauke numfashi ta ce.
"Haka ne, sai dai kuma ba kowa ne zai gane hakan ba, ba kowa ke da irin zuciyarki ba Rahama, ai gasu nan ina zaune da mutanen gidan wad'anda suka kasance y'an uwa a gare ni na jini, kinga suna  kwatanta abin da ke kike mini?"
Na jijjiga kai saboda maganarta gaskiya ce, muka d'an yi shiru wucewar mintina biyu, sannan ta k'ara duba na ta ce.
"Kin san alak'ata da Ahmad kuwa?" Ta tambayeni.
Na girgiza kai na dube ta.
"A'a! Zan dai iya ce wa ke yayarsa ce, ban sani ba dai ko kun had'a mahaifi da mahaifiya ne."
Tayi murmushi ta girgiza kai ta ce.
"Ahmad kenan, yana da zurfin ciki da k'arancin magana, na san za a rina, domin na san ko yadda bikin nan ya wakana da abubuwan da suka kasance bai miki bayani ba ko?"
Na gyara zama na ce.
"K'warai kuwa bai ce mini komai ba, ban san komai ba, abubuwa da yawa ban sani ba a kansa, ban kuma san dalilinsa na b'oye mini lamuran ba."
Fuskarta ta sauya cike da jimami ta ce.
"Kiyi hak'uri Rahama, Ahmad ba shi da laifi a kan abubuwan da suka faru, an fi k'arfinsa ne har aka zalunce shi, shi kuma dayake yana da matuk'ar hak'uri da kawar da kai a lamura da dama, kuma yana amfani da wasiyyar da mahaifiyarsa ta ba shi a kan ya yi wa Hajiya biyayya tamkar ita ta haife shi.
"Wace ce Hajiya?" Tambayar da ta sub'uce daga bakina kenan, wadda na jima ina son jin amsar, domin Ahmad a dunk'ule ya ba ni a lokacin da na tambaye shi.
Umman Fati ta ce "Hajiya yayar marigayiya ce mahaifiyarsu Ahmad, uwarsu d'aya ubansu d'aya, kuma Hajiya ita ce mahaifiyar Atika, wadda ta zo ta d'ibar miki kayan gara ta ce miki za a raba wa dangin miji alhali k'arya take yi ita ce ta tafi da su."
Gabana ya yanke ya fad'i, domin a take na hango Hajiya da Yaya Atika sune masu son toshe numfashin aurena. Umman Fati tayi ajiyar zuciya ta ci gaba da magana.
"Mahaifiyar Ahmad y'ar asalin wani gari ce mai suna Kafin Hausa, mahaifita mashahurin mai arzik'i ne attajiri sosai saboda yana noma da kiwo, kuma yana da filaye da gidaje, a lokacin da ya rasu y'ay'a biyu kacal ya bari, wato Hajiya ita ce babba, sai kuma mahaifiyar Ahmad, ya bar musu gado mai d'umbun yawa da ya kasance a wurin Hajiyar saboda ita ce babba, mahaifiyar Ahmad sun yi aure da mahaifinsa inda a haihuwar farko suka haifi y'a mace mai suna Suwaiba, na san kin san ta ita ce wadda take d'aya daga cikin kewayen da ke gidan nan tana zaman jinya domin lalurar aljanun da take fama da su ta baro gidan mijinta, daga ita kuma sai Ahmad, sannan Maryam, ita ma tana gidan aure yanzu haka, sai kuma Auwal wanda a haihuwarsa ne ta had'u da lalura, bayan shekara da haihuwarsa ta rik'a wata irin cuta wadda har tiyata aka yi mata, aka d'akko wata irin ajiya da aka yi mata a k'irjinta, wasu irin allurai da layoyi da gashi, wanda har zuwa yanzu an rasa wanda ya yi mata asirin, bayan kwana biyu da yi mata aikin ne ta rasu a asibitin (Malam Aminu Kano) da ke garin Kano, kafin kuma ta rasu sai da ta kama hannun Ahmad ta yi masa wata magana, a lokacin yana d'an shekara takwas ne kacal, amma da yake yaro ne mai basira ya rik'e abin da ta ce masa 'Ahmad ka rik'e y'an uwanka da amana, ka zauna lafiya da su ka kula da su sosai, duk da ba kaine babba ba amma kusan girman ya hau kanka saboda kaine namiji. Sannan ga yayata nan wato Hajiya, a yanzu baku da uwar da ta fita, ina so kayi mata biyayya tamkar ni, kar ka gujewa umarninta, duk abin da take so ka bita kar ka musa mata kamar yadda ba za ka iya musa mini ba, ka yi mata biyayya iyakar iya wa, y'ar uwata ce wadda ba ni da kamarta, kuma ita ma na san za ta rik'e ku amana' Wannan wasiyyar ita mahaifiyar Ahmad ta ba shi, kuma ya rik'e ta k'am, bayan rasuwarta sai Hajiya ta d'auki Auwal ta cigaba da rainonsa har ya girma, da ya fara girma sai ta soma azabtar da shi, takan hana shi abinci ta d'ora masa talla, yayin da take jiyar da y'ay'an da ta haifa dad'i, duk ranar da Auwal bai sayar da tallan da ta d'ora masa ba takan azabtar da shi, duka da hantara babu kalar wanda bai ga ni ba, ta mayar da shi kamar almajirinta, akwai ranar da bai sayar da tallan ba ya ji tsoron ya koma gida saboda azabar da za ta gana masa, sai ya k'i komawa gidan ya rik'a gararamba a garin Kano inda Hajiyar ke zaune da iyalanta, a haka wata mai sayar da abinci ta tsince shi a unguwar fagge, har kuma yanzu yana hannun mai abincin yana mata aiki ita kuma tana kulawa da shi, daga baya Allah ya bayyana shi amma Hajiya bata damu ba, shi kuma mahaifinsu ba shi da cikakken k'arfi, kuma talaka ne wanda an dankwafar da shi bai isa ya ce komai ba, ga shi da hak'uri domin kusan ma Ahmad hak'urinsa ya gado, dole haka Auwal ya ci gaba da zama wurin mai abincin, har wa yau yana hannunta tana kulawa da shi, kuma haka gadon mahaifiyarsu Ahmad wanda ya kamata a ce su Ahmad d'in sun ci, yana hannunta ta rik'e ta hau kai ta danne musu, har zuwa girmansu kuma ta hana su. Mahaifin Ahmad wanda ya kasance k'ani ne ga mahaifina, wato ni da Ahmad y'an maza zar muke, ya kasance talaka sosai, amma duk da hakan ya jajirce sosai kan karatun Ahmad da yana yaro, da ya fara girma kuma da kansa yakan fita ya yi aikin k'arfi domin ya sama wa kansa kud'in makaranta. Ahmad ya kasance kamilin yaro, jajirtacce wurin neman ilimi da neman na kansa, yana da matuk'ar hak'uri, yakan hak'ura da jin dad'insa domin wani ya ji dad'i, yana da biyayya da sauk'in kai, sai dai yana da zurfin ciki da rashin magana sosai. Ahmad ya yi makarantar tahifuzul Qu'an mai suna School for Arabic and Islamic studies(SAIS) tun daga jiniyo har siniyo, babbar makaranta ce da sai masu k'wak'walwa mai kaifi ke yin ta, akwai b'angaren English, akwai b'angaren larabci, haka nan akwai tahfiz, to shi tahfiz ya yi har ya zama gangaran a b'angaren karatun Qur'ani, kuma makaranta ce ta kwana. Bayan ya kammala sakandire ya dawo gida ya kama aikin k'arfi domin ya tara kud'in cigaba da karatu, ya sha wahala sosai, wanda da Hajiya ta ba su gadonsu to da ya samu kud'in da zai tallafi rayuwarsa da ta y'an uwasa, amma ta had'a ta handame ita da y'ay'anta, kud'i ne da ita sosai, a haka ya samu ya shiga makarantar  Bilyamun Usman polytechnic (BUPOLY) ya yi diploma, inda a nan ne dab da kammalwarsa kuka had'u har soyayya ta shiga tsakaninku. Ahmad koda ya yi samartaka ba shi da irin gigin nan na samari masu tara y'ammata barkatai, bai tab'a budurwa ba koda a nan garin kuwa, sai fa a kanki, tunda ya zo da maganarki kuma muka tabbatar lallai da gaske yana miki so na hak'ik'a, domin ba k'aramin  gigicewa ya yi da ganinki ba."

Ta sauke ajiyar zuciya bayan doguwar maganar a tayi, ni kuwa gabad'aya hankalina na kanta na bata nutsuwata sosai ina kwasar karatun da na d'okanta na sani, ta d'auki ruwan da na kawo mata ta sake kurb'a ta ajiye, sannan ta kuma mayar da hakalinta kaina, na rafka tagumi ilahirin jikina ya yi lak'was kamar an watsa mini ruwan sanyi. Tayi gyaran murya ta ci ga ba da ce wa.

"Ina baki labarin nan ne ba don tsurku ko munafurci ko makamancin hakan ba, sai don ina so na fitar da ke duhun da kike ciki domin ki mik'e da addu'a a kan lamarin da ya hau kanki na zama da wad'annan mutanen, domin na san ba lallai Ahmad ya bud'e baki ya gaya miki komai ba, dalilin zurfin cikinsa da kuma yanayin tsoron da aka saka masa a zuciya, domin na tabbatar ba haka aka barshi ba, don ma ya kasance yana addu'a da halin da zai tsinci kansa ya fi haka. Game da batun aurenki ba k'aramin shiri ya yi wa auren ba, bayan kammala karatunsa ya bi k'anin mahaifinsa Abuja inda suka fara sana'a saboda bai samu aiki ba, kin san dai k'asarmu Nigeria talaka yana wahala kafin ya samu aiki, Allah ya bud'a masa domin ya samu kud'i da yawa har ya sayi fili ya fara ginin gidan da za ku zauna, kuma ya had'a lefe mai uban yawa kaya masu tsada, tunda Hajiya ta ji labari sai da ta saka shi a gaba ta karb'e takardun wannan fili da duk wasu kayayyaki da ya tara, ta ce ya bar komai a hannunta, bayan komawarsa Abuja matar nan ta saka filin a kasuwa wanda aka yi nisa da gini ta sayar, ta tako zuwa garin nan ta samu mahaifin Ahmad ta ce masa tana so a cikin gidan nan a sayar mata da kewaye domin tana so Ahmad ya zauna a cikin gidan yadda za a rik'a lura da shi da matar da ya auro, domin ta samu labarin matar da zai aura mai ilimi ce mai wankakken ido, don kar ta rik'a yi masa wayo, kuma wancan filin da ya saya daji ne sosai, ba zai yiwu a kai amarya daji ba, wannan kewayen da kike zaune shi aka saya wa Ahmad, wanda ya kasance mallakin k'anin Baban Ahmad da k'anin Babana, domin gidan na gado ne, ni ma kewayen da nake zaune gadon mahaifina ne wanda kafin a raba a ba ni na sha matuk'ar wahala sai da kusan kowa na gidan nan ya juya mini baya saboda na nemi hak'k'ina. Asalin wannan kewayen ma bayangida ne, don k'ark'ashin gadonki ma shadda ce ma'ana masai, aka rufe aka yi gyare-gyren da za ayi, aka d'an shafa farar k'asa aka yi masa kwaskwarima wuri ya d'an yi kyau. Ita Atika ita mahaifiyarta wato Hajiya ta bawa kud'in gyaran wurin, saboda ita Atikar ba mu da nisa da garin da take aure, muguwar mace ce wadda ta gaji halin mahaifiyarta na mugunta, domin idan zan baki labarin dambarwar Atika za mu kwana ban kammala miki ba. Kayan lefenki kuwa tsaf ta juyr da su zuwa ga d'anta da ta haifa, ke kuma ta saya miki kojalallun kaya da rub'ab'b'iyar akwatu aka kai miki, duk abin da ake ciki Ahmad bai sani ba yana Abuja yana ta turo mata da kud'ad'en da za ta sissiyi kayayyaki domin a k'ara a lefe, ashe duk babu abin da tayi. Sai a satin bikin da ya dawo ya tarar da komai, wallahi Rahama ba zan iya k'ayyade miki matsanancin tashin hankalin da yaron nan ya shiga ba, don kulle kansa ya yi a d'aki ya rik'a kuka, domin ba shi da yadda zai yi, ga shi a lokacin kema kin d'auki fushi da shi, shi kuma bai san ta yadda zai miki bayani ba, yana tsoron ya fad'a miki komai ki fasa aurensa bayan an jarabci zuciyarsa da matsanancin son ki, har asibiti sai da ya kwana biyu a kwance saboda yadda damuwa ta so halaka shi."

Kuka nake sosai hawaye na sharara da jin wannan tashin hankali, k'irjina ya cika da tausayin mijina da y'an uwansa, hak'ik'a an zalunce su zalinci ma fi girma, wannan wace irin rayuwa muke ciki da yayar mahaifiyarka da suka fito ciki d'aya za ta illata rayuwar y'ay'an y'ar uwarta saboda ba ta raye? Ya ilahi!

Umman Fati ta matso ta kama hannayena ta rik'e, idanuwanta cike da k'walla ta cigaba da ce wa.
"Rahama na ba ki wannan labarin ne domin ki zama mai adalci ga Ahmad, Ahmad yana matuk'ar son ki, kar ki rik'e shi a ranki da fushi kan ya b'oye miki wasu abubuwa, wallahil azim an sark'afe shi ne ta yadda ba kya zato, shawarata gare ki ki rik'e mijinki da kyau, ki so shi kamar yadda yake son ki, ki kyautata masa iya iyawarki, domin na tabbtar idan ya samu dama zai gatantaki ya mayar da ke abar kwatance, kuma ki rik'a saka shi a addu'a kan Allah ya kare shi daga azzalumai, ke ma Allah ya yi miki katangar k'arfe da su, domin mutanen nan babu Allah a ransu, za su iya aikata komai don su bak'anta muku ko su ga bayanku."

Ba zan iya kwatanta halin da na shiga a lokacin ba, sosai na rik'a shesshek'ar kuka tamkar raina zai fita, Umman fati tana rarrashina da kalamai na kwantar da hankali tare da shawarwari na gari, na goge hawayena ina shirin magana, muka ji wata k'ara da iface-iface daga babban tsakar gida, wanda ya firgitamu sai gamu tsaye daga ni har ita cikin firgici idanuwanmu a warwaje...



#Share
#Comments
#Vote






BY HASSANA D'AN LARABAWA ✍️

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now