HAYATUL ƘADRI! page 17-18

103 15 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 17-18

K'awar Mama ta dafa kafad'ata tare da jinjina kai, ta mayar da kallonta kan Mama ta ce.
"Wato Rahama tana da hankali da nutsuwa."
Mama ta saki murmushi tana jin dad'in yabon da aka yi mini, kafin ta yi magana k'awarta ta riga ta ta hanyar sanya hannu ta d'ago kaina na kalleta, ta ce mini.
"Kar ki damu Rahama, in sha Allahu na d'auki alk'awarin yi miki wannan addu'ar, kuma ina da yak'inin Allah zai amsa ya yi miki zab'in alheri a rayuwarki. Domin wuri ne na amsa addu'a ba a juyar da ita."
Sosai na ji dad'i har na bayyana mata ta hanyar godiyata.
"Na gode Allah ya k'ara girma."

************

Duk da hakan ni ma na dage da istihara kan lamarin, a gefe guda kuma Ahmad na sake k'aimi wurin damu na da zancen maganar aure, ina son sa, kuma a lokacin ne ma nake k'ara jin zuciyata ta tsumu da k'aunarsa, dalilin da yasa na rik'a jin shi d'in alheri ne a gare ni, ba tare da b'ata lokaci ba na ba shi damar turo magabatansa wurin iyayena domin su tattauna.
Ba zan iya hasaso yawan farincikin da Ahmad ya kasance a ciki ba, sai dai zan iya tunawa ya yi k'wallar farinciki a gabana tare da jaddada mini kalaman k'auna a lokacin da na ba shi damar.
"Na gode Mamina! Allah ya ninka miki adadin farincikin da kika sanya ni a wannan rana."

Zumud'i ne ya saka a washegari sai ga wakilansa a gidanmu, Abba da y'an uwansa suka yi musu tarbar girma, ba tare da b'ata lokaci ba suka bayar da kud'in aurena a ka sanya lokaci a kan da na kammala karatu a satin za a yi bikinmu.

Lokacin da k'awar Mama ta dawo daga aikin hajji ta samu labarin kawo kud'ina da Ahmad har gida ta zo taya ni murna, dayake akwai wasa tsakaninmu da ita tana da barkwanci har dungurin kaina ta dinga yi tana dariya da fad'in.
"Rahama buri ya cika, to a ba ni salalata tunda ni na dage wurin addu'ar Ahmad ya zame miki alheri."
Dariya na rik'a yi na kasa ce wa komai, da na gaji da zaulayarta ma sai na gudu d'aki na cigaba da harhad'a kayana domin komawa makaranta.

**********

Muka cigaba da karatu sosai bayan mun koma, har second semester na level 2 ta tawo k'arewa inda muke ta karatu ba ji ba gani domin mu samu sakamako mai kyau. Lokacin jarrabawa ya zo muka za na cikin sauk'i sakamakon bamu yi wasa da karatu ba, masu wasa sukai ta gwalala idanu da kallon sili da cizon kan biro.
A gefe guda ina shan fama da Aliyu bisa takurar da yake mini, shi fa da gaske matuk'ar k'aunata yake yi, kuma ba zai hak'ura da ni ba sai ya ga abinda ya turewa buzu nad'i, da na gaya masa cewar har kud'in aurena an karb'a sai ya yi murmushi ya ce mini.
"Rahama karb'ar kud'in aure ba shi ne aure ba, ba zan hak'ura da ke ba sai ranar da na ga an d'aura miki aure, kuma ina fatan sa'ar aurenki a kaina take."
Sai na saki baki kawai ina kallon k'arfin hali irin nasa.

Mun kammala level 2 lafiya sai shirin tafiya Teaching practice(T.P). Inda muka ciccike makarantun da muke so domin muje koyarwa, kowa kuma a garin da yake zai zab'i makaranta. Na cike wata makaranta da ke garinmu firamare ce, nan na yi koyarwata inda na samu had'in kan d'alibai sosai har ma da malamai dalilin iya koyarwata, duk k'ok'arin yadda zan yi domin na ga d'alibai sun iya karatu ko ba duka ba ina yi. Wannan semester d'in mun k'areta ne a (T.P) gabad'aya, wato farkon semester na lavel 3. Daga nan kuma muka je (Gamborin gala) Inda muka yi wasu kwasa-kwasai na Arabic.

Ahmad yakan zo daga Abuja wurin da yake sana'a, har nakan masa k'orafi a kan ya zauna ya dinga hutawa saboda zaryar da yake yi ta yi yawa, yakan ce mini shi ba zai iya d'aukar tsawon lokaci bai ganni ba, burinsa a kullum mu kasance tare.
A lokacin ne kuma d'an damar da na samu ta koyarwa na k'ara neman wata private ita ma ina koyarwa a cikinta, makarantar da nake (T.P) ina zuwa k'arfe takwas mu tashi sha biyu da rabi na rana, ita kuma private d'in muna shiga k'arfe biyu ne, asalin makarantar Mamanmu ce take koyarwa a cikinta, to a lokacin sai ta gamu da rashin lafiyar laulayin cikin y'an biyu da ta samu, wanda su ne suka zama autannin mu, shi ne dalilin da na karb'i koyarwar na ci gaba da yi kafin ta samu lafiya.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now