HAYATUL ƘADRI! page 31-32

116 13 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 31-32

*TALLA! TALLAH!! TALLAH!!!*

HALACCIN MAZA BIYU!

*Duk da ta kasance goyon kaka hakan bai gurb'ata tarbiyyar ta ba, sai dai ta wayi gari da rashin makusantan da sune adon duniyarta, a lokacin da ta samu shiga aljannar duniya sakamakon had'uwa da shi, a yayin ne wata guguwar k'addara ta kawo sauyi*

Shin wane sauyi ne...?

*Sihirin bai sauka kansa ba sai kan uwar da ta kawo shi duniya, wanda ya sababba tarwatsewar rayuwarsa a kan furucinta na cewar...*

Wane furuci ne...?

*Ta zab'i rabuwa da d'an da ta haifa ta shiga duniya, dalilin fuskar jaririn tana fama mata wani tabo da ya mamaye zuciyar da ke k'irjinta...*

Wane tabo ne...?

*A lokacin da ta yanke k'auna ga rayuwa, sai tayi gamo da Halacci na biyu...*

Shin wane halacci ne? Kuma wanne ne halaccin farko?

Na san kuma kuna yi wa kanku wad'annan tambayoyin, kuma za ku samu amsarsu kad'ai ne cikin gawurtaccen labarinnan mai suna *HALACCIN MAZA BIYU* wanda marubuciya *REAL LADINGO* ta rubuta. Babbar tambayar ma shin ya HALLACIN MAZA biyu yake ga mace? marubuciyar ce kad'ai ke da wannan amsar, kuma za ku same ta ta hanyar sayan labarin a kan 300 kacal👌Kar ku sake a yi babu ku domin wannan tafiyar ta daban ce🥰 Za ku iya tuntub'arta a kan wannan number +22796515805 domin sayan labarin.

D'an sauran kuzarin da ya rage mini a jikina na tattaro na ture kansa da ke saman k'irjina na mik'e a razane, da gaske maganar da ya furta ta kad'a mini y'ay'an hanjin da ke cikina, kaina ya sara, na ji hajijiya ta fara kwasata tana shirin kaini k'asa. Yadda nake kallonsa k'irjina na sama da k'asa alamar k'untacewa haka ya zuba mini ido a marairaice yana duba na, ina son furta maganar da nake so amma tsananin takaici ya saka mak'oshina bushewar da nake jin matuk'ar rad'ad'i a mak'ogorona. Cikin kai kawon da numfashina yake yi hawaye ya fara rufe mini idanu har ban ga lokacin da ya mik'e ya matso inda nake tsaye ba, na tsinci kaina ne rungume a jikinsa yana sauke mini wahalallen numfashinsa cikin kunnuwana, da cikin farinciki nake babu abin da zai hana ni taimaka masa wurin k'ara nutsar da jikina cikin jikinsa, domin dai ya samu dad'in da yake da muradi wurin kasancewa tare da ni, sai dai akasin hakan, na samu kaina ne da zame masa tamkar k'iraren itace. Can cikin kunnuwana na jiyo sautin muryarsa mai cike da rauni yana fad'in
"Don Allah Mami kar ki sa katangar k'arfe ki katange yarda da uzurin da kika saba yi mini, duk abubuwan da suke faruwa ba da son raina ba ne sai don sun zamo daga cikin k'addarata, wallahi Mami zuciyar da ke k'irjinki ba ta kai wadda ke k'irjina kasancewa cikin k'unci ba a duk sa'ilin da aka saka mana katanga, don girman Allah kiyi hak'uri Mami, watarana sai labari."
Wad'annan jawaban da yake yi su suka sake tabbatar mini da cewar da gaske fa sake bari na zai yi ya tafi, amma duk da hakan  sai na zab'i sake tabbatar da hakan ta hanyar tambayar da na watsa masa.
"Da gaske kenan dai gobe tafiyar za ka yi ka bar ni?"
Ya d'ago ni daga kafad'arsa tare da kama hannayena ya rik'e, ya tsura mini idanuwa muna kallon juna, sai kuma ya yi k'asa da kai.
"Da gaske ne Mami...Amma don Allah...
Kukan da na rushe da shi ya tsayar da maganar da yake ba tare da ya shirya ba, sai ya gigice ganin yadda na runtse idanu ina ta faman rusa kuka numfashina kamar ya d'auke saboda hakin da nake yi, tsabar rikicewa rasa yadda zai yi da ni ya yi, illa rik'o kafad'una yana girgizani cikin matuk'ar tashin hankali.
"Mami za ki haifar mini da matsala, ganin tashin hankalinki bai da misali wurin kwatanta damuwar da zan samu kaina, don Allah Mami ki fahimceni ki daina zubar da hawayen nan, bud'e idanuwanki ki kallen kin ji...
Ban fasa kukan ba, ban kuma bud'e idanuwan ba, jefa ni ya yi a k'irjinsa yana shafa bayana, bai tab'a sanin zan damu har haka da tafiyarsa ba.
K'arar da wayarsa tayi ya sa ya d'an cika ni, ina jikinsa amma rawar da jikinsa ke yi ta so ta tsoratani, a haka ya zaro wayar ya danna tare da karawa a kunnensa.
Kamar ni na d'aga wayar haka na rik'a jiyo kalaman da mai kiran wayar take furtawa.
"Ina fatan ka ji sharad'ina ko? Wanda k'etare shi daidai yake da samuwar babbar matsala a gare ka, idan har ka sake ka wuce gobe ba ka tattara ka koma Abuja ba wallahi idan ranka ya yi miliyan sai ya b'aci, mutumin banza kawai."
K'it! Ta katse wayar ba tare da ta tsaya sauraren maganar da za ta fito daga bakinsa ba, kamar kayan wanki haka ya zube a gabana kan guiwoyinsa tare da saka hannu ya rungume k'uguna, kansa bisa ruwan cikina, hawayen da ke fita ta idanuwana suna sauka bayan wuyansa suna gangarawa tsakiyar bayansa.
"Allah ga bawanka Ahmad, ka sassauta masa, ka yi masa katanga da duk wata fitina da ke tunkaro shi, ka sanyaya zuciyar matarsa daga ganin bak'insa, ka sanya salama a zuciyar da ke...
Zame hannunsa na yi daga jikina, na juya da gudu na shige cikin d'aki na fad'a kan gadona ina kuka, so nake na tausaya masa, domin na san an d'aure shi da igiyoyi masu k'arfin da ba zai iya kwancewa ba sai da taimakon Allah. Amma ai ni ma ina buk'atar a tausaya mini.
Ban san me yasa hawaye ya kasa tsayawa a idanuwana ba, sai dai na san tafiyarsa ta farko bata gigitani kamar wannan ba, kuma dalilin ba ya rasa nasaba da matuk'ar shak'uwar da muka yi da juna ba, tare da wata irin kalar soyayya da muke gwadawa juna wadda ba mu tab'a tsammanin irin ta a duniyarmu ba, damuwa ta kai damuwa, har ban san yanayin da na shiga ba domin cajin kaina sai da ya d'auke d'if!
Ya fi k'arfin awa biyu a falon bai shigo ba, ban sani ba ko kukan shi ma yake yi, sai can ya shigo yana bin bango a zatonsa ko na yi bacci, motsinsa ne kuma ya sa na runtse idanuwana tamkar mai baccin, ya zo ya rab'a gefena ya kwanta tare da rungumoni jikinsa yanata sakin ajiyar zuciya. A haka muka kwana babu batun cin abincin da na kwashe lokaci na girka, domin a yanayin abincin ba shi da muhalli a cikkunanmu.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now