HAYATUL ƘADRI! page 77-78

135 17 2
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 77-78

Tun daga Haɗejia har Kano kuka nake yi, Muhibba tana raina na kasa mantawa da kallon da tayi mini, ba zan iya fasalta hali da yanayin da na shiga ba, idan na tuna kallon da tayi mini da haɗuwar idanuwanmu guri guda, sai na ji duk duniyar ta yi mini baƙi, kuma babu abin da za a yi mini ya faranta mini.

A gidan yayan Abbanmu muka sauka, wanda yake a unguwar 'Yankaba. Ba mu jima da zuwa ba kuma Mustafa ya aiko da mota saboda ya san mun sauka, muka ɗunguma gidansa a lokacin dab da magariba ne.
Gida ne Masha'Allah babu laifi! Ya gyare gidan sosai saboda tun daga ƙasan bango har zuwa tsakiya duk tayels ne a gabaɗayan gidan, gida ne mai kyau daidai misali.

Mustafa ba tsananin kuɗi ko dukiya ba ne, sai dai yana da arziƙi da rufin asiri daidai gwargwado, kuma mai zuciyar yi ne, Ɗankasuwa ne mai sana'ar sayar da wayoyi na zamani sababbi fil masu tsada a kasuwar Beirut road.
A wannan daren aka yi jere, ɗaki ya yi kyau babu ƙarya. Hankalina bai ƙara tashi ba sai da 'yan'uwana za su tafi, saboda za su koma gidan yayan Abba su kwana, washegari kuma su juya Haɗejia.

Na rasa inda zan tsoma raina, ga tunanin Muhibba da nake ta yi a tsawon ranar tunda muka tawo ban ganta ba, yarinyar da ba na son yin nesa da ita kullum muna tare, farinciki babu shi, rai ya yi duhu.

Kafin su tafi ina wannan kukan amma sai da Anti Zulaiha ta tilasta mini ta ba ni wasu haɗe-haɗen magunguna na sha ina kukana, kuma suka ɗaukeni suka kaini har ɗakin uwargida Shamsiyya da take zaune da nata dangin, aka damƙa mata amanata sannan aka haɗu aka yi mana nasihar zama lafiya da juna da kaucewa gutsiri tsoma da cutar da juna.

Kaina yana ƙasa ban ɗago ba har aka yi addu'a aka shafa, sannan dangina suka kaini wajen  dangin Mustafa da ke sitting room a zaune, nan ma sun saka mana albarka a auren, sannan sun ce matar Mustafa tana da haƙuri ba sa wa ba fitarwa, don haka ni ma na yi kwaikwayo da ita don mu zauna lafiya da juna. Sun yabe ta dai sosai, a yayin da ni ma dangina suka yabe ni cewar ni ma ina da haƙuri, domin a tarihin rayuwata ba ni da abokin faɗa, na iya zama da mutane dabkawar da kai a al'amura.

Kafin su tafi sai da suka ci abinci, wanda ƙannen Mustafa ne suka dafa Jalop ɗin taliya da ta sha kifi da kaji, ga kuma lemuka da ruwa, suka ci suka yi ƙat.

Suka tattara suka tafi duk da kukan da nake yi, suka bar ni daga ni sai Ummu Maryam.

Ummu Maryam wata mace ce mai matuƙar kirki da haɗuwar social media ta haɗa ni da ita, domin a group ɗin da na haɗu da Mustafa ita ma muka haɗu, jinina da ita ya haɗu ne sakamakon kirkinta da addininta da kuma haƙurinta, sannan kusan ita ma ta haɗu da ƙaddarorin rayuwar aure, uwar miji da kishiya suka takura mata sai da suka raba ta da mijin da yaransu guda biyar, 'yar garin Azare ce. Mun shaƙu sosai, a lokacin da ta ji za mu yi aure ni da Mustafa ta yi murna sosai, saboda ta san Mustafa a cikin group ɗin kamilin mutum ne, ta taya ni murna.

Ummu Maryam sai da ta tako har Haɗejia a ranar bikin, ta kawo mini gudummawar turarukan wuta da Humra masu ƙamshi, har da kayan gyaran jiki, da ita aka sha shagalin bikin, kuma bata tafi ba sai da ta rako ni har gidana a Kano.

Sai bayan isha'i sannan Ummu Maryam ta tafi, bayan ta cika ni da nasihohi da shawarwari na gari. Muka yi sallama ina ta kuka tana ba ni haƙuri, ita ma ta tafi ta bar ni, sai ni ɗaya tal a cikin ɗakin nawa.

A tsorace nake, ga kuma tarin damuwa, hakan ya sababba mini shiga cikin wani irin yanayi mara daɗi, har zuwa lokacin da na ji shigowar Mustafa cikin gidan, kuma bai shigo ɗakina ba sai da ya zarce wurin uwargida Shamsiyya.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now