HAYATUL ƘADRI page 67-68

108 22 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 67-68

*KU YI HAƘURI TSAWON KWANA BIYU DA BAKU JI NI BA, SABGOGI DA AYYUKA SUN MINI YAWA, WALLAHI YANZU MA DA ƘYAR NA DAURE NA JINGINE WASU ABUBUWAN NA YI MUKU DON NA FARANTA MUKU, A CIKIN KWANAKIN NAN DA SUKA WUCE NA ƘARA HAƘIƘANCEWA LABARIN HAYATUL ƘADRI YA KAI INDA BA NA ZATO, YA SAMU KARƁUWA FIYE DA TUNANINA, INA GODIYA SOSAI, ALLAH YA BAR ZUMUNCI.*

HAPPY TAKUTAHA. ALLAH YA BAMU ALBARKACIN WANNAN RANA MAI TARIN ALBARKA, ALLAH YA ƘARA TSIRA DA AMINCI GA SHUGABANMU ANNABI MUHAMMAD (S A W), ALLAH YA ƘARA MANA SOYAYYAR MA'AIKI.

ALLAH ya nufe ni da yin mu'amala da su, mu'amalar da na zace ta a girmama juna saboda zaman tare, sai ga shi ban ankara ba ta rikiɗe ta yi birgima zuwa ga komawa mu'amalar soyayya, kowanne kuma burinsa ya zama ƙyallin da zan maƙala a goshina domin ya riƙa haskaka mini gabana.
Kodayake, mutum biyu ne a lokaci guda suka fara shan sharafinsu, wato Sahabi da Abdul Jalal, yayin da Mustafa ya koma gefe ya zama ɗan kallo, tare da kawar da kai kamar bai san abin da ke tsakanina da su ba, saboda shi ɗin miskilin mutum ne na bugawa a jarida, sai ya bar su su biyu a fagen suna badam-badama, suna takara da juna da jin haushin juna, domin kowanne daga cikinsu burin shi ya farauto zuciyata zuwa ga soyayyar shi, a yayin da ni kuma tuni na rufe babin soyayyar, saboda ban riski wani abin ƙawa ko zakwaɗi da marmari ga sake afkawa cikinta ba.
Bari mu fara da batun Sahabi, wanda ya fito daga garin Katsina ta dikko ɗakin kara, nagartaccen mutum ne da ya mallaki mace guda ɗaya, sai ga shi a dalilin wannan group ya yi arangama da ni, kuma a take ya kwaɗaitu da son na zame masa mace ta biyu da mu'amala irin ta aure za ta shiga tsakanina da shi. Yakan bi ni private ya yi mini magana tare da miƙo gaisuwa, amma ban taɓa amsa masa ba, saboda a ƙa'idata idan na ga an mini magana nakan fara duba sunan wanda ya yi mini magana, idan mace ce zan amsa, idan namiji ne kuma ba zan amsa ba, sai dai na yi magana da shi a cikin group yadda kowa zai ga ni.
Da ya ga naƙi amsa maganar sai ya kira ni ta waya, sai da na ɗaga sannan na ji muryar namiji.
"Assalamu alaiki, suna na Sahabi Ɗanmusa, ɗaya daga cikin ɗaliban ki na group ɗin (Mu ƙaru da juna)."
Na fahimci ko wane ne, saboda yana bayar da gudummawa sosai wajen bunƙasar group ɗin da kawo cigaba, na ɗan saki muryata wurin amsa masa.
"Ma sha ALLAH, malam Sahabi ya himma?"
Ya amsa da ce wa, "Alhamdulillah! Ina ta magana ta private amma babu amsa, shi ya sa na yi tunanin kiranki, sai ga shi na samu tagomashin jin kamilalliyar muryar da ake mana rowarta ma."
Na yi ɗan murmushi na ce,
"Ka san doka ne namiji ya bi mace private ko?"
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce.
"Idan kuma wata alaƙa mai girma ce take shirin ƙulluwa fa?"
Cikin mamaki na tambaye shi.
"Alaƙa? Wace irin alaƙa kenan?"
Ya sanyaya murya ya ce.
"Ta soyayya mana, irin wadda za ta girma sosai har ta kai ga auren juna."
Wannan maganar da ya yi ita ta sanyayar mini da jikina, kawai sai na sauke wayar daga kunnuwana ba tare da na ba shi amsa ba.
Tun daga ranar Sahabi bai bar ni na huta ba, ya cigaba da yaƙin yaɗa manufarsa, tun ina ƙi tare da dojewa har ya ci nasara a kaina na fara sauraren shi, wanda na yi hakan ne kawai don na samu mu rabu lafiya tunda ni ba aure ne a gabana ba a lokacin. Ganin na ɗan saki jiki da shi sai ya fara murna a zaton shi tuni na fara son shi.
A daidai wannan lokaci ne shi ma Abdul Jalal aka jarrabe shi da so na, mazaunin Abuja ne kuma babban malami ne, lakcara ne, babban mutum don har ya soma manyanta ma. Ya kasance mutum masanin ilimin addini sosai.
Na wayi gari ne kawai na ganni a cikin wani group nasa, wanda ba a magana da Hausa sai da larabci, ana koya larabci sosai a ciki da karatuttuka na addini, to ashe shi ne ya saka ni, saboda ganin yadda nake bayar da gudummawa sosai a group ɗin da muke tare, wajen yaɗa da'awa da kuma tsantsar nutsuwar da ke tare da ni.
Tunda na lura namiji ne ya saka ni a group ɗin sai ban yi magana ba, sai daga baya ya zo yake ba ni haƙuri cikin harshen larabci yake faɗa mini ce wa.
"Kiyi haƙuri malama, kiyi mini uzuri, na ɗauki lambarki na saka ki a cikin group ba tare da amincewarki ba, wallahi kin cancanta da zama a group ɗin ne shi ya sa na saka ki, saboda gudummawar da kike ba wa musulunci da musulmai."
Da na ga abu ne na ƙaruwa sai ban damu ba, na amsa masa da "Babu komai, ALLAH ya sa mu dace."
Daga wanna lokaci ne kuma muka ci gaba da gaisawa ni da shi, kuma idan zai mini magana da larabci yake mini, haka ni ma da larabcin nake mayar masa da amsa, saboda na lura kamilin mutum ne sosai.
Shi ma yana da mata guda ɗaya, da yara guda biyu manya, ɗaya ɗan shekara ashirin, ɗaya kuma shekara goma sha takwas.
Abdul Jalal ya bayyana mini yana so na, wanda ina matuƙar ganin girmansa dalilin yawan shekarunsa kuma ga shi malami, sun kafa takara lokaci ɗaya shi da Sahabi, wanda kusan hankalina ya fi karkata ga Abdul Jalal saboda wani naƙasu da na fuskanta daga shi Sahabi, naƙasun da ya jawo na ga ba zan iya tsayawa soyayya da shi ba balle ma har ta kai ni ga aurensa.
Yana da kishi sosai, wanda ko a group ya ga Abdul Jalal ya yi magana na kula shi tofa zai biyo ni ta private ne ya yi ta mini ɗacin rai tare da fito da kishinsa a fili, haka nan wata ɗabi'a da ya fara kwaso mini ita ce, yawan kawo mini zancen matarsa da yake yi, da gaya mini laifukanta da wurin da ta gaza da shi, ni kuma sai na ga ba zan iya jura ba, saboda ciwon 'ya mace na 'ya mace ne, yaushe zan zauna yana kwaso mini zancwn matarsa yana kawo mini, ni ma watarana zai kwashi nawa zancen ya kai wa wata kenan, nan da nan ya ƙarasa ficewa a raina, domin ba zan iya zama da namiji mai bakin ganga ba, mai kwashe sirrin matarsa yana yaɗawa duniya. Ya san wasu abubuwa da suka shafi ɓangarena, to amma sai na mayar da hankali ga addu'ar ALLAH ya yi mini zaɓi na gari cikin rayuwata ta gaba, ban jima ina addu'ar ba na ji gabaɗaya Sahabi ya fice mini daga rai, a take kuwa na ja baya da shi.
Mafarin rabuwata da shi kenan, wanda na ɗan fara mayar da hankalina kan Abdul Jalal, da nake ganin ba zan samu wani naƙasu a tare da shi ba, tunda shi ɗin mai yawan shekaru ne, ga hankali, ga kuma tarin ilimi na addini, don a lokacin ma yana jagorantar wani sashe cikin masallacin Abuja.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now