HAYATUL ƘADRI! page 37-38

120 17 4
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 37-38

Kallon da yake mini cikin firgici da tsantsar tsoron yadda kamannina suka sauya a cikin idanuwansa, har jakar da ke hannunsa ta faɗi ƙasa bai sani ba, ni kuma sai na sunkuyar da kai hawaye ya fara zubo mini, wata matsananciyar kunya ta rufe ni da ganin yadda ya zo ya same ni. Babu wani gyara babu kintsi, na harbitse na yagalgale domin babu kayan gyaran.
Cikin maƙurar tashin hankali ya matso gare ni ya durƙushe gabana ya zuba mini idanuwa da mamakin ganina a wannan yanayi wanda bai taɓa zato ko tsammani ba, ya riƙo hannuna da naman jiki duk ya zagwanye sai tarin ƙasusuwa da jijiyoyi, na ɗaga kaina muka haɗa ido a yayin da hawaye ya zubo masa, ya miƙe tsaye tare da miƙar da ni tsaye yana ta ƙare mini kallo daga sama har ƙasa da tunanin ko an canja masa ni, cikin rawar baki ya iya furta ce wa.
"Mamina! Ke ce kika dawo haka?"
Hawaye kawai nake fitarwa na kasa magana. Ahmad ya fashe da wani irin kuka ya zube bisa guiwoyinsa ina daga tsaye, ya kife kansa kan laƙumammen cikina da yunwa ta gama rarakewa tamkar ya haɗe da bayana, kuka na fitar hankali yake yi jikinsa na mugu-mugun rawa haɗi da furta wasu irin kalamai.
"ALLAH ka yafe mini zalincin da nake wa wannan baiwa taka, ALLAH ka yi mini afuwa da gafara kar ka kama ni da alhakin rashin riƙe amanar da ka danƙa mini, ALLAH ni mai laifi ne saboda na kasance mai zalinci, ka dube ni ka yi mini sassauci a lokacin da za ka yiwa Mami sakayya a kaina...
Kalaman da yake furtawa da yadda na riƙa tuna azabar da wahalar da na sha lokacin da baya nan, su suka sababba mini fashewa da wani irin kuka tamkar na shiɗe, na zame na durƙushe kamar yadda yake a durƙushe, shi yana kukan tausayina ni ina kukan tausayin shi, da ƙyar ya iya ɗago hannu ya tallafi fuskata da ta canja launi daga fara zuwa baƙa, hawaye na shatata ya buɗe baki ya ce.
"Ni ban san da wane baki zan baki haƙuri ba, ban san da muryar da zan yi amfani wurin neman afuwarki ba, sai dai dole na nema saboda ina tsoron hukuncin da Ubangiji zai tanada a kaina, na yin wasarere da hakkinki da ya rataya a wuyana. Ban kasance azzalumi ba Mamina, saboda ALLAH ya haramta shi a kansa kuma ya haramta shi a tsakaninmu mu bayinsa, amma ina da yaƙinin a yanzu dole zuciyarki da bakinki su ambace ni da azzalu...
Hannu na kai na rufe masa baki tare da girgiza  masa kai, a cikin muryar kuka nake ce masa.
"Kai ba azzalumi ba ne, kai mutum ne na gari mai ƙoƙarin sauke nauyin da ALLAH ya ɗora maka, illa wata ƙaddara da ke watangaririya da kai da neman sauya maka suna daga mutum na gari zuwa akasin haka, amma ka sani, ko muryoyin mutanen duniya gabaɗaya za su haɗu suna faɗin kai azzalumi ne, to muryata za ta dawwama wajen ƙaryatasu da faɗin mijina salihin bawan bawan ALLAH ne, mijina mai tsoron ALLAH ne, mijina mai kyautatawa ne, mijina mai yi don ALLAH ne, mijina mai kyakkyawar zuciya ne, mijina mai...
Ya faɗo saman ƙirjina tare da rungumeni tamkar ya nutsa ni cikin jikinsa yana shessheƙar kuka.
"Mami! Na yarda kowa ya zage ni idan za ki yabe ni, na yarda kowa ya ga baƙina idan za ki ga farina, na yarda kowa ya aibatani idan za ki kare ni, ke ɗin rahama ce a gare ni, ina son ki Mami! Ina ƙaunarki Mami! Ina fatan na rayu da ke har ƙarshen numfashina, ina roƙon ALLAH ya ba ni ikon kyautata miki fiye da kowane namiji da zai kyautatawa matar aurensa."
Haka ya riƙa faɗa mini kalamai cikin kuka, na ɗago shi na riƙa share masa hawaye, ni a lokacin ne ma nake jin matuƙar ƙaunarsa na sake ratsa ni, na san ba yin kansa ba ne, don shi kansa ya yi tsananin rama duk ya fita daga hayyacinsa.
Wucewar mintuna muka samu nutsuwa daga kukan da muka sha, sai ya zame ni daga jikin shi ya miƙe da hanzari ya fita, ma bishi da kallo ƙirjina yana ta faman bugu.
Ina nan zaune bai jima sosai ba sai ga shi ya dawo da leda a hannunsa, kayan kwalliya ne kala-kala da sabulai na gyaran fata, da kansa ya hura ragowar itacen da nake da shi ya ɗora ruwan zafi, bayan ya tafasa ya juye ya kai mini banɗaki, ya zo ya kama ni muka shiga tare, tamkar jaririya haka Ahmad ya yi mini wanka saboda ba ni da kuzari, da muka fito shi ya ɗauko kayan kwalliyar ya zube a gabana, shi burinsa na yi kwalliya na fito ras kamar lokacin baya, wanda kuma hakan ba zai yiwu ba, na kwashe lokaci cikin yanayi mara daɗi na fita daga kamannina, ba zai yiwu a ce lokaci guda na dawo kamar da ba, don ko kwalliya na yi kwata-kwata ba na kyah, kwalliyar takan fita daban, ni ma daban, saboda tsananin duhu da ramar da na yi.
Haka ya riƙa rarumo kaya yana ba ni wai na saka, ya ɗauko sarƙa ya saka mini, shi fa a lallai so yake ya ga na yi kyau sosai har ma nafi kowa kyau tunda biki ake yi, haka dai ya taya ni na ɗan yi kwalliyar duk da ban yi wani kyau ba, amma shi sai yaba ni yake yi.
Muka ci abincin da ya sayo mana mai daɗi har da nama, wanda rabon da na ci irinsa ni dai ba zan iya tunawa ba.
Aka yi kamun amarya, gida ya cika da jama'a ana ta hidima, amma Ahmad ya ƙi fita ko ina yana manne a kewayenmu, mintuna kaɗan zai yi kirana, da zarar na je kuma babu wata magana sai dai ya ce mini wai ya kirawo ni ne don kawai ya kalle ni ya ji daɗi, sai dai na yi mirmushi kawai, yakan janyoni ya rungumeni tare da 'yan tsotse-tsotsensa sannam ya bar ni na koma, ba za a jima ba zai sake kirana. A daren kam ba mu ba wa soyayya kunya ba, domin sai da muka ƙure zuwa babban birnin maji daɗi.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now