HAYATUL ƘADRI! page 71-72

105 19 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 71-72

*DON ALLAH MA SU TAMBAYA SUNA SO DAGA FARKO SUYI HAƘURI HAR A KAMMALA SAI SU SAMU COMPLETE, WALLAHI YANZU NA YI NISA SOSAI INA SHAN WAHALA WAJEN TURA MUKU DAGA FARKO, KO KU TAMBAYA A GROUPS ZA KU SAMU. NA GODE*

Na rikice; na gigice; da ganin wannan saƙo, wanda rikicewar da na yi a lokacin da Ahmad ya bayyana mini soyayya a falon Asiya sai ta zama nafila, bayyanawar mustafa ta zama farilla duk da a cikin waya ne ba ido da ido ba. Tsigar jikina tayi masifar miƙewa jikina ya riƙa rawa, ban ma san lokacin da na danne wayar na kashe ta gabaɗaya ba, na ja jiki can gefe na maƙure na kwanta ina mayar da numfashi idanuwana a runtse.
Kalamansa sun mini nauyi ɗingiringim! Na rasa inda zan tsoma raina, ga ni nan ne dai ban san abin da ke yawo a zuciyata ba.
Tunda na kashe wayar kuma sai da na kwashe kusan kwana huɗu ko kallon inda take ban yi ba balle na kunna na ci karo da saƙon shi, ko kuma ya addabe ni da kira, sai dai a tsawon waɗannan kwana huɗu a gida ma sai da aka gane sauyi a tare da ni, na rage yawan magana da kazar-kazar, sai yawan tunani da kwanciya, ko makaranta na je ba na asshaka abin arziƙi.
A cikin kwana na biyar ne na buɗe wayata, ba zan iya lissafa adadin saƙonnin da na tarar daga gare shi ba, ta ko'ina saƙonni ne rututu suke ta shigowa a jejjere, wayata har wani ƙamewa take yi.
Da ƙyar na iya fara duba saƙonnin jiki na mazari, tun kafin na yi nisa jikina ya mace murus, saboda wasu irin azababbun kalamai na kaiwa maƙura a soyayya da ya riƙa turo mini, waɗanda suka sanyayar mini da jiki gabaɗaya.

'Ban taɓa gamuwa da yarinyar da ta shiga zuciyata lokaci guda ba kuma ta yi mini mugun kamu ba tare da kuma na taɓa ganin ta ba irin ki, wallahi ina son ki domin kin tattara abubuwa da yawa wanda samun ki ga kowane namiji kawai rabo ne, kuma lallai da gasken gaske kin fi mini mata million ba adadi, wannan sirrin zuciyata ne amma dole na fito na bayyana miki yanda nake jin ki a raina, ALLAH ne shaidata, soyayyarki a gare ni min indillahi ce.'

Sai kuma waɗansu irin kalamai na rauni da ya rubuto mini wanda suke alamta yana cikin tsananin tashin hankali da rashin jin amsata.

"Daga ma'adanar sirrina, wato zuciyata da ruhina, nake ɗauko miki rahoton da ke ciki game da duhun da suka samu kansu ciki a yayin da suka laluba suka tarar kin yi ɓatan dabo. JANNAT (Kamar yadda zuciyata ta ambace ki da sunan dalilin kin zamo aljannata), ba zan ɓoye miki ba kin azabtar da zuciyata azabar da ba ta taɓa riska ba, da na san cewa idan na furta miki abin da ke zuciyata game da ke hakan za ta faru da na haƙura na cigaba da jinyar zuciyata koda hakan zai kassara ragowar kuzarina, na fi ƙaunar farincikinki fiye da komai, ina tausayinki, na yi nadama fiye da komai, ki gafarta mini Jannat, don Allah kiyi haƙuri idan na saɓa miki...

Danshin da na ji a fuskata ya tabbatar mini da hawayena ne ke zuba, na kai hannu na share wasu na ƙara ɓullowa, sosai zuciyata ta yi rauni, musamman da na yi ƙasa sosai na karanta saƙon da ya kasance kusan na ƙarshe.

"Duniya ta yi mini zafi a lokacin da na wayi gari ko gilmawarki ba na gani, ban san ta inda zan same ki ba Jannat, ban san kowa naki ba bare ya sada ni da ke, makamin da na rike shi ne sanin sunan garin da ya kasance mahaifarki, wanda shi na rike ya zame mini tsani wajen ɗaukar ƙafa na nufi Haɗejia hankali a tashe domin nemanki. Na je Haɗejia ban san kowa ba sai ke, ke kuma kin ɓacewa ganina, na yi gararamba sosai tamkar mahaukaci ina neman inda zan gan ki, sai dai ban samu nasara ba saboda ko sunan unguwarku ba ki ambata cikin labarinki da kika ba ni ba, haka na riƙa bin mutane ina tambayarsu inda zan gan ki, wasu su amsa mini da basu sani ba, wasu suyi mini kallon mara kai, haka na wuni ina garari da yawo a garinku sannan na juya zuciyata tana mini ciwo matsananci."

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now