HAYATUL ƘADRI! page 89-90

308 24 1
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 89-90

*ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!*

Sai ta ɗauki wani salo na duk ranar girkinta sai ta yi girki kaɗan wanda ba zai isa ba, idan ta yi girkin sai ta juyewa yaran su tafi da shi makaranta ta bar mana ɗan'kaɗan, to daman tuni Mustafa ya kafa mana wata ƙa'ida ta cin abinci tare, a ganinsa hakan zai ƙara mana danƙon zumunci da zama lafiya.

Na saka mata ido a kan hakan ban tanka ba, har dai ta ƙure ni na gaji, saboda gabaɗaya ba na ƙoshi abincin ɗan'mitsil take zubowa wanda ko ni kaɗai ya mini kaɗan ba ma mu biyu ba.

Da Allah ya tashi tona mata asiri ranar yana gida bai fita ba, ta girka abincin ta zuba wa yara, mu kuma ta zubo mana ragowar har da shi domin mu ci, ƙila mantawa ta yi tare da shi za mu ci shi ya sa, sai da muka zauna cin abincin sannan ya kalli abincin sosai ya yamutsa fuska ya dube ta fuskarsa cikin alamar tambaya sannan ya yi magana.

"Wannan abincin fa? Jarirai kika zubowa ne?"

Ta kama sosa kai tana far-far da idanu, murya na rawa ta amsa masa.

"Daman fa bai isa ba ne."

Ya tsura mata idanu ya ce.

"Ban gane bai isa ba! Abincin ne kwata-kwata babu a gidan ko yaya?"

Kanta a sunkuye ta amsa.

"A'a! Akwai ragowar dafaffe, amma na dare ne na ajiye saboda ba na son na kuma yin girki."

Ya yi murmushin takaici ya ce.

"To kin san dai mu ba ƙananan yara ba ne da wannan abincin zai ishe mu, don haka ki tashi ki ɗauko wancan ki juye mana da daren kya ƙara dafa wani, ba na son ƙwauron abinci."

Da ta ji abin da ya ce sai ta fara gardama wai ita fa ba za ta kuma wani girkin ba, aikuwa ya rufe ta da bala'i kamar zai kai mata duka, ya fusata ainun, nan da nan ta shiga taitayinta ta miƙe ta ɗauko abincin.

To da ta ga hakan sai ta daina baƙin halin idan ta fuskanci yana nan, sai idan ni da ita ne sai ta tsifaro abincin kaɗan, ni kuwa da na fita iya shege da mun cinye ɗaukar faranti nake na nufi ktcheen na ƙaro a wansa ta ajiye na dare, tunda ta ɗorawa kanta rayuwar girkin tazarce, idan har ban ƙoshi ba ƙarowa nake in zauna a gabanta kuma in ci abuna in ce mata ni ban ƙoshi ba, ruwanta ne ta ƙara dafawa ruwanta ne ta bar shi hakan.

Wani lokaci da daddare idan ya dawo sai ta je masa da ƙorafin wai abinci bai isaba, shi kuwa ya yi fuska ya ce mata.

"Ai ba abincin muka rasa a gidan nan ba, idan buhu guda kika so dafawa ga shi nan a zube, me ya sa kike yin kaɗan? Me ya sa duk ranar girkinki abinci yake yin kaɗan?"

A wannan lokacin sai na ga bari na faɗa masa kawai, tunda ina ta rufa mata asiri kan abubuwan da take yi amma ta kasa hankalta, ƙila idan na faɗa masa wannan za ta hankalta, shi ya sa na dube shi na ce masa.

"Abin da ya sa duk ranar girkinta abinci yake yin kaɗan ɗan'mitsitsi take dafawa, idan ma ta dafa dayawa sai ta jibgawa yaran su tafi makaranta da shi, mu kuma ta ba mu kaɗan, kullum sai na shiga ktcheen na ƙaro da kaina, don yau ma ban ƙoshi ba sai da na shiga na ƙaro.

Aikam sai ya rufe ta da faɗa, ta inda ya shiga ba ta nan yake fita ba, ya riƙa faɗin.

"Na fara gajiya da baƙin halin da kika ɗorawa kanki Shamsiyya, idan ma wasu kr zuga ki a waje za su kaiki su baro ki, domin ni dai kin sani ba zan ɗauki wannan iskancin ba, ban ga macen da za ta hana ni zaman lafiya a gidana ta riƙa haifar mini da fitintinu ba, me kike so ne? Me aka yi miki? Me na rage ki da shi da kullum sai kin fito da wata matsalar? Kina babba amma kin kasa riƙe girmanki, haka kike so 'ya'yanki su tashi su ga kina yi su ma su koya? Ya kamata ki mayar da hankalinki."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 22, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now