HAYATUL ƘADRI! page 19-20

102 14 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 19- 20

"Yaushe kika fara k'arya Rahama? Yaushe kika zama mak'aryaciya bamu sani ba? Me ya fara canja ki daga asalin yadda kike?" Kalaman da Anti Zulaiha ta ambata mini kenan, wadda a yanayin da na ji muryarta na fita na tabbatar tana cikin matsanancin b'acin rai. K'afafuwana suka fara rawa tamkar ba za su d'auki gangar jikina ba, a hankali na zame jiki na rab'a gefen gado na zauna ina numfarfashi, da k'yar na iya fizgo magana na furta saboda yadda mak'oshina ke k'ok'arin cushe wa.
"Anti Zulaiha me ya had'a ni da k'arya? 'Hanyar jirgi daban, haka nan hanyar mota daban' Don Allah warware mini k'ullin saboda na rikice."
Na sake jiyo muryarta mai d'auke da b'acin rai tana fad'in.
"Duk da kin raba hanya da k'arya wannan karon kin rab'e ta dalilin Ahmad."
"Ban fahimta ba Anti, me ya kawo Ahmad cikin maganar? Don Allah sanar da ni." Ban tab'a ambatar sunansa ba sai a ranar saboda rud'e wa, ina girmama sunan kamar yadda yake girmama sunana.
"Kin wa Abba da Mama k'arya, kin ce musu Ahmad ya gina gidan da za ku zauna, mun nemi mu je ganin gida don auna labulaye da yadda za a yi tsarin jere, sai aka nausa da mu cikin wani k'auye, cikin wani gida mai d'auke da mata bakwai rigis, ke ce za ki zama ta takwas, d'akin da za ki zauna mai d'auke da jar k'asa babu siminti ko na naira biyar, wanda aka rufe shi da rufin leda."
Na dafe kaina saboda sarawar da ya yi, da Hausa tayi maganar yadda zan fi fahimta amma tabbas ba komai na fahimta ba saboda rud'ewar da na yi. Anti Zulaiha ta ci gaba da magana a harzuk'e.
"Yanzu don Allah mene ne ribar k'aryar da ya zabga miki har kema kika zabga wa su Abba k'aryar, kika sa suka kashe kud'i suka tanadar miki abubuwa na more rayuwa domin ki ji dad'i, wallahi Rahama a kaso biyar na abinda aka tanadar miki kaso d'aya ba zai shiga akurkin kejin da ya tanada domin ki ba, duk da ba burinki ne auren mai kud'i ba amma ban ga ta yadda za a yi ki iya rayuwa a wannan k'auyen kina da iliminki da wayewarki ba, tun farko me yasa bai fad'a miki gaskiy ba? Ya zauna ya shirga miki k'arya tare da d'ora ki a keken b'era, sai yanzu da komai ya zo gab sannan halinsa ya fito, Rahama ina mai bak'incikin shaida miki Ahmad bai dace da ke ba, don haka kiyi nazari da tunani."
K'it! Ta katse wayar ta bar ni da gwama numfashi da saraftun hawaye bisa kan fuskata, wayar da ke hannuna ta zame ta fad'i, a yayin da ina daga zaune amma hajijiya nake gani a idanuwana, da jiri ya d'ebe ni sai ga ni yab'ar kwance a gadon ina juya kaina da nake jin tamkar an d'ora masa dakon dutsen dala, ba zan iya k'iyasta mintunan da na kwashe a wannan yanayi ba har su Saudat suka zo suka same ni a haka, hankalinsu ya yi matuk'ar tashi suka rud'e suna tambayata abin da ya faru, amma nak'i ce musu komai, sai a lokacin ne ma zuciyata ta karye na rik'a kuka hawaye na malala, suka yi juyin duniya domin na fad'a musu damuwata amma na kasa, sai suka hak'ura suka cigaba da rarrashina, a take zazzab'i ya rufe ni na ka sa cin komai sai rawar d'ari nake, Saudat, Kadija, da Halima duk hankulansu suka kasa kwanciya da yanayin da na samu kaina a ciki.
Zan iya ce wa a tun rayuwar fara karatuna ban tab'a kasancewa cikin damuwa kamar lokacin ba, ga shi jarrabawa muke yi ina da buk'atar nutsuwar jiki da ta zuciya, amma hakan ya gagara, ko jarrabawar nake zana wa tunanina ba a kanta yake ba yana wata duniyar, ba don Allah ya taimakeni ya yi ni da k'wak'walwa ba to da na san tabbas a wannan jarrabawa sai na fad'i, amma da taimakon Allah na kammala zana jarrabawar tsaf muka fara shirye-shiryen komawa gida.
Zuwa wannan lokaci ba zan iya k'iyasta yawan adadin kiran da Ahmad ya yi mini a waya ba, amma ban tab'a gigin d'auka ba, idan na ga lambarsa ma wani takaici ne yake k'ume ni na ji tamkar na saka kuka, text kuwa na kalaman k'auna da rarrashi ko duba su ba na yi nake gogewa, saboda a ganina ba shi da abin da zai fad'a mini, na ba shi dukkan yardata na guji maza da yawa ciki har da y'an uwana amma shi ne zai saka mini da k'arya, yau da a ce ya fito ya fad'a mini gaskiyar magana tun farko ba zan ji komai ba, ba zan je na fad'a wa iyayena abin da ba haka ba, amma a yanzu kunyar na koma gida na had'a idanu da su nake yi, ba su tab'a kama ni da wata k'arya ba sai a dalilinsa yanzu.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now