HAYATUL ƘADRI! page 59-60

122 14 0
                                    

*HAYATUL ƘADRI!*

(LABARIN DA YA FARU A GASKE)

*HASSANA ƊAN LARABAWA* ✍️

EXQUISITE WRITER'S FORUM (EWF)

🅿️ 59-60

Abin da na ga ni a cikin wannan mafarki shi ne:
Da ni da shi muna cikin tafiya a cikin wata maƙabarta muna ta zagayawa, kawai sai wani ƙabari ya buɗe, sai ga abin da ke cikin ƙabarin ya fito tamkar fatalwa, ta yo kanmu a yayin da yake riƙe da hannuna muna wani irin gudu saboda tsoro, fatalwar kuma ba ta fasa bin mu ba, Muhibba tana hannuna, muna ta gudu har muka samu nasarar fitowa daga maƙabartar zuwa cikin gari saboda maƙabartar cikin jeji take. Muka tsaya muna sauke wahalallen numfashi a lokacin da ya ƙara damƙe hannuna muka haɗa idanuwa, sai ya sheƙe da dariya yana faɗin.
'Tsoro ne da ke daman Mami? Haka kike da tsoro?'
Na zumɓuro baki gaba na ce.
'Ai ka fi ni tsoro, tunda kai namiji ne, ni kuma mace ce.'
Ya ƙyalƙyale da dariya, muka wuce muka ci gaba da tafiyarmu, mun ɓullo wata kwana kenan sai muka ga taron mutane sosai kamar ana zaman makoki, sai dai alamun mutanen da yadda fuskokinsu suka nuna kamar taron ɗaurin aure ne, sai dai gabaɗayansu jajayen kaya ne a jikinsu, muna zuwa wurin suka nufo mu suka damƙi Ahmad, yana tirjewa yana gudu amma haka suka danne shi suka saka masa irin kayan jikinsu, ni kuma ina tsaye daga gefe jikina sai rawa yake yi, sai a lokacin waɗannan mutanen suke faɗin ɗaurin auren Ahmad za a yi da wata. Ina tsaye har aka ɗaura auren, wanda sai a lokacin ya samu kuɓucewa daga hannunsu ya tashi ya cire rigar ya wurgar, ya nufo inda nake a guje yana kiran sunana yana kuka, sai da ya zo dab da ni ƙiris ya rage ya ƙaraso sai kuma wani irin nisa ya shigo tsakaninmu, ga shi dab da ni, amma mun kasa kusantar juna kamar wanda ake zuƙewa ta baya, nisan ya yi yawa, a lokacin kuka nake sosai, shi kuma sai ɗago mini hannu yake muryarsa na amsa-amo a filin wurin yana faɗin.
"Mami ki tsaya, kar ki tafi ki bar ni a wurin nan, ki tsaya kin ji Mamina."
Ni kuma ganin hakan ya ƙi tawowa wurina sai na yi fushi na tafi ina kuka, yana ta ƙwala mini kira na ƙi juyawa. Ina tafe har na ƙarasa gidan yayan Mama wato Kawu Aliyu da ya taɓa taimaka mana, na tarar ana taron suna matarsa fa haihu. To a lokacin ne na farka daga wannan mafarki da ya rikitani na ka sa bambance abin da mafarkin ke nufi, duk jikina a sanyaye nake faɗa wa Mama abin da na ga ni a mafarkin, sai Mama ta kwantar mini da hankali da faɗin.
"Kar ki damu Rahamatullahi, babu komai in sha Allahu sai tarin alheri."
Mama tana rufe baki sai ga kiran waya, tunda ta ɗaga na ji tana ambatar 'Innalillahi wa inna ilaihir raji'un' Sai gabana ya yi wata irin faɗuwa kamar ya ruguzo, na riƙeta gam ina tambayarta.
"Mene ne ya faru Mama? Don ALLAH mene ne ya faru?"
Ta sauke waya jikinta a sanyaye ta sanar da ni rasuwar yayan Abbanmu wanda yake zaune a Kano, mun ji raauwar sosai, wanda ni kuma sai na jingina wannan mafarki da na yi da rasuwar, a tunani na daman rasuwar za a yi shi ya sa na yi wannan mafarki, nan da nan kuwa Mama ta shirya ita da Abba da wasu daga cikin dangi suka nufi Kano domin ta'aziyya.
Ni kam a ranan ma sai da na je wurin Ahmad a ma'aikatar su, duk jikina a sanyaye yake, ya ji daɗin ganina sosai, musamman da ya ganni da abinci har da kuɗi na kai masa, sai ya rasa bakin magana ma ya riƙa hawaye, ni yawan kukan da yake yi a kaina tuni ya daina ba ni mamaki, domin na fahimci halittarsa ce haka, indai zan masa wani abu da ya ji daɗi to zai nuna mini godiyar shi ta hanyar zubar da hawayen murna da farinciki, kuma hakan na ƙara mini so da matuƙar tausayin shi.
Ya buɗe abincin ya ga ni yana ta sharar hawaye, ya mayar ya rufe ya dube ni, sai na ce masa.
"Bari na zo na koma."
Ya riƙe hannayena yana ta kallona ya ce.
"Ki ɗan jira ni Mami ina so na yi sallar la'sar, idan na idar sai na zo na raka ki bakin titi ki samu mota."
Na gyaɗa kai, saboda ni ma ina so ya raka ni hanyar domin na ba shi labarin mafarkin da na yi, ga shi ina jin tsoron hanyar saboda kusan jeji ne babu mutane sosai a wajejen.
Ina nan tsaye ya je suka yi jam'i a cikin ma'aikatar, sannan ya dawo gare ni, Muhibba tana goye a bayana tana baccinta, shi kam yana leƙata yana sumbatarta, muka tawo hanya muna ɗan taɓa hira, sai nake ba shi labarin mafarkin da na yi raina duk a jagule, har na ƙara masa da ce wa.
"Ni babban tashin hankalina auren da aka ɗaura maka, kuma sai ga shi ka manta da ni ka manta da Muhibba ma."
Tsayawa ya yi cak ya ka sa ci gaba da tafiya, ni ma na ja na tsaya muka zurawa juna idanu, fuskarsa babu annuri ko kaɗan, haka nan murya a shaƙe ya yi magana.
"Mami me yasa za ki faɗa mini wannan mummunan mafarkin wanda faɗarsa ba alheri ba ne? An ya kina son rayuwata kuwa? Kina son numfashina ya cigaba da gudana kuwa? Kin ji yadda kika tayar mini da hankali kuwa?"
Na sunkuayar da kai ina wasa da yatsuna na yi magana a hankali.
"To ai kai masoyina ne, shi ya sa na zaɓi na faɗa maka saboda har yanzu abin yana raina na kasa mantawa da shi, sosai mafarkin nan ya ɗaga mini hankalina, domin ba na son abin da zai raba ni da kai."
Ya ɗan yi murmushi a lokacin da ya kira suna na na ɗaga kai na kalle shi.
"Mami! A kullum ina roƙon ALLAH ya bar ni da ke har ƙarshen numfashina, saboda rabuwa da ke tamkar rabuwa da numfashin nawa ne, Ina roƙon ALLAH ko mutuwa ce za ta riskemu to ta ɗaukemu a rana ɗaya ni da ke, mu koma ga mahaliccinmu a lokaci guda, ga ƙabarina ga naki. Mami idan ana bunne mutane biyu a ƙabari ɗaya zan so namu ya kasance guda, a saka ni a can ƙasa ke kuma kina saman jikina."
Wani irin hawaye ne ya ratso mini fatar idanuwana, sai ya kai hannu ya goge mini tare da faɗin.
"Don ALLAH Mami na roƙe ki kar ki sake faɗawa wani zancen mafarkin nan, babu kyau a riƙa faɗin mafarki irin wannan, domin kowa da yadda zai fasaara shi."
Na gyaɗa kai ina dubansa na ce.
"In sha ALLAH babu wanda zan sake faɗawa, daman Mama kawai na faɗawa sai kuma kai."
Ya yi murmushi ya shafi gefen kumatuna tare da ce wa.
"ALLAH ya yi miki albarka Mamina."
Na amsa ina murmushi, sannan muka ci gaba da tafiya har zuwa bakin titi, ya tarar mini mota na shiga, yana tsaye muna ta ɗagawa juna hannu har motarmu ta ɓace bai bar wurin ba.

HAYATUL ƘADRI!Where stories live. Discover now